KARBAN KYAUTUTTUKAN IDINKIRSIMETI DA CIN ABINCINWANNAN RANA KAMAR YADDA SALAFUS SAA'LIH SUKA YIBAYANI(Dr Ibrahim Jalo Jlingo)

Kafin mu shiga bayanin wannan
mas’alah ya kamata ‘yan’uwa su
san abubuwa kamar haka:-
Na farko: Shi dai bukin kirsimeti
wata bidi’ah ce da kiristoci suka
kirkira sannan suka maida ita wata
ibada da ake samun lada ta hanyar
yin ta -kamar dai yadda wasu
karkatattu cikin Musulmi suka kirkiri
bidi’ar idin mauludi- Kiristoci sun
kirkiri wannan bidi’ar ne kuwa a
shekarar miladiyyah ta 360, watau
a cikin karni na hudu bayan
haifuwar Annabi Isa alaihis salam.
Na biyu: babu wanda ya isa ya
bugi kirji a duniyan nan ya ce: ga
tabbatacciyar wata da rana da aka
haifi Annabi Isa alaihis salam a
cikin su, sai dai kowa ya fadi abin
da yake zato kawai, wannan shi ya
sa ma Kiristoci masu yin bukin
ranar Kirsimeti watau ranar
haifuwar Annabi Isa suka yi sabani
game da ranar da za a yi wannan
bukin, har mazhabobi biyu:-
Mazhabar farko: Za a yi bukin
Kirsimeti ne a ran 25 ga watan
December, wannan ita ce
mazhabar da Catholic, da
Protestant, da kuma mafi yawan
darikokin Kiristoci suke bi.
Mazhaba ta biyu: Za a yi bukin
Kirsimeti ne a ran 7 ga watan
January, wannan ita ce mazhabar
da darikokin Orthodox suke bi.
Na uku: Kiristoci kafurai ne kamar
yadda Yahudawa, da Majusawa,
da kuma sauran masu bautar
gumaka suke kafurai.
Na hudu: Ya kamata a san cewa
akwai wasu kafurai da Musulunci
ya kebanta su da wani hukunci
saboda tabbatar wa Musulmi wata
maslaha, wadannan kuwa su ne:
Yahudawa, da Kiristoci, su wannan
nau’i na kafurai Musulunci ya
halatta wa Musulmi cin yankansu,
da kuma auren matansu, sabanin
mabiya addinin majusu, ko mabiya
addinin indiyawa, ko mabiya
addinin Budha, ko mabiya sauran
addinai na bautan gumaka. Idan
an fahimci wannan sai mu shiga
bayanin mas’alarmu da muke son
yi wa jama’a bayaninta. Allah
Madaukakin Sarki Ya taimake mu.
HUKUNCIN KARBAN
KYAUTUTTUKAN KAFURAI A
RANAR IDINSU:
Su kyaututtukan da kafurai -Ahlul
kitabi ko wasun Ahlul kitabi- ke ba
wa Musulmi a ranakun idinsu na
kafurci da bidi’ah sun kasu kashi
biyu ne:-
Na farko: Kyaututtukan da suke ba
nama ba ne da ake bukatar
yankawa, watau kamar irinsu:
halawa, da tufafi, da kayan
marmari, sa sauransu.
Na biyu: Kyaututtukan da suke
nama ne da ke bukatar a yi masa
yanka irin ta Shari’ah.
To shi na farkon, watau
kyaututtukan da suke ba nama ba
ne da ke bukatar yanka irin ta
Shari’ah, babu sabani tsakanin
Salafus Salih a iya saninmu cikin
halaccin karbarsu, saboda dalilai
kamar haka:-
1- Imamul Baihaqii ya ruwaito
athari na 18,644 daga Muhammad
Dan Siiriin cewa:-
(( ﺃﺗﻲ ﻋﻠﻲ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻬﺪﻳﺔ ﺍﻟﻨﻴﺮﻭﺯ، ﻓﻘﺎﻝ: ﻣﺎ
ﻫﺬﻩ؟ ﻗﺎﻟﻮﺍ: ﻳﺎ ﺍﻣﻴﺮ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ ﻫﺬﺍ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻨﻴﺮﻭﺯ.
ﻗﺎﻝ: ﻓﺎﺻﻨﻌﻮﺍ ﻛﻞ ﻳﻮﻡ ﻓﻴﺮﻭﺯ.(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((An zo wa Sayyidina
Aliyyu Dan Abii Taa’lib Allah Ya
kara masa yarda da kyautar (idin)
Nairuuz, sai ya ce: mene ne
wannan? Sai suka ce: Ya Amirar
Muu’miniin! Wannan ranar Nairuuz
ce. Sai ya ce: (in haka abin yake)
ku rika yin Fairuuz a ko wace rana)
). Intaha.
2- Imam Ibnu Abii Shaibah ya
ruwaito cikin Musannaf athari na
24,371, da Imam Ishaq Ibnu
Raa’huyyah cikin Musnad athari na
1,606 daga Qaa’bus Dan Zibyaan
daga shi mahaifin nasa cewa wata
mace ta tambayi Nana A’isha Allah
Ya kara mata yarda ta ce:-
(( ﺍﻥ ﻟﻨﺎ ﺍﻛﺎﺭﺍ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﺠﻮﺱ ﻭﺍﻧﻪ ﻳﻜﻮﻥ ﻟﻬﻢ ﺍﻟﻌﻴﺪ
ﻓﻴﻬﺪﻭﻥ ﻟﻨﺎ، ﻓﻘﺎﻟﺖ: ﺍﻣﺎ ﻣﺎ ﺫﺑﺢ ﻟﺬﻟﻚ ﺍﻟﻴﻮﻡ ﻓﻼ
ﺗﺄﻛﻠﻮﺍ ﻭﻟﻜﻦ ﻛﻠﻮﺍ ﻣﻦ ﺃﺷﺠﺎﺭﻫﻢ.(( ﺍﻧﺘﻬﻰ
Ma’ana: ((Muna da ‘yan kodago
daga cikin Majusawa, sannan
kuma suna da ranar idin da suke
aika mana da kyaututtuka. Sai ta
ce: Amma abin da aka yanka
saboda wannan ranar to kada ku
ci, to amma ku ci daga ‘ya’yan
itatuwansu)). Intaha.
3- Imam Ibnu Abii Shaibah ya
ruwaito a cikin Musannaf athari na
24,372 daga Abuu Barzah cewa:-
(( ﻛﺎﻥ ﻟﻪ ﺳﻜﺎﻥ ﻣﺠﻮﺱ ﻓﻜﺎﻧﻮﺍ ﻳﻬﺪﻭﻥ ﻟﻪ ﻓﻲ
ﺍﻟﻨﻴﺮﻭﺯ ﻭﺍﻟﻤﻬﺮﺟﺎﻥ ﻓﻜﺎﻥ ﻳﻘﻮﻝ ﻷﻫﻠﻪ: ﻣﺎ ﻛﺎﻥ ﻣﻦ
ﻓﺎﻛﻬﺔ ﻓﻜﻠﻮﺍ ﻭﻣﺎ ﻛﺎﻥ ﻣﻦ ﻏﻴﺮ ﺫﻟﻚ ﻓﺮﺩﻭﻩ .((
ﺍﻧﺘﻬﻰ.
Ma’ana: ((Yana da wasu mazauna
Majusawa, kuma sun kasance
suna aika masa da kyautuka a
lokacin Nairuuz da Mihrajan,
sannan ya kasance yana gaya wa
iyalansa cewa: Kyautar da ta
kasance ta kayan marmari ne to ku
ci, wacce kuma ta kasance ba
hakan ba, to ku mayar da ita)).
Intaha.
Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya
yi taliki a kan wadannan hujjojin a
cikin littafinsa mai suna Iqtidhaa’us
Siraa’til Mustaqiim 2/554-555 ya
ce:-
(( ﻓﻬﺬﺍ ﻳﺪﻝ ﻋﻠﻰ ﺍﻧﻪ ﻻ ﺗﺄﺛﻴﺮ ﻟﻠﻌﻴﺪ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﻨﻊ ﻣﻦ
ﻗﺒﻮﻝ ﻫﺪﻳﺘﻬﻢ، ﺑﻞ ﺣﻜﻤﻬﺎ ﻓﻲ ﺍﻟﻌﻴﺪ ﻭﻏﻴﺮﻩ ﺳﻮﺍﺀ؛
ﻻﻧﻪ ﻟﻴﺲ ﻓﻲ ﺫﻟﻚ ﺇﻋﺎﻧﺔ ﻟﻬﻢ ﻋﻠﻰ ﺷﻌﺎﺋﺮ ﻛﻔﺮﻫﻢ .((
ﺍﻧﺘﻬﻰ.
Ma’ana: ((Wannan duka yana nuni
ne a kan cewa: Idi ba yi da wani
tasiri a kan hana karban kyautarsu,
a’a hukuncin karban kyautarsu ba
yi da wani bambanci tsakanin
lokacin Idi da kuma lokacin da ba
na Idi ba, saboda babu wani abu
na taimakon addininsu a cikin
karban kyautarsu)). Intaha.
TALIKI:
Da wannan ne za mu fahimci
cewa: Maluman Musulunci sun
hana cin yankan da Majusawa
suka yi domin bukukuwan idinsu,
to amma fa ba wai sun hana cin
yankan ba ne saboda
kasancewarsa yankan da aka yi
domin bukin idin kafurai ba, a’a an
hana cin yankan ne saboda
kasancewarsa yankan Majusawan
da ba sa cikin mutanen nan ne da
ake kira Yahudawa ko ake kira
Kiristoci, dukkan kuma kafurin da
ba ya cikin abin da ake kira
Yahudawa ko ake kira Kiristoci to
ba cin yankansa.
HUKUNCIN CIN NAMAN DABBAR
DA YAHUDAWA KO KIRISTOCI
SUKA YANKA DA HANNAYENSU
SABODA YIN BUKUKUWAN
IDINSU:
Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya
yi bayani game da cin abin da
Yahudawa ko Kiristoci suka yanka
saboda bukukuwan idinsu, a cikin
littafinsa mai suna Iqtidhaa’us
Siraa’til Mustaqim 2/555,558 ya
ce:-
(( ﻭﺍﻧﻤﺎ ﻳﺠﻮﺯ ﺍﻥ ﻳﺆﻛﻞ ﻣﻦ ﻃﻌﺎﻡ ﺍﻫﻞ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻓﻲ
ﻋﻴﺪﻫﻢ ﺑﺎﺑﺘﻴﺎﻉ ﺍﻭ ﻫﺪﻳﺔ ﺍﻭ ﻏﻴﺮ ﺫﻟﻚ ﻣﻤﺎ ﻟﻢ ﻳﺬﺑﺤﻮﻩ
ﻟﻠﻌﻴﺪ. ﻓﺄﻣﺎ ﺫﺑﺢ ﺍﻟﻤﺠﻮﺱ ﻓﺎﻟﺤﻜﻢ ﻓﻴﻬﺎ ﻣﻌﻠﻮﻡ ﻓﺈﻧﻬﺎ
ﺣﺮﺍﻡ ﻋﻨﺪ ﺍﻟﻌﺎﻣﺔ. ﻭﺃﻣﺎ ﻣﺎ ﺫﺑﺤﻪ ﺍﻫﻞ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ
ﻻﻋﻴﺎﺩﻫﻢ ﻭﻣﺎ ﻳﺘﻘﺮﺑﻮﻥ ﺑﺬﺑﺤﻪ ﺍﻟﻰ ﻏﻴﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﻧﻈﻴﺮ
ﻣﺎ ﻳﺬﺑﺢ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻮﻥ ﻣﻦ ﻫﺪﺍﻳﺎﻫﻢ ﻭﺿﺤﺎﻳﺎﻫﻢ
ﻣﺘﻘﺮﺑﻴﻦ ﺑﻬﺎ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ، ﻭﺫﻟﻚ ﻣﺜﻞ ﻣﺎ ﻳﺬﺑﺤﻮﻥ
ﻟﻠﻤﺴﻴﺢ ﻭﺍﻟﺰﻫﺮﺓ، ﻓﻌﻦ ﺍﺣﻤﺪ ﺭﻭﺍﻳﺘﺎﻥ: ﺍﺷﻬﺮﻫﻤﺎ
ﻓﻲ ﻧﺼﻮﺻﻪ: ﺍﻧﻪ ﻻ ﻳﺒﺎﺡ ﺍﻛﻠﻪ ﻭﺍﻥ ﻟﻢ ﻳﺴﻢ ﻏﻴﺮ
ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ. ﻭﻧﻘﻞ ﺍﻟﻨﻬﻲ ﻋﻦ ﺫﻟﻚ ﻋﻦ ﻋﺎﺋﺸﺔ ﻭﻋﺒﺪ
ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻋﻤﺮ.(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: (Cin abincin Ahlul Kitabi a
lokacin idinsu ga abin da dama ba
su yanka shi saboda Idi ba, yana
halatta ne ta hanyar saye da kudi,
ko kuwa kyauta, ko wanin haka.
Amma abin da Majusawa suka
yanka hukuncinsa sananne ne,
watau haramun ne a wurin dukkan
malamai, to amma abin da Ahlul
Kitabi suka yanka saboda idinsu,
da kuma abin da suke yin ibada ta
hanyar yanka shi ga wanin Allah’
kamar abin da suke yankawa
saboda Almasihu, da Zahrah, irin
dai abin da Musulmi suke yankawa
na Hadaya, da Layya, domin
neman kusantar Allah da shi, to,
Imam Ahmad yana da fatawowi
biyu game da hakan, fatawar farko
wacce ita ce ta fi shahara: Wannan
ba ya halatta a ci shi koda kuwa ba
a ambaci sunan wanin Allah a
kansa ba. An nakalto hana cin
wannan yankan ma daga Nana
A’isha, da Abdullahi Dan Umar..
Fatawa ta biyu ita ce: Cin wannan
yankan makruuhi ne ba haramun
ba. Wannan ita ce mazhabar
Malikiyyah, Imam Malik ya kyamaci
cin abin da Ahlul Kitabi suka yanka
saboda Coci-Cocinsu, ko saboda
idinsu amma ba tare da ya
haramta hakan ba)). Intaha.
Sannan har yanzu Sahikhul Islam
Ibnu Taimiyyah ya ce a cikin
Iqtidhaa’us Siraa’til Mustaqim
2/559 :-
(( ﻭﻧﻘﻠﺖ ﺍﻟﺮﺧﺼﺔ ﻓﻲ ﺫﺑﺎﺋﺢ ﺍﻷﻋﻴﺎﺩ ﻭﻧﺤﻮﻫﺎ ﻋﻦ
ﻃﺎﺋﻔﺔ ﻣﻦ ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﻢ، ﻭﻫﺬﺍ ﻓﻴﻤﺎ
ﺍﺫﺍ ﻟﻢ ﻳﺴﻤﻮﺍ ﻏﻴﺮ ﺍﻟﻠﻪ، ﻓﺎﻥ ﺳﻤﻮﺍ ﻏﻴﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻲ
ﻋﻴﺪﻫﻢ ﺍﻭ ﻏﻴﺮ ﻋﻴﺪﻫﻢ ﺣﺮﻡ ﻓﻲ ﺍﺷﻬﺮ ﺍﻟﺮﻭﺍﻳﺘﻴﻦ،
ﻭﻫﻮ ﻣﺬﻫﺐ ﺍﻟﺠﻤﻬﻮﺭ، ﻭﻫﻮ ﻣﺬﻫﺐ ﺍﻟﻔﻘﻬﺎﺀ ﺍﻟﺜﻼﺛﺔ
ﻓﻴﻤﺎ ﻧﻘﻠﻪ ﻏﻴﺮ ﻭﺍﺣﺪ، ﻭﻫﻮ ﻗﻮﻝ ﻋﻠﻲ ﺑﻦ ﺍﺑﻲ ﻃﺎﻟﺐ
ﻭﻏﻴﺮﻩ ﻣﻦ ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ، ﻭﻫﻮ ﻗﻮﻝ ﺍﻛﺜﺮ ﻓﻘﻬﺎﺀ ﺍﻟﺸﺎﻡ
ﻭﻏﻴﺮﻫﻢ. ﻭﺍﻟﺜﺎﻧﻴﺔ: ﻻ ﻳﺤﺮﻡ ﻭﺍﻥ ﺳﻤﻮﺍ ﻏﻴﺮ ﺍﻟﻠﻪ،
ﻭﻫﺬﺍ ﻗﻮﻝ ﻋﻄﺎﺀ ﻭﻣﺠﺎﻫﺪ ﻭﻣﻜﺤﻮﻝ ﻭﺍﻻﻭﺯﺍﻋﻲ
ﻭﺍﻟﻠﻴﺚ.(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((An ciro yin sauki a kan
cin yanke-yanken idodin
(Yahudawa da Kiristoci) da
makamantansu (su yanke-yanken)
daga wani sashi na Sahabbai Allah
Ya kara musu yarda amma fa
wannan sai idan ba su ambaci
wanin Allah a lokacin yankan ba, in
kuma har sun ambaci wanin Allah
a lokacin yankan to cin sa ya
haramta a cikin fatawa mafi
shahara daga cikin fatawowi biyu
da Imam Ahmada yake da su a
cikin mas’alar, wannan kuwa shi ne
mazhabar jumhur, kuma shi ne
mazhabar Fuqaha’un nan guda
uku, kamar yadda mutane da yawa
suka ruwaito, kuma shi ne
maganar Aliyyu Dan zabii Taa’lib
da waninsa a cikin Sahabbai, daga
cikinsu ma akwai Abud Dardaa, da
Abu Umamah, da Irbadh Dan
Saa’riyah, da Ubaa’dah Dan
Saa’mit, kuma shi ne maganar
maluman Sham da wasunsu.
Fatawar Imam Ahmad ta biyu ita
ce: Cin wannan yankan ba
haramun ba ne koda kuwa sun
ambaci sunan wanin Allah a
lokacin yankan, wannan kuwa shi
ne maganar Ataa’u, da Mujaa’hid,
da Makhuul, da Auzaa’ii, da kuma
Laith)). Intaha.
TALIKI NA FARKO:-
Za mu fahimta daga maganganun
malaman da suka gabata cewa:
Abin da Yahudawa da Kiristoci
suke yankawa saboda bukukuwan
idinsu yana kasuwa ne zuwa kashi
biyu:-
Na farko: Abin da suka ambaci
sunan Allah yayin yanka shi.
Na biyu: Abin da suka ambaci
sunan wanin Allah yayin yanka shi.
To ita tabbar da aka ambaci sunan
Allah lokacin yanka ta, Malamai
sun kasu kashi biyu game da
hukuncin cinta.
Mazhabar farko: Sahabbai da
yawa sun ba da damar cin wannan
nama. Maluman Malikiyyah, da
Imam Ahmad cikin ruwayah sun
halattar da cinsa amma tare da
nuna kyama.
Mazhaba ta biyu: Nana A’isha, da
Abdullahi Dan Umar, da kuma
Maluman Hanaa’bilah sun ce cin
wannan nama haramun ne.
Sannan ita kuma dabbar da aka
ambaci sunan wanin Allah lokacin
yanka ta, watau kamar wacce aka
ambaci sunan Yesu Almasihu
lokacin yanka ta, wannan ma
Malamai sun kasu kashi biyu game
da hukuncin cin wannan dabbar:-
Mazhabar farko: Cin wannan
dabba bai halatta ba, wannan shi
ne abin da Aliyyu Dan Abii Taa’lib,
da Abud Dardaa’u, da Abuu
Umamah, da Irbadh Da Saa’riyah,
da Ubaa’dah Dan Saa’mit, da
Hanafiyyah, da Malikiyyah, da
Shafi’iyyah, da Hanaa’bilah, da
mafi yawan maluman kasar Sham,
suk fada.
mazhaba ta biyu: Cin wannan
dabba halal ne, wannan shi ne
abin da Ataa’u, da Mhjaa’hid, da
Makhul, da Auzaa’ii, da Laithu Dan
Sa’ad, da kuma Imam Ahmad cikin
ruwaya suka fada.
TALIKI NA BIYU:-
Za mu iya fahimta daga
maganganun da suka gabata
cewa: Naman kasuwa da Musulmi
ke yankawa da hannayensu idan
Kiristoci suka saya suka dafa a
matsayin abincin Kirsimeti, to
wannan abincin halal yake ga
dukkan wanda suka ba da shi gare
shi. Wallahu A’alam.
Mun kawo maganganun Salafus
Saa’lih ne cikin wannan mas’alah,
saboda kwaranye wa ‘Yan’uwa
Musulmi mushikilar da ke cikinta.
Muna rokon Allah Madaukakin
Sarki ya nuna mana gaskiya
gaskiya ce ya ba mu ikon bin ta, ya
nuna mana karya karya ce ya ba
mu ikon guje mata.

2 responses to “KARBAN KYAUTUTTUKAN IDINKIRSIMETI DA CIN ABINCINWANNAN RANA KAMAR YADDA SALAFUS SAA'LIH SUKA YIBAYANI(Dr Ibrahim Jalo Jlingo)”
  1. Muhammad chigari kumo Avatar
    Muhammad chigari kumo

    Masha Allahu

  2. Zeenat kabeer Avatar
    Zeenat kabeer

    Allah ya saka da alkhairi kuma insha Allah zamu kiyaya

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: