Mas'alolin aure Fitowa ta 6(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

Danna nan domin shiga karatu Online

TAMBAYA:
Shin manema aure za su iya yin gwajin lafiyarsu kafin su yi aure?
AMSA:
Na`am! Ma`aurata za su iya yin gwajin lafiyarsu kafin su yi aure. Domin shari`ar Musulunci ta zo ne saboda ta kare abubuwa guda biyar, kamar yadda malaman Usulul Fiqhi suka fada; a cikin su, akwai kare rayuwar dan Adam. Ga shi kuma cututtukan zamani sun zama ruwan dare, ta yadda mutum a cikin rashin gwaji, zai iya aurar matar da take dauke da irin wadannan cututtukan; ko ita matar ta auri namiji mai dauke da su. Don haka yin gwaji sababi ne na samun kariya, kuma a dogara ga Ubangiji subhanahu wa ta’ala.
WATA TAMBAYAR ITACE:
Wane mataki ya kamata daya daga cikin ma’aurata ya dauka yayin da ya gane cewa abokin zamansa yana dauke da cutar kanjamau?
AMSA:
Idan mace ta gane mijinta yana dauke da cutar kanjamau, ko shi ya fahimci haka, kafin su yi saduwar aure, to, lallai ne a je wurin kotun Musulunci don a raba auren. Saboda fadin Ubangiji subhanahu wa ta’ala cewa:
…وَلَا تُلْقُوا بِأَيْدِيكُمْ إِلَى التَّهْلُكَةِ… البقرة: 195
Ma’ana:
…Kada ku jefa kawunanku zuwa halaka…
Kuma yana daga cikin manya-manyan manufofin addinin Musulunci, tsare ran musulmi da lafiyarsu. Don haka sai a gujewa wannan annoba ta kanjamau.
Amma idan sun riga sun yi saduwar aure kuma aka tabbatar cewa kowannensu ya kamu da cutar, to sai su yi hakuri da junansu, su ci gaba da zama, su yarda da kaddarar Allah, tare da neman magani. Kuma su dauki matakan kare `ya`yansu daga fadawa cikin wannan annobar. Allah ya kare mu, amin.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates