Fatawoyin Falalar Goman Farko Na Watan Babbar Salla Da Layya Da Sallar idi(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Godiya ta tabbata ga Allah
Ubangijin talikai. Tsira da amincin
Allah su kara tabbata ga Annabi
Muhammadu sallallahu alaihi wa
sallama da iyalan gidansa, da
sahabbansa.
Bayan haka, wannan littafi ya
kunshi bayanai a kan hukunce-
hukuncen layya da falalar kwanaki
goma na farkon watan Zul-Hijja.
Kuma littafin ya samu ne
sakamakon bukatar da ake da ita
ta fahimtar wannan babbar ibada
karkashin koyarwar Alkur’ani da
Sunnar Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama bisa fahimtar
magabata na kwarai.
Sakamakon muhimmancin da
wannan al’amari yake da shi, na
kuduri aniyar tunatar da ku,
musamman wadanda suke nesa,
da wadansu kasashe wadanda
wnnan Littafi bai je ba.
Muna rokon Ubangiji subhanahu
wa ta’ala ya kyautata niyyarmu ya
sanya wannan aiki ya zama
karbabbe a wurinsa, sannan ya
yafe mana kurakuranmu, āmīn.
ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ
Darasi na 1
A wannan darasi za mu amsa
tambaya kamar haka;
Mene ne falalar ranaku goman
farkon Zul-Hijja?
AMSA:
Hakika wadannan ranaku,
ranakune ne masu falala, kamar
yadda Ubangiji subhanahu wa
ta’ala ya fada a cikin littafinsa mai
tsarki cewa;
ﻭﺍﻟﻔﺠﺮ (1) ﻭﻟﻴﺎﻝ ﻋﺸﺮ 2) )
Ma’ana:
Ina rantsuwa da ketowar alfijir,
kuma ina rantsuwa da darare
goma (ma’ana ranaku gona na
farkon Zul hijja).
Kuma hadisi ya tabbata daga
Abdullahi Ibn Abbas radhiyallahu
anhu ya ce: Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama ya ce:
ﻣﺎ ﺍﻟﻌﻤﻞ ﻓﻲ ﺃﻳﺎﻡ ﺃﻓﻀﻞ ﻣﻨﻬﺎ ﻓﻲ ﻫﺬﻩ ﻗﺎﻟﻮﺍ ﻭﻟﺎ
ﺍﻟﺠﻬﺎﺩ ﻗﺎﻝ ﻭﻟﺎ ﺍﻟﺠﻬﺎﺩ ﺇﻟﺎ ﺭﺟﻞ ﺧﺮﺝ ﻳﺨﺎﻃﺮ
ﺑﻨﻔﺴﻪ ﻭﻣﺎﻟﻪ ﻓﻠﻢ ﻳﺮﺟﻊ ﺑﺸﻲﺀ .
Ma’ana:
Babu wasu ranaku da ayyukan
alkhairi suka fi soyuwa a wurin
Ubangiji subhanahu wa ta’ala
kamar wadannan ranaku (goma na
farkon Zul-Hijja). Sai suka ce: ya
Ma’aikin Allah sallallahu alaihi wa
sallama ko da jihadi fisabilillahi
ne? Sai Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama ya ce: Ko da
jihadi fisabilillahi ne, Sai dai
mutumin da ya fita jihadi da ransa
da dukiyarsa kuma bai koma gida
da wani abu ba (ma’ana: ya yi
shahada a fagen fama har da
dukiya baki daya).
Haka kuma, an karbo daga Jabir
Ibn Abdullah radhiyallahu anhu ya
ce: Manzon Allah sallallahu alaihi
wa sallama ya ce:
ﺃﻓﻀﻞ ﺃﻳﺎﻡ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ ﺍﻟﻌﺸﺮ ﻳﻌﻨﻲ ﻋﺸﺮ ﺫﻱ ﺍﻟﺤﺠﺔ ﻗﻴﻞ
ﻭﻻ ﻣﺜﻠﻬﻦ ﻓﻲ ﺳﺒﻴﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻗﺎﻝ ﻭﻻ ﻣﺜﻠﻬﻦ ﻓﻲ ﺳﺒﻴﻞ
ﺍﻟﻠﻪ ﺇﻻ ﺭﺟﻞ ﻋﻔﺮ ﻭﺟﻬﻪ ﺑﺎﻟﺘﺮﺍﺏ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ
Ma’ana:
Mafifitan ranakun duniya su ne
ranaku goma (na farkon Zul-Hijja).
Sai aka ce da shi: babu
kwatankwacinsu ko a jihadi fi
sabilillahi? Sai ya ce: babu
kamarsu sai dai mutumin da aka
turmuza fuskarsa a cikin turbaya
(Ma’ana: an kashe shi, ya yi
shahada a fagen fama).
Don haka Sa’īd Ibn Jubaīr ya
kasance yayin da ranaku goma na
farkon Zul-Hijja suka shiga, yana
yawaita ibada a cikinsu.
Don haka nake kira da cewa
Yana da kyau ga dukkan mai
kaunar Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama, kuma yake son
samun babban rabo da ya kasance
yana kara kyautata ayyukansa a
cikin wadannan ranaku.
Wa sallallahu wa sallama ala
Nabiyyina Muhammadin wa ala
alihi wa Sahbihi ajma’in.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

7 responses to “Fatawoyin Falalar Goman Farko Na Watan Babbar Salla Da Layya Da Sallar idi(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)”
  1. mustapha salmanu Avatar

    Allah ya saka da alkhairi,ameen

  2. Salisu h Avatar
    Salisu h

    Allah yasaka da alkairi

  3. muhammad sani Avatar
    muhammad sani

    Allah yasaka da alheri

  4. ZANNAH GREMA MADU Avatar

    allah ya saka da alkhairi

  5. adamu dalhat Avatar
    adamu dalhat

    Allah ya saka da alkhairi amin

  6. Malam Allah ya saka da mafificin alkhairi yasa mudace da wadannan ranaku.

  7. […] Fatawoyin Falalar Goman FarkoNa Watan Babbar Salla Da LayyaDa Sallar idi(Sheikh Abdulwahhab Abdullah…. […]

Leave a Reply

Latest updates
Categories