HUKUNCE HUKUNCEN AIKIN HAJJI DA UMRA Darasi na 14(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

A yayin zaman Mina, ana son
mahajjaci ya yawaita yin zikirai da
hailala da hamdala da salatin
Annabi sallallahu alaihi wa
sallama, musamman bayan an
gama kowace sallar farilla. Haka
kuma, ana son ya yawaita fadin
ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ
ﻭﻟﻠﻪ ﺍﻟﺤﻤﺪ
Ma’ana:
Allah shi ne mafi girma! Allah shi
ne mafi girma! Babu wanda ya
cancanta a bautata masa sai Allah.
Allah shi ne mafi girma! Allah shi
ne mafi girma! Dukkan godiya ta
tabbata ga Allah.
Haka kuma a rika yawan godewa
Allah bisa ni’imar da ya yi, ta
kammala aikin hajji lafiya; sannan
a rika sa rai da kyautata
tsammanin ko Allah ya karbi aikin
hajjin ko bai karba ba. Watau a
kasance ( ﺑﻴﻦ ﺍﻟﺨﻮﻑ ﻭﺍﻟﺮﺟﺎﺀ) tsakanin
fatan rahamar Allah da tsoron
azabarsa . Hakika yin haka yana
daga cikin siffofin Annabawa a
cikin ibadarsu.
Haka kuma ana son a zauna a
Mina na tsawon kwanaki uku, tare
da cewa idan an kwana biyu
kawai, ya wadatar. Amma yin
kwana ukun shine yafi. Manzon
Allah sallallahu alaihi wa sallama
da sahabbansa kwana uku suka yi,
ba kwana biyu ba., kuma babu
shakka, yin hakan shi ne ya fi cika
wajen tsoron Allah, kamar yadda
Alqur’ani ya bayyana.
Amma a halin yanzu mafi yawancin
mutane sun manta da wannan
sunnar, kai ka ce wadannan
kwanaki ukun ma babu su kwata-
kwata. Abin da ya fi daure kai shi
ne, irin yadda za ka ga wasu
manyan malaman da ake koyi da
su, kuma ake sauraren
maganarsu, sun ki cika kwanaki
ukun. Koda yake shari’a ba ta zargi
wanda ya bar Mina bayan kwana
biyu ba, to, amma ya kamata irin
wadannan malamai su rika
dagewa wurin cika kwanakin Mina,
don su bayar da kyakkyawan
misali ga al’umma. Allah ya sa mu
dace, amin.
Dangane da abubuwan da
mahajjata ya kamata su nisanta a
zamansu na kwanakin Mina, wajibi
ne su nisanci duk wani nau’i na
sabon Allah, da ayyukan zubar da
mutunci. Amma idan mutum ya
dubi abubuwan da wadansu suke
aikata wa abin akwai ban tsoro,
musamman ga duk mai tsoron
Allah. Domin za ka ga wadansu
mutane, musamman mutanen
Afrika ta yamma da sauransu, suna
yin fito na fito da dokokin Allah
Ta’ala, suna saba masa a sarari,
kai ka ce ba aikin hajji suke yi ba.
Wani lokaci sai ka ga mace ta caba
ado da kwalliyar da ke jawo
hankalin maza. Abin bai tsaya a
nan ba, har da dauke-dauken
hotuna a cikin shemomi, da
cakuduwa tsakanin maza da mata,
ta yadda hakan zai haifar da fitinar
zina. An sha kama masu aikata irin
wannan laifin, ba sau daya ba, ba
sau biyu ba, musamman mata
masu zaman kansu a Jidda da
birnin Makka, wadanda ba su
samun damar yin fasadi sai a
wannan lokacin. Wani lokaci sai ka
ga karuwan sun dungumo sun zo
Mina, suna jan hankalin mahajjata,
don su yi fasadi da rashin mutunci
a wannan wuri mai albarka. Haka
kuma, wani lokaci ana samun
wadansu marasa tsoron Allah da
suke biyewa barayi, su yi ta sace-
sace a cikin wadannan ranaku
masu albarka.
To, muna kira da babbar murya ga
hukumomin alhazai da su yi aiki
tukuru wajen magance wannan
fasadi. Lallai ne su dauki mataki
mai karfi a kan haka. Domin babu
wanda ya fi karfin doka. Idan kuma
ba za a iya daukar mataki a can
kasa mai tsarki ba, to sai a bari
idan an dawo gida, a hukunta su
daidai gwargwadon irin laifin da
suka yi.
Allah ya kyauta.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories