ME YA FARU A KARBALA 38(Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga karatu Online

Me Zamu Yi A Ranar Ashura?
Ranar Ashura ita ce rana ta goma
ga watan Muharram, watan farko a
kalandar musulunci kuma daya
daga cikin watanni hudu masu
alfarma da madaukakin sarki ya
fade su a cikin Alkur’ani (Suratut
Taubah: 36). Manzon Allah
(SAWW) ya bayyana falalar
wannan watan da kuma
musamman kwana goma na
farkonsa, wadanda ya bayyana
cewa, babu wasu kwanaki da aikin
kwarai ya fi soyuwa a wurin Allah a
cikin su kamar su.
Wannan rana ta goma ga wata ta
kasance rana mai dinbin tarihi da
akwai a cikin hadisai, wasun su
masu inganci wasu kuma masu
rauni a kan ta. Hadisan sun
bayyana cewa, a daidai wannan
ranar ne madaukakin sarki ya
halicci annabi Adam (AS). A irin ta
ne kuma ya shigar da shi cikin
aljanna. A irin ta ne kuma ya karbi
tubansa bayan da shedan ya
zamar da shi zuwa ga abinda aka
hane shi. A kuma irin ta ne har
wayau Allah ya kubutar da annabi
Musa (AS), ya nutsar da makiyin
Allah Fir’auna.
Wannan ya sa Annabi Sallallahu
Alaihi Wa Alihi Wasallam yake
azumtar ranar Ashura tun yana
Makka kamar yadda mushrikai su
ma suna yi. A lokacin da ya zo
Madina kuma sai ya tarar da
Yahudawa su ma suna yin azumin,
suna cewa murna muke yi da ranar
da annabinmu Musa ya samu
kansa shi da kakanninmu Bani
Isra’ila. Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wa Alihi Wasallam sai ya ce,
to ai mun fi ku cancanta da annabi
Musa (AS). A nan ne ya umurci
musulmi su ma su yi azumin, har
ma ya ce, wanda ya riga ya fara cin
abinci a ranar Ashura to ya kama
bakinsa. Babban dalilin kenan
cewa azumin ya zama farali ba
mustahabbi ba. Amma a lokacin da
aka saukar da wajabcin azumin
Ramadhan a cikin Suratul Baqara
sai Sallallahu Alaihi Wasallam ya
sassauta hukuncin ya zamanto
wanda ke so ya yi, wanda kuma
bai so ba ya bari. Amma kuma ya
jaddada irin dinbin ladar da ke
tattare da yin azumin.
Hadisai sun zo da dama ta
hanyoyin da malamai masana
kimiyyar hadisi suka gamsu da su
cewa, annabi (S) ya bayyana
muhimmancin wannan azumi.
Misali, a cikin Sahih al-Bukhari
Ibnu Abbas (RA) ya ce, bai taba
ganin wata rana da manzon Allah
(S) yake kirdadon yin azumin ta ba
yana fifita shi a kan na sauran
ranaiku kamar ranar Ashura. Haka
kuma babu wani watan da yake
fifita yin azumi a cikin sa kamar
Ramadhan.
A cikin hadisin Abu Qatadata (R.A)
wani mutum ya zo ya yi fatawa
gurin manzon Allah (S) ya ce, ya
manzon Allah! Mene ne matsayin
azumin ranar Arafat? Sai ya ce,
“Ina fatar Allah zai goge zunuban
bara da na bana ga wanda ya yi
shi”. Ya ce, to azumin ranar Ashura
fa? Sai Sallallahu Alaihi Wa Alihi
Wasallam ya ce, “Ina fatar Allah ya
goge zunubin shekarar bara ga
wanda ya yi shi.”
Da wannan ta tabbata kenan ranar
Ashura kafin ta zama ranar
shahadar sayyadi Husaini (RA)
rana ce da akwai wata shari’ar
Allah a kan ta. Kuma tun da yake
addinin Allah ya cika kafin wafatin
manzon Allah (SAWW) ba wani
abin da zai faru da zai iya canza
mana shari’ar da shi Manzon Allah
ya bar mu a kanta. Ko da
kasancewar wannan rana tana da
tarihi mai dangantaka da annabi
Adam da annabi Musa (AS) ba mu
isa mu farar da wata ibada da
wannan manufar ba sai don shi
uban tafiya ya karantar da mu ita.
Ai ka ga ba ma azumtar ranar
Hijira ko ta Badar ko Isra’i da
Mi’iraji dss. Amma da maigidan ya
karantar da mu haka (SAWW) da
mun kama kenan har yaumut-
tanadi. Wannan shi ne addinin
Allah da ba mai ikon yin shisshigi a
cikin sa. Wanda kuma Allah da
mazno kadai ke shar’antawa a
cikin sa. Allah (T) yana cewa:
(( ﻳﺎ ﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺁﻣﻨﻮﺍ ﻻ ﺗﻘﺪﻣﻮﺍ ﺑﻴﻦ ﻳﺪﻱ ﺍﻟﻠﻪ
ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ ﻭﺍﺗﻘﻮﺍ ﺍﻟﻠﻪ ﺇﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﺳﻤﻴﻊ ﻋﻠﻴﻢ((
ﺍﻟﺤﺠﺮﺍﺕ: ١
“Ya ku wadanda suka yi imani!
Kada ku shiga gaban Allah da
manzonsa. Kuma ku ji tsoron
Allah, hakika Allah mai cikakken ji
ne, mai cikakken sani”. Suratul
Hujuraat: 1.
Saboda haka, duk mumini mai son
ya tashi a tutar manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wa Alihi
Wasallam to, abinda manzon Allah
ya sunnanta ne kadai zai yi a
wannan rana; shi ne azumi. Ba zai
biye ma masu makoki ba, haka
kuma ba zai biye ma masu cewa a
yi murna har da caba ado da sa
fararen kaya da yalwata ma iyali
don su cika ciki ba. Ana maganar
azumi me ya kawo maganar cika
ciki kuma?! Wannan wata bidi’a ce
da jahilai suka zo da ita don
tunkarar waccan tsohuwar bidi’ar
‘yan Shi’a ta makoki. Kuma an
kirkira hadisai da dama a kan
haka. Amma malamai magadan
annabawa sun yi fashin baki a kan
su kuma sun tabbatar ba su asali.
Allah muke roko ya datar da mu da
sawaba. Ya ba mu ikon kasancewa
a cikin “..wadanda suke sauraron
magana sai su bi mafi kyawon ta.
Wadannan su ne wadanda Allah
ya shiryar, kuma wadannan su ne
masu kaifin hankali”. Suratuz
Zumar: 18.
Alhamdu Lillah.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

2 responses to “ME YA FARU A KARBALA 38(Dr. Mansur Sokoto)”
  1. Aliyu umar Avatar
    Aliyu umar

    Malam Allah yasaka da alkhairi.

  2. alhamdulillahi allah yasakawa mmaigirma limamin makka hudubarsa takarshe yayita agabar da itane damuwarmu ayanzu dukkan musulmi yancikin wannan hali

Leave a Reply

Categories
Latest updates