Mas'alolin aure fitowa ta 9(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Na ambata muku nau’ikan auren da shari’ar musulunci ta hana a jiya, kuma na yi muku bayanin nau’i na farko a jiya, wato auren shigari.
TAMBAYA:
Mene ne auren kisan wuta kuma mene ne hukuncinsa?
AMSA:
Malamai sun ce: ma’anar auren kisan wuta shine; Mutum ya auri mace don ya halatta ta ga mijinta na farko, wanda ya yi mata saki uku, wanda a shari’ance ba za ta koma wurinsa ba, har sai ta auri wani mijin kuma ya sadu da ita.
Babban malamin nan Ibn Asir ya fassara auren kisan wuta da cewa:
هو أن يُطَلِّق الرجل امرأته ثلاثا فيتزوّجها رجل آخرُ على شريطة أن يُطَلّقَها بعد وَطْئها لتَحلَّ لزوجها الأوّل .
Ma’ana:
Shi ne mutum ya saki matarsa saki uku, sai kuma wani mutumin ya aure ta da sharadin zai sake ta bayan ya sadu da ita, don ya halattawa wancan mijin nata na farko ita.
Wanda ya aure ta da sharadin zai sake ta ana kiransa «المُحِلُّ» “al-Muhillu”, ma’ana: mai halattawa, shi kuwa wanda aka sake ta domin ta koma wurinsa (wato mijinta na farko) ana kiransa da «المُحَلَّلُ لَهُ» “al-Muhallalu Lahu”, ma’ana wanda aka halattawa.
Auren Kisan Wuta yana da halaye uku
1-Hali na farko shine: wanda zai aure ta na biyu ya shardanta yayin daurin auren cewa: zan aure ta ne don na sakarwa mijinta na farko ita.
Imam Abu Hanifa ya ce: wannan auren ya halatta, amma a zubar da sharadin.
Amma Imam Malik da Imamush Shafi’i da sauran malamai sun ce: auren haramun ne, bai halatta ba, domin an kafa sharadin ne yayin daurin auren.
2-Hali na biyu shine: waliyyin matar ya shardantawa miji na biyu yayin daurin auren cewa: zan aura maka `ya ta, idan ka sadu da ita, to, za ka sake ta don ta koma wurin mijinta na farko.
A nan ma Imam Abu Hanifa ya ce: wannan auren ya halatta, amma a watsar da sharadin.
Amma Imam Malik da Imamush Shafi’i da sauran malamai sun ce: wannan auren bai halatta ba, saboda an kafa sharadin ne yayin daurin auren.
3-Hali na uku kuwa shine: wanda zai aure ta ya yi sharadin kafin daurin aure, ko kuwa ya kudurta a zuciyarsa cewa: zai aure ta ne don ya halattawa mijinta na farko ita.
Imam Abu Hanifa ya ce: wannan auren ya halatta, amma a watsar da sharadin.
Amma Imam Malik da Imamush Shafi’i da sauran malamai sun ce: dukkan wadannan halaye da aka ambata guda ukun haramun ne, ba su halatta ba, Saboda dalilai kamar haka;
Hadisi ya tabbata daga Abdullahi Ibn Mas’ud radhiyallahu anhu ya ce:
لعن رسول الله صلى الله عليه و سلم المحل والمحلل له
Ma’ana:
Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya la’anci mai halattawa (wato wanda ya auri mace don ya halattawa wanda ya sake ta saki uku ita), da kuma wanda aka halatta wa (wato wanda aka auri mace don a halatta masa ita).
Kuma Imamut Tirmizi ya ce:
والعمل على هذا الحديث عند أهل العلم من أصحاب النبي صلى الله عليه و سلم منهم عمر بن الخطاب و عثمان بن عفان و عبد الله بن عمرو وغيرهم وهو قول الفقهاء من التابعين وبه يقول سفيان الثوري و ابن المبارك و الشافعي و أحمد و إسحق
Ma’ana:
Ma’abota ilimi daga sahabban Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam suna kan aiki da hukuncin wannan hadisin, daga cikinsu akwai Umar Ibnul Khaddab da Usman Ibn Affan da Abdullahi Ibn Amr da wasunsu radhiyallahu anhum, wannan shine fadin ma’abota ilimi daga tabi’ai, kuma wannan shine mazhabin Sufyanus Saurī da Ibnul Mubarak da Shafi’ī da Ahmad da Ishak.
Sannan kuma ya ce:
وسمعت الجارود بن معاذ يذكر عن وكيع أنه قال بهذا وقال ينبغي أن يرمي بهذا الباب من قول أصحاب الرأي.
Ma’ana:
Na ji Jarud Ibn Mu’az yana cewa: Waki’u ma ya tafi a kan haka, sannan ya ce: ya kamata a yi wurgi da maganar ma’abota ra’ayi (wato su Abu Hanifa) a wannan babin.
Sannan Imamut Tirmizi ya ci gaba da cewa:
قال جارود قال وكيع وقال سفيان إذا تزوج الرجل المرأة ليحللها ثم بدى له أنه يمسكها فلا يحل له أن يمسكها حتى يتزوجها بنكاح جديد
Ma’ana:
Imam Jarud ya ce: Waki’u ya ce: Sufyan ya ce: Idan mutum ya auri wata mace don ya halatta ta ga wani, sai kuma ya ga dacewar ya ci gaba da zama da ita, to, bai halatta ya ci gaba da zama da ita ba, har sai an daura musu sabon aure.
Ma’ana Malam Sufyan yana so ya ce mana; auren da aka daura shi a kan wannan niyyar ba aure ba ne, sai idan an sake daura wani sabon auren.
Haka kuma an rawaito daga Umar Ibnul Khaddab radhiyallahu anhu ya ce:
لا أوتى بمحلل ولا بمحلل إلا رجمتهما
Ma’ana:
Ba za a zo mini da mai halattawa (wato wanda ya yi aure don ya halatta wa wani matarsa) ba, ko kuma wanda aka halattawa (wato wanda aka auri mace don a halatta masa ita), face na jefe su. (domin ba aure suke yi ba zina suke yi).
Ibn Abdul Bar ya ce: auren kisan wuta haramun ne kuma rusasshen aure ne, don ba fa’ida a la’anci abu kuma a ce ya halatta. Wannan ita ce magana mafi rinjaye.
Allah shi ne mafi sani.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories