Su waye Ahlul-Kitabi Kuma shin suna nan har yanzu?

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Maqala

Tambaya: Su waye Ahlul-kitabi? Kuma shin akwaisu a wannan Zamani? Kuma ya halatta aci yankansu ko a auri Matan su?

Amsa: Da sunan Allah Mai Rahama mai jin ƙai. Ahlul Kitabi sune Yahudawa da Nasara. Wanda Allah ya sauƙar Musu da Littafi, amma addinin su an shafe shi da turo Annabi Sallallahu Alaihi Wa Sallam. Duk wata Aya da Allah ya ambaci Ahlul kitabi a AlƘur’ani to yana Nufin Yahudawa da Nasara ne. Na wancan zamani da wannan zamani. Saboda haka Kiristoci da Yahudawa na Wannan zamani namu sune Ahlul Kitabi.

Ya Halatta aci yankan Yahudawa da Nasara, hakanan ya halatta a aure matayensu idan har sun kasance masu kame kansu ne ga barin aikata Alfasha.

Allah maɗaukakin sarki yace:

A yau ne aka halatta muku dukkan abubuwa masu daɗi, kuma abincin wa’inda aka baiwa littafi halal ne a gare ku, kuma abicnku halal ne a gare su. da mata masu kamun kai daga muminai, da mata ƴaƴa(ba bayi ba) masu kamun kai na wa’inda aka basu littfi a gabaninku.

Suratul Ma’ida: Aya ta 5

Wannan ayah yayi bayani ƙarara na halaccin cin yankan Ahlul kitabi, haka nan da halaccin auren matayen su. Wannan kuma shine maganan Jumhurin Malamai.

Wataƙila wani yace: Ai Ahlul kitabi na Zamanin Annabi ba kaman na yanzu bane. Kuma yanzu littafan su an jirkita shi.

Amsa shine: Tun lokacin Annabi littafin su an riga an jirkita shi, an ɓoye gaskiya da yake ciki shiyasa ma suka ƙi yin Imani da Annabi domin a Littafin su na Asali akwai bayanin zuwan Annabi.

Sannan kuma kamar yadda suke da akwai Lalatattu a cikinsu akwai na gari, haka nan ma yanzu akwai Lalatattu akwai na gari.

Ibnu Aashur mai Tafsirin Attahrir wat-tanwir a ƙarƙashin Fassarar wannan aya dake cikin suratul ma’ida aya ta biyar yace:

Ahlul Kitab ya shafi wanda suke ƙarƙashin Zimmar Musulmai, da wanda aka ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya dasu, dama wanda ake yaƙi dasu. Wannan shine abin da yafi bayyana. Sai dai Imamu Malik, yaƙi auren Matan wanda ake yaƙi dasu. Amma jumhurun Maluma sun ce Halal ne auren matan Ahlul kitabi amma banda Mushrika ko Bamajusiya.

Yahudu da Nasara Mushrikai ne kamar yadda Alƙur’ani yayi bayani.

Allah yace:

Sun riƙi Malumansu(Yahudawa) da Masu Bautansu(Nasara) Abin Bauta koma bayan Allah, sannan sun riƙi Isa ɗan Maryam haka(a matsayin abin bauta)

Suratut-Taubah: 31

Wannan aya yana nunawa ƙara cewa Yahudawa da Nasara Mushrikai ne. Kuma Allah ya hana auren Mushrikai da nassin Alƙur’ani

Allah yace:

Kada ku auri Mushrikai mata har sai sunyi Imani,

Suratul Baqara: 221

Wannna ayah yana nuna haramcin auren mushrikai sai dai kuma ayar da muka kawo ya keɓance yahudawa da nasara daga cikin sauran Mushrikan.

Wannam game da halacci kenan. A addinin Musulunci Halal ne Musulmi ya auri bayahudiya ko banasariya haka nan Cin yankan su halal ne. Sai dai kaman yadda maluma sukayi bayani duk da cewa halal ne ya kamata Musulmi ya zaɓi abinda yafi masa. Shine ya auri ƴar uwarsa mumina wanda zata Tarbiyyanci ƴaƴan sa kan tafarki madaidaici.

Ibnu Qudama yace:

Idan wannan ya tabbata to abinda yafi dace wa shine kada mutum ya auri Ahlul kitabi, domin Umar Allah ya ƙara masa yarda ya umarci Musulmai wa’inda suka auri Ahlul kitabi yace ku sake su, suka sake su sai Huzaifa ne yaƙi sakar tashi matar. Umar yace masa ya sake ta, sai yace shin kana shaidawa cewa Auren ta haramun ne? Sai yace masa Ita garwashin wuta ce. Haka sukayi har sau uku. Sai Huzaifa yace eh na san cewa Garwashin wuta ce ita amma dai ita Halal ce a gare ni. Amma daga baya Huzaifa ya sake ta.

Al Mugni: 7/99

Sheikh Bin Baz Allah yayi Masa rahama yace:

Idan aka san Matar Ahlul Kitabi da kame kai da nesantar alfasha to ya Halatta a aure ta, domin Allah ya halatta mana hakan. Ya halatta mana matayen su da abincin su.

Sai dai a wannan zamani ana tsoron Sharri mai yawa ga wanda ya aure su, domin zata iya ƙiran sa zuwa ga Addinin ta, haka nan yaran sa zasu iya zama Kiristoci. Haɗarin yana da girma. Abinda yafi shine kada mutum ya aure su.

Fatawa Islamiyya: 3/172

A taƙaice: Ahlul Kitabi sune yahudu da nasara(Kiristoci). Ya Halatta aci yankan su, sannan ya halatta a auri matayensu. Sai dai rashin auren sun shine yafi saboda tsoron kada mutum ya faɗa zuwa ga Halaka. Ko kuma ta rinjaye yaran sa su koma addinin ta. Allah shine mafi sani.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates