Mas'alolin aure Fitowa ta 19(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

TAMBAYA:
Mene ne sharudddan daura aure
kuma yaya sigarsa take?
AMSA:
Aure yana tabbata ne idan aka cika
sharudda shida. Sharuddan kuwa
su ne;
1- A samu ma’aurata biyu, namiji
da mace, wadanda ya halatta a
daura masu aure a shari`ar
musulunci.
2- Waliyin mace: wanda zai bayar
da ita.
3- Wakilin ango: wanda zai
karbawa masa aure ko kuma shi
ango da kansa.
4- Akalla shaidu guda biyu
wadanda za su yi shaidar aure a
tsakanin ma’auratan.
5- Sadaki: Za a iya bayar da shi, ko
wani abu daga cikinsa, kafin daurin
auren, ko a lokacin da za a daura,
ko kuma bayan an daura.
6- Sigar bayarwa da karba.
Waliyyin mace ya ce: ya aurar da
ita ga wane. Shi kuma ango ya ce:
ya karba ko kuma wakilinsa ya
karba masa a madadinsa.
Sigar daurin aure takan zo da
lafazi kamar haka:- Na aura maka
ko kuma na halatta maka ita.
Dukkan wadannan lafazai sun
tabbata daga bakin Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama yayin
da ya ce da wani daga cikin
sahabbai (alhali yana daura masa
aure da wata mata), “Na mallaka
maka ita”. Kuma wannan lafazin
bai tsaya ga Larabci ba kawai, duk
lafazin da zai iya nuna bayarwa da
karba ya halatta a yi amfani da shi,
ko da wane irin yare ne kuwa.
Wannan shi ne abin da Ibn
Taimiyya ya fada a cikin fatawarsa.
Wannan zancen kuma, shine mafi
rinjaye a wurin mafi yawan
malamai.
Misali a harshen Hausa, za a iya
cewa: “Na mallaka maka ita, ko na
aura maka ita, ko kuma daga yau
ta zama halal a gare ka”. Da
sauransu. Haka kuma mai karba
zai iya amfani da lafazi kamar
haka: Na karba, Na amince ko
kuma na yarda da sauran lafuzzan
da al’adar gari ta saba amfani da
su wadanda suke nuna cewa an
mallaka maka ita kuma ka karbi
auren. Saboda haka kada a
tilastawa waliyyai (na ango ko na
amarya) cewa dole ne su fada da
Larabci. Kuma ya kamata a fahimci
cewa auren ba zai taba kulluwa ba,
face an yi amfani da sigar aurarwa
da kuma ta karba.
Akwai tambayoyi guda biyu
dangane da waliyyi kamar haka;
TAMBAYA:
Wane ne ya kamata ya zama
waliyyin matar da ta musulunta?
AMSA:
Waliyyinta shi ne shugaban
Musulmin da take zaune tare da
su, ko liman ko na’ibinsa ko
waninsu. Domin ya tabbata a cikin
wani hadisi mai tsawo, Manzon
Allah sallallahu alaihi wa sallama
yana cewa:
… ﻓﺎﻟﺴﻠﻄﺎﻥ ﻭﻟﻰ ﻣﻦ ﻻ ﻭﻟﻰ ﻟﻪ.
Ma’ana:
… Shugaba shi ne waliyyin macen
da ba ta da waliyyi.
Wannan yana nuna cewa kafiri ba
zai taba zama waliyyin mace
Musulma ba, ko da kuwa `yarsa ce
ko kanwarsa ko `yar’uwarsa.
TAMBAYA
Mene ne hukuncin matar da ta
aurar da kanta ba tare da waliyyi
ba?
AMSA:
A shari`ar Musulunci mace ba za ta
iya aurar da kanta ba, sai dai
waliyyinta. Domin Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama ya ce:
ﻻ ﻧﻜﺎﺡ ﺇﻻ ﺑﻮﻟﻰ
Ma’ana:
Aure ba ya tabbata sai da
Waliyyi…
Waliyyi a nan shi ne mahaifinta, ko
kane ko wan mahaifinta, ko kaninta
namiji, ko yayanta namiji, ko kuma
`ya`ya mazan da ta haifa da
sauransu. Kuma hadisi ya tabbata,
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama ya ce:
ﺃﻳﻤﺎ ﺍﻣﺮﺃﺓ ﻧﻜﺤﺖ ﺑﻐﻴﺮ ﺇﺫﻥ ﻭﻟﻴﻬﺎ ﻓﻨﻜﺎﺣﻬﺎ ﺑﺎﻃﻞ
ﻓﻨﻜﺎﺣﻬﺎ ﺑﺎﻃﻞ ﻓﻨﻜﺎﺣﻬﺎ ﺑﺎﻃﻞ …
Ma’ana:
Duk macen da ta yi aure ba tare da
izinin waliyyinta ba, to, auren ta
batacce ne, auren ta batacce ne,
auren ta batacce ne (ya fadi haka
har sau uku)…
A wani hadisin kuma Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama ya ce:
ﻻ ﺗﺰﻭﺝ ﺍﻟﻤﺮﺃﺓ ﺍﻟﻤﺮﺃﺓ . ﻭﻻ ﺗﺰﻭﺝ ﺍﻟﻤﺮﺃﺓ ﻧﻔﺴﻬﺎ …
Ma’ana:
Mace ba ta aurar da mace kuma
mace ba ta aurar da kanta…
Wannan hadisin yana nuna mana
cewa mace ba za ta zama
waliyyiyar wata ba, ko da `yarta ce
ko kanwarta ko `yar’uwarta. Haka
kuma ba za ta aurar da kanta ba.
Don haka ne muke kira ga ‘yan
uwanmu musulmi da su guji
al’adar nan ta turawa; idan dangin
mace ba sa son Ango sai su hada
baki su gudu, su je wani guri wasu
su daura musu aure, su Sani lallai
auran su ba aure bane kuma
zaman zina suke yi. Allah ya shirye
mu baki daya.

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: