DOMIN TABBATAR TAUHIDI DOLE NE A GUJE WA BIDI'A

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Mai Rubutu: Dr. Ibrahim Jalo Jalingo
An gina Musulunci ne a kan rukunai biyar, mafi girmansu shi ne: ((لا اله الا الله محمد رسول)) watau yarda da cewa babu abin bauta a bisa cancanta sai Allah, sannan Muhammad manzon Allah ne. Wadannan jumloli biyu: ((Laa Ilaaha Illal Laahu Muhammadur Rasuulul Laahi)) su ake kira lafuzan Tauhidi.
Kamar kuma yadda ake gani shi wannan Rukuni na Tauhidi yana da rassa biyu ne:-
1. Reshe na farko shi ne tabbatarwa babu wani abin bauta a bisa cancanta sai Allah Shi kadanSa; saboda haka duk wanda aka bauta wa in dai ba Allah ba ne to zalunci ne aka yi; domin an ba shi abin da bai cancanta a ba shi ba, an ba shi abin da yake ba hakkinsa ne ba. Lalle tsaida wannan reshe na Tauhidi yana nufin nisantar dukkan wani nau’i na Shirka.
2. Reshe na biyu shi ne yarda da cewa Annabi Muhammad mai tsira da amincin Allah Manzo ne na Allah. Lalle tsaida wannan reshe na Tauhidi yana nufin nisantar dukkan wani nau’i na bidi’ah; watau kada kowa ya bauta wa Allah sai da abin da Annabi Muhammadu mai tsira da amincin Allah ya shar’anta, ko dai ta hanyar Alkur’ani mai girma, ko kuwa ta hanyar ingantattun hadithansa masu daraja. Duk wanda za a ce da shi ga abin da Annabi ya fada cikin mas’ala kaza, sannan ya ce ba zai yi aiki da abin da ya fada ba, zai yi aiki ne da fadar waninsa, to lalle wannan bai tsaida hakkin Muhammadur Rasuulul Laahi ba, kuma tauhidinsa bai cika ba. Allah Ya taimake mu.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories