Idan mutum yana cikin yin sahur, sai ya ji kiran sallah yaya zai yi?( Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

AMSA:
A irin wannan hali mutum zai
qarasa abin da ke hannunsa ne.
Domin hadisi ya tabbata daga Abu
Huraira radhiyallahu anhu ya ce:
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama ya ce:
ﺇِﺫَﺍ ﺳَﻤِﻊَ ﺃَﺣَﺪُﻛُﻢْ ﺍﻟﻨِّﺪَﺍﺀَ ﻭَﺍﻟْﺈِﻧَﺎﺀُ ﻋَﻠَﻰ ﻳَﺪِﻩِ ﻓَﻠَﺎ
ﻳَﻀَﻌْﻪُ ﺣَﺘَّﻰ ﻳَﻘْﻀِﻲَ ﺣَﺎﺟَﺘَﻪُ ﻣِﻨْﻪُ
Ma’ana:
Idan dayanku ya ji kiran sallah
alhali qwarya tana hannunsa, kada
ya ajiye ta, har sai ya biya
buqatarsa .
Amma a nan sai a yi hattara, kada
a mayar da irin wannan dabi`a ta
zama al`ada a kullum domin ba
ance mustahabbi bane yin hakan
ballantana a ce ana so a rinqa yi,
sassauci ne akayi ga wanda ya
fara cin abinci sai lokaci ya kure
masa.
wa sallallahu wa sallama ala
Nabiyyina Muhammadin wa ala
aa’lihi wa sahbihi ajma’in.

Yaushe ne ya fi dacewa a yi sahur?(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

AMSA:
Haqiqa Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama ya kwadaitar da a
jinkirta yin sahur zuwa kusan
ketowar alfijir, kamar yadda ya
tabbata a cikin hadisin da aka
karbo daga Anas daga Zaīd Ibn
Thābit radhiyallahu anhu ya ce:
ﺗَﺴَﺤَّﺮْﻧَﺎ ﻣَﻊَ ﺍﻟﻨَّﺒِﻲِّ ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠَّﻢَ ﺛُﻢَّ ﻗَﺎﻡَ
ﺇِﻟَﻰ ﺍﻟﺼَّﻠَﺎﺓِ ﻗُﻠْﺖُ ﻛَﻢْ ﻛَﺎﻥَ ﺑَﻴْﻦَ ﺍﻟْﺄَﺫَﺍﻥِ ﻭَﺍﻟﺴَّﺤُﻮﺭِ
ﻗَﺎﻝَ ﻗَﺪْﺭُ ﺧَﻤْﺴِﻴﻦَ ﺁﻳَﺔً
Ma’ana:
Mun yi sahur tare da Annabi
sallallahu alaihi wa sallama,
sannan sai ya tashi zuwa sallah.
Sai na cewa (Anas) yaya (tsawon
lokacin da ke) tsakanin kiran sallah
da yin sahur yake? Sai ya ce:
Gwargwadon (karanta) ayoyi
hamsin .
Haka kuma an karbo daga Sahal
Ibn Sa’ad radhiyallahu anhu ya ce:
ﻛُﻨْﺖُ ﺃَﺗَﺴَﺤَّﺮُ ﻓِﻲ ﺃَﻫْﻠِﻲ ﺛُﻢَّ ﺗَﻜُﻮﻥُ ﺳُﺮْﻋَﺘِﻲ ﺃَﻥْ
ﺃُﺩْﺭِﻙَ ﺍﻟﺴُّﺠُﻮﺩَ ﻣَﻊَ ﺭَﺳُﻮﻝِ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ
ﻭَﺳَﻠَّﻢَ
Ma’ana:
Na kasance ina yin sahur cikin
iyalina, bayan wannan sai in yi
gaggawa domin in samu sujada
(sallah) tare da Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama.
Wadannan hadisai na nuna cewa
ana yin sahur ne dab da ketowar
alfijir.

Hakikanin kaunar Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama.( Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

Alhamdu lillahi rabbil A’lamin,
Wa sallallahu wa sallama ala
Nabiyyina Muhammad wa ala alihi wa
sahbihi ajma’in.
Amma ba’ad;
Lallai wanda yake son Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama zai fifita
shi akan duk abin da yake da girma
ko daraja ko tsada a gunsa. Domin
son Allah da manzonsa sune imani,
kuma imanin bawa bazai cika ba sai
da su. Allah subhanahu wa ta’ala
yace:
“ kace idan har iyayenku da
‘ya’yanku da ‘yan uwanku da
matanku da danginku da dukiyar da
kuka tsuwurwurta da kasuwancin da
kuke jin tsoron tasgaronsa da gidaje
da kuke yarda dasu sune suka fi
soyuwa a gareku daga Allah da
Manzonsa da jihadi saboda Allah ;to
ku zauna har Allah ya zo da
al’amarinsa, allah baya shiryar da
fasikai” {Tauba :24}
Wannan ayar nassi ce karara a bisa
wajibcin kaunar Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama,da
wajibcin gabatar da wannan kaunar
akan duk wani abin kauna.
Alkali Iyadh yace: “wannan ayar ta
isa wajen zaburarwa da fadakarwa da
shiryarwa da zama hujja ta gaske a
bisa wajibcin kaunar Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama da
cancantarsa da wannan soyayyar,
domin Allah ya kwankwashi wadanda
dukiyarsu da iyalansu da ‘ya ‘yansu
suka fi soyuwa a garesu fiye da Allah
da manzonsa,kuma yayi musu narko
cewa su jira har Allah ya zo da
al’amarinsa,sannan ya fasikantar da
su, ya kuma sanar da su cewa sun
bacewa hanya madaidaiciya, Allah ba
zai shiryar da su ba.
Hakanan kuma wanda ya yi la’akari
da wannan ayar zai ga cewa umarnin
bai tsaya ga samuwar soyayya ga
Allah da Manzonsa kadai ba, barima
dai dole ne sai wannan son ya zama
sama da son duk wani abu wanda ba
su ba.
Wa sallallahu wa sallama ala
Nabiyyina Muhammad wa ala alihi wa
sahbihi ajma’in.

Mece ce alamar son Manzon Allah (S.A.W)?( Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

Amsa:
Kafin mu amsa wannan tambayar ya
na da kyau muyi wa kanmu
wadannan tambayoyin:
-Mece ce soyayya?
-Mene ne yake sa a so mutum?
-Mene ne rabe-raben so?
-Mece ce alamar so?
Daga nan kuma sai musan mece ce
hakikanin soyayyar Manzon Allah
(S.A.W)?
Mece ce soyayya?
Hafiz Ibin hajar babban malamin
hadisin nan da yayi sharhin sahihul
bukhari yace: haqiqanin soyayya
awajen masana; wata aba ce da ba’a
iya bayyanata,mai yinta kawai shi ne
ya san yadda yake jinta,amma baya
yiwuwa ya furta yadda take.
Mallam ibnul Qayyim yace: Ba’a
bayyana soyayya da wani bayani fiye
da ace mata soyayya. Duk abin da
za’a bayyana game da ita ba zai kara
mata komai ba sai buya,bayaninta
kawai shi ne samuwarta, ba kuma a
sifantata da wata siffa fiye da soyyya.
Mutane kawai suna yin maganane
game da abinda yake jawota,da
abinda yake wajabta ta, da
alamominta da shaidunta da abinda
ake samu idan anyi ta.
Mene ne yake sa aso mutum a
dabi’ance?
Akan so mutum a dabi’ance saboda
abubuwa masu yawa. Kadan daga
ciki sune kamar haka:
– Akan so mutum don yawan
kyautatawarsa,
-ko don kyawun surarsa wadda take
burge mutane,
– ko don cikar kamalarsa,
-ko baiwar ilmi, ko mulki, ko dukiya,
ko wani abu wanda yake burge
mutane.
Haka kuma akan so mutum don
kyawawan halayensa na gari ko kuma
saboda amfanarwarsa ga al’umma.
Manzon Allah (S.A.W) kuwa ya
tattare dukkan wadannan sababbai da
ninkin-ba-ninkinsu wadanda suke sa
a so mutum.
Don haka ya zama wajibi a so shi fiye
da kowane irin mahluki.
Tambaya;
Menene rabe raben so?
Amsa;
Imam ibn bazzar da alkali Iyadh da
wasunsu sunce soyayya ta kasu kaso
uku:
1)- Soyayya don girmamawa da
taimakawa; kamar soyayyar ‘ya ‘ya ga
iyayensu.
2)- soyayyar tausayi da jin kai;
kamar soyayyar iyaye ga ‘ya’yansu
3- Soyayyar bani in baka; ita ce ke
sanya kyautatawa wanda ya kyautata
maka; kamar soyayyar da sauran
al’umma suke wa junansu.
Idan muka kalli wadannan rabe-rabe
da sababbai da suke sa a so mutum
zamu ga cewa Manzon Allah (S.A.W)
ya tattare dukkaninsu.
Don haka ibn Bazzar yace: “wanda
yake da cikakken imani ya san
Manzon Allah (S.A.W) ya fi girman
hakki akansa fiye da hakkin kansa
akan kansa, haka zalika hakkin
iyayensa da na ‘ya’yansa da na
mutanen duniya baki daya.
Domin da imani da kaunar Manzon
Allah (S.A.W) ne Allah ya tserar da
mu daga wuta kuma ya shiryar da mu
daga bata.
Mece ce alamar son Manzon Allah
(S.A.W)?
Imam alkali Iyadh yace: “kusani, lallai
duk wanda ya so abu dole zai fifita
shi akan komai ,kuma zai fifita binsa
kwabo da kwabo.
Idan kuwa bai zama haka ba to
sonsa ba na gaskiya ba ne,da’awar
son kawai yake yi.
Mai son Manzon Allah (S.A.W) da
gaske shine wanda alamomin
soyayya suke bayyana a gare shi
kamar haka:
-Na farkon su shi ne koyi da shi.
-Aiki da sunnar sa.
-Bibiyar zantukansa da aiyukansa.
-Kwatanta umarninsa.
-Nisantar hane-hanensa.
-Ladabtuwa da ladabansa, a halin
wahala da yalwa,da nishaxi da
damuwa.
Abinda yake karfafa wannan shine
fadin Allah (S.W.T):
ma’ana:
ka fada musu ya kai wannan annabi
mai girma, idan kun kasance kuna
son Allah, to ku bi ni sai Allah ya so
ku, kuma ya gafarta zunubanku. lallai
Allah mai yawan gafara ne mai yawan
jinkai”{al-imrana:31}
Wannan ayar ta nuna cewa biyayya
ita ce matakin farko na soyayya.
Sannan alkali ya ci gaba da cewa:
Da fifita abin da ya shar’anta ko
yakwadaitar da yinsa fiye da son
zuciyarka da sha’awarka.saboda
fadin Allah s.w.t:
Ma’ana:
“Wadanda suka riki Madina wurin
zamansu(al-ansar) da imani kafin su
(muhajirun) suna kaunar wadanda
suka yi hijira zuwa garesu,(wato
manzon Allah da muhajirun)kuma
basa jin wani kyashi a zuciyarsu
game da abinda Allah ya bawa
(muhajirai na falala da matsayi da
daukaka da gabata a cikin Ambato da
matsayi), kuma suna fifita su
(muhajirai) akan kansu ko da kuwa
suna da matsananciyar bukata.”
Imam addabari da imam assuyidi
kuwa sun fassara ayar da cewa:
“Wadanda suka riki madina wurin
zamansu(al-ansar) da imani kafin su
(muhajirun) suna kaunar wadanda
suka yi hijira zuwa garesu,(wato
manzon Allah da muhajirun)kuma
basa jin wani kyashi a zuciyarsu
game da abinda Manzon Allah
(S.A.W) ya bawa (muhajirai da shi na
ganima da fai’i) kuma suna fifita su
(muhajirai) akan kansu ko da kuwa
suna da matsananciyar bu tata.”
Sannan alkali iyadh ya ambaci hadisi
da isnadinsa zuwa anas bn malik
(r.a) yace:
Ma’ana:
ya kai Dan qaramin Dana, idan ka
sami iko ka wayi gari ko ka yammata
ba tare da wani kulli a zuciyar ka
game da wani ba to ka aikata:
wannan yana daga sunnata,wanda ya
raya sunnata haqiqa ya soni.wanda
ya soni zai kasance tare da ni a cikin
aljana.
Sai alqali iyadh yace:wanda ya
siffantu da waxannan sifofi da suka
gabata to shi ne mai cikakkiyar
soyayya ga allah da
manzonsa.wanda kuma yasa va
musu a xaya daga cikin abubuwan da
aka ambata to wannan soyayyarsa
tauyayyiya ce,duk da ba za’a kore
musu soyayyar gaba daya ba.
Haka dai. yayi ta kawo alamomin da
su ke nuna kaunar Manzon Allah
(S.A.W) ga wanda ya siffantu da su.
Acikin wannan littafi na sa mai
albarka (asshifa). Ya rage wa mai
hankali da tunani ya kalle su da idon
basira don ya ga a da’awar da yake
yita son Manzon A awane aji yake?
Kuma ya yi wa kansa adalci wajen
gane cewa anya kuwa ba yaudararsa
ake yi ba wajen nuna masa abin da
Manzon Allah (S.) bai yi ba a ce
masa shi ne qaunar Manzon Allah
(a) ? Allah ka bamu ganewa amin.
Wa sallallahu wa sallama ala
nabiyina Muhammad wa ala a’lihi wa
sahbihi ajma’in’.

FALALAR SAHABBAI( Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

Alhamdu lillahi rabbil A’lamin, wa
Sallallahu wa sallama ala Nabiyyina
Muhammadin Wa ala a’alihi wa
sahbihi ajma’in.
Amma ba’ad, hakika hadisi ya tabbata
daga Anas Bin Malik radhiyallahu
anhu ya ce;
ﻛﺎﻧﺖ ﺍﻷﻧﺼﺎﺭ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﺨﻨﺪﻕ ﺗﻘﻮﻝ
ﻧﺤﻦ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺑﺎﻳﻌﻮﺍ ﻣﺤﻤﺪﺍ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺠﻬﺎﺩ ﻣﺎ ﺣﻴﻴﻨﺎ ﺃﺑﺪﺍ
ﻓﺄﺟﺎﺑﻬﻢ
ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻻ ﻋﻴﺶ ﺇﻻ ﻋﻴﺶ ﺍﻵﺧﺮﻩ ﻓﺄﻛﺮﻡ ﺍﻷﻧﺼﺎﺭ
ﻭﺍﻟﻤﻬﺎﺟﺮﻩ
Ma’ana
Ansar sun kasance a yayin da suke
haka ramin khandaku suna cewa;
“Mu ne wadanda suka yiwa Manzon
Allah sallallahu alaihi wa sallama
mubaya’a akan jihadi muddin muna
raye har abada”. Sai Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama ya ce;
“Ya Ubangiji babu wata rayuwa sai
rayuwar lahira.
Ya Allah ka girmama Ansar da
muhajirai”
‘Yan uwa wannan ya nuna bai halatta
wani mutun ya zagi sahabbai wadan
suke kaunar Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama shima yake
kaunarsu ba, duk wanda ku ka ji yana
zaginsu ku Sani wannan tababbe ne,
yayi asara duniya da lahira.
wa Sallallahu wa sallama ala
Nabiyyina Muhammadin Wa ala
a’alihi wa sahbihi ajma’in.

FATAWOYIN LAYYA2(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

A wannan darasi za mu amsa
tambayoyi kamar haka;
*Tambaya:
Mene ne sharuddan layya?
AMSA:
Yana daga cikin sharuddan layya:
abin da za a yanka, lallai ya
kasance daga cikin “bahimatul
anʿām” (dabbobin ni’ima), irin su:
rakuma da shanu da awaki da
tumaki). Domin haka, ba ya cikin
sharuddan layya, a yi ta da namun
daji, kuma ba za a yanka kaji da
sauran tsuntsaye ba, kamar yadda
wasu daga cikin ‘yan Zahiriyyah
suka tafi a kai. Dalili kuwa fadin
Ubangiji subhanahu wa ta’ala
cewa:
ﻭﻟﻜﻞ ﺃﻣﺔ ﺟﻌﻠﻨﺎ ﻣﻨﺴﻜﺎ ﻟﻴﺬﻛﺮﻭﺍ ﺍﺳﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﻣﺎ
ﺭﺯﻗﻬﻢ ﻣﻦ ﺑﻬﻴﻤﺔ ﺍﻟﺄﻧﻌﺎﻡ (34) … ﺍﻟﺤﺞ: ٣٤
Ma’ana:
Kowacce al’umma mun sanya
musu ibadunsu, domin su ambaci
sunan Allah a bisa abin da (Allah)
ya arzuta su da shi daga cikin
dabbobin ni’ima…
Wannan aya ta nuna cewa,
Ubangiji subhanahu wa ta’ala ya
ambaci dabbobin ni’ima ne, kuma
ya nuna cewa lallai ne idan za a
yanka su, a ambaci sunansa.
Amma ayar ba ta ambaci cewa ana
iya layya da namun daji ba, ko
tsuntsaye, kamar kaji da sauransu.
Kuma koda a cikin dabbobin ni’ima
din ba a yankawa sai wacce ta cika
wadannan sharuddan:
1- Shanu: Sai sun cika shekara
biyu zuwa sama.
2-Raquma: Sai sun cika shekara
biyar zuwa sama.
3-Tumaki da Awaki: Sai sun cika
shekara daya zuwa sama. Sai dai
idan ya ta’azzara ba a samu
shekararriya ba, to babu laifi a
yanka wacce ba ta shekara ba
amma ta kusa cika shekara a cikin
raguna ko awaki (watau jaz’a),
saboda hadisin da aka karbo daga
Jabir Ibn Abdullah radhiyallahu
anhuma ya ce: Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama ya ce:
ﻟﺎ ﺗﺬﺑﺤﻮﺍ ﺇﻟﺎ ﻣﺴﻨﺔ ﺇﻟﺎ ﺃﻥ ﻳﻌﺴﺮ ﻋﻠﻴﻜﻢ ﻓﺘﺬﺑﺤﻮﺍ
ﺟﺬﻋﺔ ﻣﻦ ﺍﻟﻀﺄﻥ.
Ma’ana:
Kada ku yanka sai shekararriya,
sai dai idan ya gagareku , sai ku
yanka wacce ake kira jaz’a daga
raguna.
Haka kuma, ana so dabbar da za a
yi layya da ita ta kasance
kubutacciya daga aibu. Saboda
hadisin da aka karbo daga Bara’u
Ibn Azib radhiyallahu anhuma ya
ce: Manzon Allah sallallahu alaihi
wa sallama ya ce:
ﻻ ﻳﻀﺤﻰ ﺑﺎﻟﻌﺮﺟﺎﺀ ﺑﻴﻦ ﻇﻠﻌﻬﺎ ﻭﻻ ﺑﺎﻟﻌﻮﺭﺍﺀ ﺑﻴﻦ
ﻋﻮﺭﻫﺎ ﻭﻻ ﺑﺎﻟﻤﺮﻳﻀﺔ ﺑﻴﻦ ﻣﺮﺿﻬﺎ ﻭﻻ ﺑﺎﻟﻌﺠﻔﺎﺀ
ﺍﻟﺘﻲ ﻻ ﺗﻨﻘﻲ
Ma’ana:
Ba a yanka ramammiya wacce
ramarta ta bayyana, ko gurguwa
wacce gurguntakarta ta bayyana,
ko mara lafiyar da rashin lafiyarta
ta bayyana, Ko me ido daya.
Banda wadannan siffofi na
dabbobi, akwai wasu siffofin. saidai
hadisan ba su inganta ba, don
haka ba mu kawo su a nan ba.
Kuma lallai ne abinda za a yanka
na layya, ya kasance mallakarsa
aka yi ta hanyar halal, ba ta hanyar
haram ba. Wato wajibi ne ya
kasance ba na sata ko kwace ba
ne, kuma ba dabbar da aka bayar
jingina ko amana ba ce.
Kuma ya kamata mai yin layya ya
sani cewa ba cewa aka yi ya yi
azumi ko rikon baki ba. Domin
haka, ba a hana shi ci ko shan abin
sha ba matukar yana bukata.
*Tambaya:
Yaushe ya kamata a yanka abin
layya?
AMSA:
Jumhurun malamai sun tafi a kan
cewa, ana yanka abin layya ne,
bayan sallar idi ko da liman bai
yanka ba. Dalilinsu kuwa shi ne
fadin Manzon Allah sallallahu alaihi
wa sallama cewa:
ﻣﻦ ﻛﺎﻥ ﺫﺑﺢ ﺃﺿﺤﻴﺘﻪ ﻗﺒﻞ ﺃﻥ ﻳﺼﻠﻲ ﺃﻭ ﻧﺼﻠﻲ
ﻓﻠﻴﺬﺑﺢ ﻣﻜﺎﻧﻬﺎ ﺃﺧﺮﻯ ﻭﻣﻦ ﻛﺎﻥ ﻟﻢ ﻳﺬﺑﺢ ﻓﻠﻴﺬﺑﺢ
ﺑﺎﺳﻢ ﺍﻟﻠﻪ .
Ma’ana:
Wanda ya yanka abin layyarsa
kafin sallarmu, to, ya sake yanka
wata dabbar maimakonta bayan
sallar idi, wanda kuma bai yanka
ba (sai bayan sallarmu), to, ya
yanka da sunan Allah.
Saidai kuma Imam Mālik ya tafi a
kan sabanin abinda jamhur suka
tafi akai inda ya ke cewa:
Ba a yanka abin layya sai bayan
liman ya yanka nasa.
Dalilinsa kuwa shi ne, hadisin da
aka karbo daga Jabir Ibn Abdullah
radhiyallahu anhu ya ce,
ﺻﻠﻰ ﺑﻨﺎ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻨﺤﺮ
ﺑﺎﻟﻤﺪﻳﻨﺔ ﻓﺘﻘﺪﻡ ﺭﺟﺎﻝ ﻓﻨﺤﺮﻭﺍ ﻭﻇﻨﻮﺍ ﺃﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ
ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻗﺪ ﻧﺤﺮ ﻓﺄﻣﺮ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ
ﻭﺳﻠﻢ ﻣﻦ ﻛﺎﻥ ﻧﺤﺮ ﻗﺒﻠﻪ ﺃﻥ ﻳﻌﻴﺪ ﺑﻨﺤﺮ ﺁﺧﺮ ﻭﻟﺎ
ﻳﻨﺤﺮﻭﺍ ﺣﺘﻰ ﻳﻨﺤﺮ ﺍﻟﻨﺒﻲ. ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
Ma’ana:
Mun yi salla tare da Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama a
Madina ranar babbar salla, sai
wasu mazaje suka je suka yi
yanka, suna tsammani Manzon
Allah sallallahu alaihi wa sallama
ya yi yanka, sai Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama ya ce:
duk wanda ya yi yanka kafin na yi,
to ya sake yankansa. Ya kara da
cewa: Kada su yanka har sai
Annabi sallallahu alaihi wa sallama
ya yanka.
Wannan shi ne zance mafi rinjaye
domin wannan hadisin da Imam
Malik ya kafa hujja da shi ya fada
karara cewar ba’a yanka sai bayan
liman yayi yankan sa, sabanin
dalilin jamhur. Don haka sai
mutum ya hakura har liman ya
yanka. Idan kuma mutum yana
nesa da gari ne, sai ya kintaci
lokacin da ya kamata a ce liman ya
yanka dabbar layyarsa, sai ya
yanka tasa. Wanda kuma ya yanka
kafin salla, to namansa ba na layya
ba ne, ya zama naman miya
kenan, ko ya sani ko bai sani ba.
Saboda haka sai ya sake yanka
wata maimakonta.
Dalili kuwa shi ne: wani sahabi
Uwaīmir Ibn Ashkar radhiyallahu
anhum ya taba yanka dabbar
layyarsa kafin sallar īdī, sai
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama ya ce:
ﺃﻋﺪ ﺃﺿﺤﻴﺘﻚ .
Ma’ana:
Ka sake yanka wata a
maimakonta.
A nan Annabi sallallahu alaihi wa
sallam bai tambaye shi ko ya sani,
ko bai sani ba. Wallahu a’alam!
*Tambaya:
A ina ya kamata liman ya yanka
abin layyarsa a sunnance?
AMSA:
A bisa koyarwa irin ta Manzon
Allah sallallahu alaihi wa sallama
liman zai yanka abin layyarsa ne a
filin idi, domin al’umma su shaida,
kuma su sami damar yin ta su
layyar, ba tare da wani kokwanto
ba. Dalili kuwa shi ne hadisin Jabir
radhiyallahu anhum ya ce:
ﺷﻬﺪﺕ ﻣﻊ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
ﺍﻷﺿﺤﻰ ﺑﺎﻟﻤﺼﻠﻰ ﻓﻠﻤﺎ ﻗﻀﻰ ﺧﻄﺒﺘﻪ ﻧﺰﻝ ﻣﻦ
ﻣﻨﺒﺮﻩ ﻭﺃﺗﻲ ﺑﻜﺒﺶ ﻓﺬﺑﺤﻪ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺑﻴﺪﻩ.
Ma’ana:
Na halarci idin babbar salla tare da
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama. Bayan ya gama
hudubarsa, sai ya sauka daga kan
minbarinsa, aka kawo masa ragon
layyarsa, sai ya yanka shi da
hannunsa (mai albarka).
Haka kuma an karbo wani hadisin
daga Abdullahi Ibn Umar
radhiyallahu anhum ya ce:
ﺃﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻛﺎﻥ ﻳﺬﺑﺢ ﺃﺿﺤﻴﺘﻪ
ﺑﺎﻟﻤﺼﻠﻰ ﻭﻛﺎﻥ ﺍﺑﻦ ﻋﻤﺮ ﻳﻔﻌﻠﻪ.
Ma’ana:
Hakika Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama ya kasance yana
yanka abin layyarsa a filin idi.
Saboda haka ni ma na kasance ina
aikata hakan.
Don haka sai limamai su yi koyi.

FATAWOYIN LAYYA(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

A yau za mu amsa wadannan
tambayoyi.
*Tambaya:
Wace dabba ya kamata a yi layya
da ita?
AMSA:
Malamai sun yi sabani akan
dabbar da aka fi so a yi layya da
ita;
Imam Mālik da daya daga cikin
riwayar Imam Ahmad suna ganin
cewa: rago shi ne yafi, sai shanu
sannan sai rakuma.
Ibn Abdul Barr ya ce: Imam Mālik
ya ce: ragon da aka fi so a yi layya
da shi, shi ne wanda ba’a fidiye shi
ba, sai wanda aka yi wa fidye, sai
tunkiya, haka kuma awaki, sai
shanu sannan rakuma. Amma idan
hadaya ce, to, rakumi shi ne ya fi,
sai shanu sannan tumaki da awaki.
Dalilinsa shi ne hadisin Anas Ibn
Mālik radhiyallahu anhu ya ce:
ﺃﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺍﻧﻜﻔﺄ ﺇﻟﻰ
ﻛﺒﺸﻴﻦ ﺃﻗﺮﻧﻴﻦ ﺃﻣﻠﺤﻴﻦ ﻓﺬﺑﺤﻬﻤﺎ ﺑﻴﺪﻩ .
Ma’ana:
Hakika Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama ya juya daga
wurin salla ya je ya yi layya da
raguna guda biyu masu fari da baki
kuma masu kaho…
Da kuma hadisin Aliyu Ibn Abī
Xalib radhiyallahu anhu wanda ya
ce:
ﺃﻫﺪﻯ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻣﺎﺋﺔ ﺑﺪﻧﺔ …
Ma’ana:
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama ya yi hadaya da rakuma
dari…
Amma mafi yawan malamai
kamarsu Imam Shāfi’ī da Imam
Abū Hanīfah, haka kuma Imam
Ashhab da Imam Ibn Sha’abān
daga Malikiyyah da sauransu sun
tafi a kan cewa a sha’anin layya da
hadaya rakumi shi ne ya fi, sai.
shanu sannan tumaki da awaki.
Dalilin da suka dogara da shi, shi
ne hadisin da a ka karbo daga Abū
Huraīrah radhiyallahu anhu ya ce:
Hakika Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama ya ce:
ﻣﻦ ﺍﻏﺘﺴﻞ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ ﻏﺴﻞ ﺍﻟﺠﻨﺎﺑﺔ ﺛﻢ ﺭﺍﺡ
ﻓﻜﺄﻧﻤﺎ ﻗﺮﺏ ﺑﺪﻧﺔ ﻭﻣﻦ ﺭﺍﺡ ﻓﻲ ﺍﻟﺴﺎﻋﺔ ﺍﻟﺜﺎﻧﻴﺔ
ﻓﻜﺄﻧﻤﺎ ﻗﺮﺏ ﺑﻘﺮﺓ ﻭﻣﻦ ﺭﺍﺡ ﻓﻲ ﺍﻟﺴﺎﻋﺔ ﺍﻟﺜﺎﻟﺜﺔ
ﻓﻜﺄﻧﻤﺎ ﻗﺮﺏ ﻛﺒﺸﺎ ﺃﻗﺮﻥ ﻭﻣﻦ ﺭﺍﺡ ﻓﻲ ﺍﻟﺴﺎﻋﺔ
ﺍﻟﺮﺍﺑﻌﺔ ﻓﻜﺄﻧﻤﺎ ﻗﺮﺏ ﺩﺟﺎﺟﺔ ﻭﻣﻦ ﺭﺍﺡ ﻓﻲ ﺍﻟﺴﺎﻋﺔ
ﺍﻟﺨﺎﻣﺴﺔ ﻓﻜﺄﻧﻤﺎ ﻗﺮﺏ ﺑﻴﻀﺔ …
Ma’ana:
Wanda ya yi wankan Juma’a ya tafi
masallaci a farkon lokaci kamar ya
nemi kusanci da Allah da yankan
rakumi ne, wanda ya tafi a lokaci
na biyu kamar ya nemi kusanci da
Allah da yankan sa, wanda ya je a
lokaci na uku kamar ya nemi
kusanci da Allah da yankan rago
mai kaho biyu, wanda ya je a
lokaci na hudu kamar ya nemi
kusanci da Allah ne da yankan
kaza, wanda ya je a lokaci na biyar
kamar ya nemi kusanci da Allah ne
da kwai…
Wannan hadisin ya nuna ana
neman kusanci da Allah ne da abin
da ya fi girma, wannan kuwa dalili
ne a bayyane da yake nuna rakumi
yafi. Wadannan malamai suka ce
hadisin da Imam Mālik ya dogara
da shi cewa Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama ya
yanka raguna biyu masu kaho a
layyarsa, wannan abin da Allah ya
hore masa kenan, kuma Annabi
sallallahu alaihi wa sallama bai
nassanta cewa rago ne ya fi ba.
Ibn Taīmiyyah ya ce: ana samun
lada ne gwargwadon gimar abin da
aka yanka.
Wannan fatawar ita ce tafi rinjaye a
kan fatawar su Imam Mālik.
*Tambaya:
Shin layya farilla ce ko sunna?
AMSA:
Hakika layya sunna ce mai karfi
daga cikin sunnonin Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama.
Ubangiji subhanahu wa ta’ala ya
umarci Annabinsa sallallahu alaihi
wa sallama da yin ta a cikin Suratul
Kauthar, inda yake cewa:
ﺇﻧﺎ ﺃﻋﻄﻴﻨﺎﻙ ﺍﻟﻜﻮﺛﺮ (1) ﻓﺼﻞ ﻟﺮﺑﻚ ﻭﺍﻧﺤﺮ (2)
ﺍﻟﻜﻮﺛﺮ١- ٢
Ma’ana:
Hakika mun ba ka Al-Kausara,
saboda haka, ka yi salla ga
Ubangijinka, kuma ka soke
(hadayarka ko layyarka)…
A wata ayar kuma Ubangiji
subhanahu wa ta’ala cewa ya yi:
ﻗﻞ ﺇﻥ ﺻﻠﺎﺗﻲ ﻭﻧﺴﻜﻲ ﻭﻣﺤﻴﺎﻱ ﻭﻣﻤﺎﺗﻲ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ
ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ (162) ﻟﺎ ﺷﺮﻳﻚ ﻟﻪ ﻭﺑﺬﻟﻚ ﺃﻣﺮﺕ ﻭﺃﻧﺎ
ﺃﻭﻝ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻴﻦ (163) ﺍﻷﻧﻌﺎﻡ: ١٦٢ – ١٦٣
Ma’ana:
Ka ce: hakika sallata da yanke-
yankena da rayuwata da mutuwata
duk suna ga Allah Ubangijin talikai,
ba shi da abokin tarayya, kuma da
haka aka umarce ni, kuma ni ne
farkon masu mika wuya.
Kuma Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama ya umarci
al’ummarsa da su yi layya mutukar
suna da ikon yi. Dalili kuwa shi ne
hadisi ya tabbata Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama ya ce:
ﻳﺎ ﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺇﻥ ﻋﻠﻰ ﻛﻞ ﺃﻫﻞ ﺑﻴﺖ ﻓﻲ ﻛﻞ ﻋﺎﻡ
ﺃﺿﺤﻴﺔ .
Ma’ana:
Ya ku mutane! Hakika yana kan
kowanne magidanci da iyalansa
yin layya a kowacce shekara.
(Manzon Allah ya fadi haka ne
alhali yana tsayuwar Arfa).
Haka kuma, hadisi ya tabbata daga
Abū Huraīrah radhiyallahu anhu ya
ce: Manzon Allah sallallahu alaihi
wa sallama ya ce:
ﻣﻦ ﻛﺎﻥ ﻟﻪ ﺳﻌﺔ ﻭﻟﻢ ﻳﻀﺢ ﻓﻼ ﻳﻘﺮﺑﻦ ﻣﺼﻼﻧﺎ .
Ma’ana:
Duk wanda Allah ya ba shi damar
yin layya bai yi ba, to, kada ya
kusanci wurin sallar idinmu.
Wannan hadisin yana nuna narko
ne ga wanda Allah ya ba shi damar
yin layya amma yaki yi.
Kuma ya tabbata cewa Manzon
Allah sallallahu alaihi wa sallama
ya yi layya kamar yadda ya zo a
cikin hadisi daga Anas Ibn Malik
radhiyallahu anhu ya ce:
ﺃﺿﺤﻰ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺑﻜﺒﺸﻴﻦ
ﺃﻣﻠﺤﻴﻦ ﺃﻗﺮﻧﻴﻦ ﺫﺑﺤﻬﻤﺎ ﺑﻴﺪﻩ ﻭﺳﻤﻰ ﻭﻛﺒﺮ ﻭﻭﺿﻊ
ﺭﺟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺻﻔﺎﺣﻬﻤﺎ .
Ma’ana:
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama ya yanka raguna biyu
masu kahonni guda biyu farare tas,
da hannunsa mai albarka, a
matsayin layyarsa, sannan ya
ambaci sunan Allah, ya girmama
shi (watau a lokacin yin yanka ya
kasance yana cewa Bismillahi,
Allahu Akbar!) Kuma ya dora
kafarsa akan wuyansu.
Wannan ke nuna cewa lallai layya
sunna ce mai karfi, ga wanda Allah
ya ba shi iko. Kuma malamai sun
hadu a kan cewa: ita layya tana
daga cikin ibada, amma ga wanda
Allah ya ba shi iko kawai.
*Tambaya:
Wace irin falala da alherai Ubangiji
subhanahu wa ta’ala ya tanadar
wa mai yin layya?
AMSA:
Ubangiji subhanahu wa ta’ala ya
tanadarwa mai yin layya alkhaīrai
da dama, amma ga kadan daga
ciki:
1-Ubangiji subhanahu wa ta’ala zai
sa shi daga cikin masu tsoronsa
idan har ya kyautata niyya, saboda
Ubangiji subhanahu wa ta’ala ya
ce:
ﻟﻦ ﻳﻨﺎﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﻟﺤﻮﻣﻬﺎ ﻭﻟﺎ ﺩﻣﺎﺅﻫﺎ ﻭﻟﻜﻦ ﻳﻨﺎﻟﻪ ﺍﻟﺘﻘﻮﻯ
ﻣﻨﻜﻢ … ﺍﻟﺤﺞ: ٣٧
Ma’ana:
Ba namanta ko jininta su ne suke
isa wajen Allah ba, sai dai tsoron
Allah, shi ne yake isa wajensa.
2-Haka kuma Ubangiji subhanahu
wa ta’ala zai sanya shi ya kasance
daga cikin managarta. Domin a
karshen ayar, Ubangiji subhanahu
wa ta’ala ya ce:
… ﻭﺑﺸﺮ ﺍﻟﻤﺤﺴﻨﻴﻦ (37) ﺍﻟﺤﺞ: ٣٧
Ma’ana:
… Ka yi wa managarta bushara.
3-Haka kuma Ubangiji subhanahu
wa ta’ala zai sa a rubuta masa
ladan masu raya sunnar Annabi
Ibrahim alaihissalam da Annabi
sallallahu alaihi wa sallama
matukar ba da kudin haram ya yi
layyar ba, kuma ya yine don Allah,
saboda Allah ba ya karbar aiki sai
tsarkakakke.
3-Haka kuma Ubangiji subhanahu
wa ta’ala zai sa shi daga cikin
masu tausayawa fajirai da
makwabta, in dai har ya raba
layyar yadda sunna ta koyar.
Duk da irin falalar da layya take da
ita, akwai hadisai da`ifai (raunana)
da wadanda aka kago a kan falalar
layya, misalin hadisin da aka ce
wai Zaīdu Ibn Arkam radhiyallahu
anhu ya ce:
ﻗﺎﻝ ﺃﺻﺤﺎﺏ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻳﺎ
ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ. ﻣﺎﻫﺬﻩ ﺍﻷﺍﺣﻲ ؟ ﻗﺎﻝ ) ﺳﻨﺔ ﺃﺑﻴﻜﻢ
ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ ( ﻗﺎﻟﻮﺍ ﻓﻤﺎ ﻟﻨﺎ ﻓﻴﻬﺎ ؟ ﻳﺎ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ : ﻗﺎﻝ
) ﺑﻜﻞ ﺷﻌﺮﺓ ﺣﺴﻨﺔ ( ﻗﺎﻟﻮﺍ ﻓﺎﻟﺼﻮﻑ ؟ ﻳﺎ ﺭﺳﻮﻝ
ﺍﻟﻠﻪ : ﻗﺎﻝ ) ﻳﻜﻞ ﺷﻌﺮﺓ ﻣﻦ ﺍﻟﺼﻮﻑ ﺣﺴﻨﺔ )
Ma’ana:
Sahabban Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama sun ce: Ya
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama; mece ce wannan layyar ?
Sai ya ce: “ Sunnar babanku
Ibrahim alaihis salam ce. Sai suka
ce: me za mu samu idan mun yi
ta? Sai ya ce: za ku samu lada ne
da kowane gashi daya na dabbar .
To, wannan hadisin maudū’i ne,
domin a cikin sanadinsa akwai
Nufaīl Ibn Hārith, wanda malamai
suke tuhumar sa da kaga hadisai
na karya, kuma ire-iren wadannan
hadisai suna da yawa.
Haka kuma akwai wani hadisi da’ifi
(mai rauni) shi ma da ake cewa wai
Nana A’ishah ﺭﺿﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ ta
ruwaito cewa Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama ya ce:
ﻣﺎ ﻋﻤﻞ ﺁﺩﻣﻲ ﻣﻦ ﻋﻤﻞ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻨﺤﺮ ﺃﺣﺐ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﻠﻪ
ﻣﻦ ﺇﻫﺮﺍﻕ ﺍﻟﺪﻡ ﺇﻧﻬﺎ ﻟﺘﺄﺗﻲ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻘﻴﺎﻣﺔ ﺑﻘﺮﻭﻧﻬﺎ
ﻭﺃﺷﻌﺎﺭﻫﺎ ﻭﺃﻇﻠﺎﻓﻬﺎ ﻭﺃﻥ ﺍﻟﺪﻡ ﻟﻴﻘﻊ ﻣﻦ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻤﻜﺎﻥ
ﻗﺒﻞ ﺃﻥ ﻳﻘﻊ ﻣﻦ ﺍﻟﺄﺭﺽ ﻓﻄﻴﺒﻮﺍ ﺑﻬﺎ ﻧﻔﺴﺎ .
Ma’ana:
Babu wani aiki mafi soyuwa a
wurin Allah da Dan Adam zai yi a
ranar idin babbar salla, kamar
zubar da jinin dabbar layya. Ya ce
wai, hakika dabbar za ta zo da
kahonta da gashinta da kofatonta.
Hakika jininta zai isa wurin Allah
kafin ya zuba kasa, saboda haka
ku yi ta da dadin rai.
Wannan da ire-irensa, suna da
yawa wadanda lokaci ba zai ba mu
damar kawo su ba a cikin wannan
littafi, sai dai a yi hattara, kuma a
rika tambayar malamai masana
sunnar Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama.
*Tambaya:
Mene ne matsayin wanda Allah ya
ba shi ikon yin layya, amma ya ki
yi?
AMSA:
Hakika wanda Ubangiji subhanahu
wa ta’ala ya ba shi ikon yin layya
amma ya ki yi, ya sabawa sunnar
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama da aikin magabata na
kwarai, kuma (sakamakon abin da
ya yi) shi ne kada ya je sallar idi,
ya yi zamansa a gida. Saboda
hadisin da ya tabbata daga Abū
Huraīrah radhiyallahu anhu ya ce:
Hakika Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama ya ce:
ﻣﻦ ﻛﺎﻥ ﻟﻪ ﺳﻌﺔ ﻭﻟﻢ ﻳﻀﺢ ﻓﻼ ﻳﻘﺮﺑﻦ ﻣﺼﻼﻧﺎ .
Ma’ana:
Wanda Allah ya ba shi yalwar yin
layya, amma bai yi ba, kada ya
kusanci wajen sallar idinmu.
Lallai ba karamar ukuba ba ce;
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama ya hana mutum kusantar
wannan alheri mai dimbin yawa a
wurin da ake neman kusanci ga
Allah da haduwa da al’umma
domin nuna farin ciki, wanda ba a
yinsa daga shekara sai shekara.
*Tambaya:
Wanda Allah ya ba shi abin yin
layya, amma iyayensa ba su samu
ba, shin ya kamata ya yi, ko kuwa
zai ba wa iyayensa ne su yi?
AMSA:
Ya kamata a fahimci cewa, a
wajen sha’anin ibada, yi wa Allah
da Manzonsa biyayya shi ne gaba
da komai. Saboda haka tunda
yake, ita layya ibada ce, wanda
duk Allah ya bai wa dama, sai ya
gabatar da tasa, sannan ya
sayawa iyayensa abin da za su yi
tasu.
Allah ya horewa duk musulmi
masu niyya.

Mece ce layya a shari’ance?(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

Mece ce layya a shari’ance?
AMSA: Layya a shari’a, ita ce
yanka dabba daga cikin dabbobin
ni’ima (Bahimatul An’ām, wato:
rakuma da shanu da tumaki da
awaki), tun daga bayan sallar idi
har zuwa faduwar ranar sha uku ga
watan Zul-Hijja, saboda neman
kusanci ga Ubangiji subhanahu wa
ta’ala. Dalili kuwa shi ne: fadinsa
subhanahu wa ta’ala a cikin suratul
Hajj cewa.
ﻟﻴﺸﻬﺪﻭﺍ ﻣﻨﺎﻓﻊ ﻟﻬﻢ ﻭﻳﺬﻛﺮﻭﺍ ﺍﺳﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻲ ﺃﻳﺎﻡ
ﻣﻌﻠﻮﻣﺎﺕ ﻋﻠﻰ ﻣﺎ ﺭﺯﻗﻬﻢ ﻣﻦ ﺑﻬﻴﻤﺔ ﺍﻟﺄﻧﻌﺎﻡ ﻓﻜﻠﻮﺍ
ﻣﻨﻬﺎ ﻭﺃﻃﻌﻤﻮﺍ ﺍﻟﺒﺎﺋﺲ ﺍﻟﻔﻘﻴﺮ (28) ﺍﻟﺤﺞ: ٢٨
Ma’ana:
Domin su halarci abubuwan amfani
(wato ayyukan hajjinsu da yanke-
yankensu), kuma su ambaci sunan
Allah a cikin kwanakin sanannu,
saboda abin da Allah ya azurta su
da shi na daga dabbobin ni’ima…
Haka kuma Abdullahi Ibn Abbās
radhiyallahu anhuma ya fassara
kwanaki sanannu wadanda suka
zo a ayar da ta gabata da cewa
sune
ﺃﻳﺎﻡ ﺍﻟﻌﺸﺮ،
Ma’ana:
Kwanaki goma na farkon Zul-Hijja.
Sannan kuma ya kara da cewa:
ﺃﻥ ﺍﻟﻤﻌﻠﻮﻣﺎﺕ: ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻨﺤﺮ ﻭﺛﻼﺛﺔ ﺃﻳﺎﻡ ﺑﻌﺪﻩ .
Ma’ana:
Kwanaki sanannu sune: ranar
layya, da kwanaki uku da suke
bayanta.
Sannan ya ci gaba da cewa:
Hakika Ubangiji subhanahu wa
ta’ala ya sanya wannan lokaci ne
domin ambatonsa.
Haka kuma, hadisi ya tabbata daga
Jubaīru Ibn Mud’īm t ya ce:
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama ya ce:
ﻛﻞ ﺃﻳﺎﻡ ﺍﻟﺘﺸﺮﻳﻖ ﺫﺑﺢ .
Ma’ana:
Dukkan ranakun hasken wata
(wato 11 da 12 da 13 ga watan
Zul-Hijjah) ranakun yanka ne.
A kan haka ne kuma magabata
suka tafi, kamar su: Imam Al-Shafi’ī
da Imamul Aūzā’ī da Imam
Hasanul Basrī da Imam Ahmad, da
Imam Mālik da Imam Abū Hanīfah
Allah ya ji kansu baki daya.
Haka kuma, ya tabbata cewa
sahabbai suna yin yanka a cikin
wadannan ranaku.

HUKUNCE HUKUNCEN AIKIN HAJJI DA UMRA Darasi na 14(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

A yayin zaman Mina, ana son
mahajjaci ya yawaita yin zikirai da
hailala da hamdala da salatin
Annabi sallallahu alaihi wa
sallama, musamman bayan an
gama kowace sallar farilla. Haka
kuma, ana son ya yawaita fadin
ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ
ﻭﻟﻠﻪ ﺍﻟﺤﻤﺪ
Ma’ana:
Allah shi ne mafi girma! Allah shi
ne mafi girma! Babu wanda ya
cancanta a bautata masa sai Allah.
Allah shi ne mafi girma! Allah shi
ne mafi girma! Dukkan godiya ta
tabbata ga Allah.
Haka kuma a rika yawan godewa
Allah bisa ni’imar da ya yi, ta
kammala aikin hajji lafiya; sannan
a rika sa rai da kyautata
tsammanin ko Allah ya karbi aikin
hajjin ko bai karba ba. Watau a
kasance ( ﺑﻴﻦ ﺍﻟﺨﻮﻑ ﻭﺍﻟﺮﺟﺎﺀ) tsakanin
fatan rahamar Allah da tsoron
azabarsa . Hakika yin haka yana
daga cikin siffofin Annabawa a
cikin ibadarsu.
Haka kuma ana son a zauna a
Mina na tsawon kwanaki uku, tare
da cewa idan an kwana biyu
kawai, ya wadatar. Amma yin
kwana ukun shine yafi. Manzon
Allah sallallahu alaihi wa sallama
da sahabbansa kwana uku suka yi,
ba kwana biyu ba., kuma babu
shakka, yin hakan shi ne ya fi cika
wajen tsoron Allah, kamar yadda
Alqur’ani ya bayyana.
Amma a halin yanzu mafi yawancin
mutane sun manta da wannan
sunnar, kai ka ce wadannan
kwanaki ukun ma babu su kwata-
kwata. Abin da ya fi daure kai shi
ne, irin yadda za ka ga wasu
manyan malaman da ake koyi da
su, kuma ake sauraren
maganarsu, sun ki cika kwanaki
ukun. Koda yake shari’a ba ta zargi
wanda ya bar Mina bayan kwana
biyu ba, to, amma ya kamata irin
wadannan malamai su rika
dagewa wurin cika kwanakin Mina,
don su bayar da kyakkyawan
misali ga al’umma. Allah ya sa mu
dace, amin.
Dangane da abubuwan da
mahajjata ya kamata su nisanta a
zamansu na kwanakin Mina, wajibi
ne su nisanci duk wani nau’i na
sabon Allah, da ayyukan zubar da
mutunci. Amma idan mutum ya
dubi abubuwan da wadansu suke
aikata wa abin akwai ban tsoro,
musamman ga duk mai tsoron
Allah. Domin za ka ga wadansu
mutane, musamman mutanen
Afrika ta yamma da sauransu, suna
yin fito na fito da dokokin Allah
Ta’ala, suna saba masa a sarari,
kai ka ce ba aikin hajji suke yi ba.
Wani lokaci sai ka ga mace ta caba
ado da kwalliyar da ke jawo
hankalin maza. Abin bai tsaya a
nan ba, har da dauke-dauken
hotuna a cikin shemomi, da
cakuduwa tsakanin maza da mata,
ta yadda hakan zai haifar da fitinar
zina. An sha kama masu aikata irin
wannan laifin, ba sau daya ba, ba
sau biyu ba, musamman mata
masu zaman kansu a Jidda da
birnin Makka, wadanda ba su
samun damar yin fasadi sai a
wannan lokacin. Wani lokaci sai ka
ga karuwan sun dungumo sun zo
Mina, suna jan hankalin mahajjata,
don su yi fasadi da rashin mutunci
a wannan wuri mai albarka. Haka
kuma, wani lokaci ana samun
wadansu marasa tsoron Allah da
suke biyewa barayi, su yi ta sace-
sace a cikin wadannan ranaku
masu albarka.
To, muna kira da babbar murya ga
hukumomin alhazai da su yi aiki
tukuru wajen magance wannan
fasadi. Lallai ne su dauki mataki
mai karfi a kan haka. Domin babu
wanda ya fi karfin doka. Idan kuma
ba za a iya daukar mataki a can
kasa mai tsarki ba, to sai a bari
idan an dawo gida, a hukunta su
daidai gwargwadon irin laifin da
suka yi.
Allah ya kyauta.

HUKUNCE-HUKUNCEN HAJJI DA UMRA Darasi na 13(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

RANAKUN MINA (WATO 11, 12 &
13)
Ibadun da mahajjaci zai yi a
kwanakin Mina sune kamar haka:
Jifan Jamrat: A rana ta daya da ta
biyu da ta uku bayan salla (wato
11-13 ga watan Dhul Hijja).
> Ana jifan jamrat guda uku a
kullun bayan zawalin Rana.
Babu wani dalili a cikin littafin Allah
ko hadisan Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama ko
ayyukan magabata na kwarai da
ke nuna halaccin yin jifa da safe ko
da hantsi kafin rana ta yi zawali.
Saidai wanda yake da uzuri, ko
wadanda suke da rauni, ko masu
gudun cunkoso, za su iya yin
jifansu ne da yamma ko da
daddare, matukar dai alfijir din
washe gari bai keto ba. Dalili a kan
haka na cikin hadisin da ya tabbata
daga Abdullahi Ibn Abbas
radhiyallahu anhu ya ce:
ﻛﺎﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻳﺴﺄﻝ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻨﺤﺮ
ﺑﻤﻨﻰ ﻓﻴﻘﻮﻝ ﻟﺎ ﺣﺮﺝ ﻓﺴﺄﻟﻪ ﺭﺟﻞ ﻓﻘﺎﻝ ﺣﻠﻘﺖ ﻗﺒﻞ
ﺃﻥ ﺃﺫﺑﺢ ﻗﺎﻝ ﺍﺫﺑﺢ ﻭﻟﺎ ﺣﺮﺝ ﻭﻗﺎﻝ ﺭﻣﻴﺖ ﺑﻌﺪ ﻣﺎ
ﺃﻣﺴﻴﺖ ﻓﻘﺎﻝ ﻟﺎ ﺣﺮﺝ
Ma’ana:
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama ya kasance ana yi masa
tambayoyi ranar idi a Mina: Wani
ya ce: na yi aski kafin in yi yanka,
sai ya ce babu komai, wani kuma
ya ce na yi jifa bayan yammaci, sai
ya ce babu komai.
Wannan hadisi yana nuna mana
cewa yin jifa da yamma ya halatta,
domin haka, mara lafiya, da duk
wani mai uzuri, za su iya jira har
sai da yamma ta yi, sannan, su je
su yi jifa.
Haka kuma, hadisi ya tabbata a
cikin Muwadda Malik daga Nafi’u
daga Babansa ya ce:
ﺃﻥ ﺍﺑﻨﺔ ﺃﺥ ﻟﺼﻔﻴﺔ ﺑﻨﺖ ﺃﺑﻲ ﻋﺒﻴﺪ ﻧﻔﺴﺖ ﺑﺎﻟﻤﺰﺩﻟﻒﺓ
ﻓﺘﺨﻠﻔﺖ ﻫﻲ ﻭﺻﻔﻴﺔ ﺣﺘﻰ ﺃﺗﺘﺎ ﻣﻨﻰ ﺑﻌﺪ ﺃﻥ ﻏﺮﺑﺖ
ﺍﻟﺸﻤﺲ ﻣﻦ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻨﺤﺮ ﻓﺄﻣﺮﻫﻤﺎ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻋﻤﺮ
ﺃﻥ ﺗﺮﻣﻴﺎ ﺍﻟﺠﻤﺮﺓ ﺣﻴﻦ ﺃﺗﺘﺎ ﻭﻟﻢ ﻳﺮ ﻋﻠﻴﻬﻤﺎ ﺷﻴﺌﺎ
Ma’ana:
Wata mace `yar dan’uwan Safiyya
Bint Abi Ubaid ta haihu a
Muzdalifa, ba ta samu isowa Mina
ba, sai bayan hudowar rana ita da
Safiyya. Sai Abdullahi Ibn Umar
radhiyallahu anhu ya umarce su da
su yi jifa bayan faduwar rana,
kuma bai ce su yi fidiya ba.
Haka kuma hadisi ya tabbata daga
Nafi’u daga Abdullahi Ibn Umar
radhiyallahu anhu yana cewa:
ﻟﺎ ﺗﺮﻣﻰ ﺍﻟﺠﻤﺎﺭ ﻓﻲ ﺍﻟﺄﻳﺎﻡ ﺍﻟﺜﻠﺎﺛﺔ ﺣﺘﻰ ﺗﺰﻭﻝ
ﺍﻟﺸﻤﺲ
Ma’ana:
Ba a yin jifa a ranaku uku (na
Mina) sai bayan rana ta yi zawali.
Ibn Abdulbarri.
A cikin sharhin wannan hadisin ya
ce:
Wannan fatawa (ta Abdullahi Ibn
Umar radhiyallahu anhu) ita ce
sunnah a wurin dukanin malamai;
babu wani sabani a kanta.
Haka kuma malamai sun yi sabani
a kan wanda ya yi jifa kafin zawali
a wadannan ranaku, Ibn Abdulbarri
ya ce:
-Jamhurum malamai sun tafi a kan
cewa sai ya sake maimaita
wannan jifan bayan rana ta yi
zawali.
A cikinsu wadannan malamai
akwai Imām Mālik da Shāfi’ī, da
mabiyansu, da Imām al-Thaūrī, da
Imām Ahmad, da Ishaq.
-Abu Yusuf da Muhammad da
Imamus Shafi’i sun ce:
Babu laifi ga wanda ya jinkirta jifa
zuwa dare ko safiya. Hujjarsu ita
ce Manzon Allah sallallahu alaihi
wa sallama ya yi rangwame ga
masu kiwon rakuma da kananan
dabbobi wadanda suke da uzuri,
da su yi jifa da daddare amma ba
su yi tun safe ba.
Yana da kyau mutane su sani
cewa Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama bai yi jifa a
ranaku uku na Mina ba sai bayan
zawali, ga shi kuma hadisi ya
tabbata daga Jabir Ibn Abdullah
radhiyallahu anhu cewa Manzon
Allah sallallahu alaihi wa sallama
ya ce:
ﻟﺘﺄﺧﺬﻭﺍ ﻣﻨﺎﺳﻜﻜﻢ…
Ma’ana:
Ku riki ayyukan hajjinku daga gare
ni…
Kuma haka sahabbansa suka
aikata a bayansa, ba tare da an
samu wani sabani a kan haka ba.
Kuma sanannen abu ne cewa
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama ya ce:
ﻣﻦ ﻋﻤﻞ ﻋﻤﻠﺎ ﻟﻴﺲ ﻋﻠﻴﻪ ﺃﻣﺮﻧﺎ ﻓﻬﻮ ﺭﺩ
Ma’ana:
Wanda duk ya aikata wani aiki da
ba shi cikin al’amarinmu (na addini
da muka karantar), to, za a mayar
masa (watau ba za a karba ba).
A wani hadisin kuma Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama cewa
ya yi:
ﻣﻦ ﺃﺣﺪﺙ ﻓﻲ ﺃﻣﺮﻧﺎ ﻫﺬﺍ ﻣﺎ ﻟﻴﺲ ﻣﻨﻪ ﻓﻬﻮ ﺭﺩ
Ma’ana:
Wanda duk ya kaga wani abu a
cikin al’amarinmu (na addini) da
babu shi a ciki, za a mayar masa.
Don haka, lallai ne mahajjata su
nisanci yin jifa kafin zawali a cikin
wadannan ranaku. Yin jifa bayan
zawali shi ne abin da ya tabbata a
cikin Muwadda Malik, kamar yadda
ya gabata.
Amma abin mamaki shi ne,
wadansu dake da’awar su ne suka
fi kowa bin mazhabar Malikiyya
suna yin jifa da safe. Idan ka
tambaye su, sai su ce: wai
malamai sun bayar da fatawa da
halaccin yin haka, kuma suka ce
wannan ita ce fatawar Imām Abū
Hanīfah.
Hakika babu wata hujja mai karfi a
kan haka , kuma shi kansa Imam
Abū Hanīfah, manya-manyan
almajiransa guda biyu, watau Abū
Yusuf da Muhammad al-Shaībānī
sun saba masa.
Ya kamata duk masoyin Manzon
Allah sallallahu alaihi wa sallama
na hakika a gan shi yana aiki da
karantarwar shi sau da kafa,
gwargwadon iko.
Haka kuma, cikar bin mazhabin
Imām Malik shine a ga mutum
yana kokarin bin abin da ya yi
fatawa da shi matukar bai sabawa
Alkur’an da sunnar Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama ba.
Saboda haka ina kira ga mahajjata
da su yi hattara da irin wadannan
fatawoyi. Idan kuwa suna da’awar
uzuri ne, to ya kyautu a fahimci irin
fatawar da magabata suka yi a kan
masu uzuri. Watau an halatta masu
yin jifa bayan faduwar rana ko
kuma da daddare amma ba da
safe ba, kamar yadda hujjoji suka
tabbata a can baya.
Idan aka zo wajen jifa a rana ta
biyu, da rana ta uku sai a fara da
Jamra ta farko, wacce take kusa da
Mina. Za a yi addu’a bayan an yi
jifan, sannan a karasa wurin wacce
ke binta, wato jamra ta tsakiya, sai
a yi irin yadda aka yi a ta farkon.
Daga nan, sai a karasa wajen
Jamra ta uku, wato babbar Jamra,
wacce ke kusa da Makka, a yi jifa.
Amma ba a tsayawa a wurin don
yin addu’a kamar yadda aka yi a ta
daya da ta biyu ba, bayan an yi
jifan. .
A kowace Jamra ana yin jifa da
tsakuwa guda bakwai ne. Idan aka
hada su za a samu tsakuwa ashirin
da daya (21) a kowace rana.

FATAWOYIN GOMAN FARKON ZUL HIJJA Darasi na 2(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

A darasinmu na yau za mu amsa
tambaya ne kamar haka;
Wadanne ibadu ne mafi soyuwa a
wurin Ubangiji subhanahu wa
ta’ala a cikin wadannan kwanaki
goma na farkon Zul-Hijja?
AMSA:
Ibadun da aka fi so a yi a cikin
wadannan kwanaki su ne:-
1- AZUMIN RANAR ARFA: Mafi
soyuwar ibada a wadannan
kwanaki shi ne, azumin ranar Arfa,
koda kuwa ta dace da ranar
Asabar.
Wasu malaman kamar Shaīkh
Nasiruddinil Albānī, da almajirinsa
Aliyu Ibn Hasan al-Atharī, suna
ganin ba za a yi azumin ranar Arfa
ba, in ya dace da ranar Asabar,
saboda sun inganta hadisin da
yake haramta yin azumin nafila
ranar Asabar. Sai dai mafiya
yawan malaman hadisi, sun
raunana wannan hadisin da hujjoji
masu karfin da lokaci ba zai ba mu
dama mu kawo su a nan ba.
Amma dalilan da suke nuna za a
iya yin azumin Arfa koda ya dace
da ranar Asabar sun hada da
hadisin da aka karbo daga Abū
Huraīrah radhiyallahu anhu ya ce:
na ji Manzon Allah sallallahu alaihi
wa sallama yana cewa:
ﻟﺎ ﻳﺼﻮﻣﻦ ﺃﺣﺪﻛﻢ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ ﺇﻟﺎ ﻳﻮﻣﺎ ﻗﺒﻠﻪ ﺃﻭ
ﺑﻌﺪﻩ .
Ma’ana:
Kada dayanku ya yi azumi ranar
Jumu’a, sai dai idan ya yi azumi
kafinta; ko zai yi azumin bayanta
(ana nufin: azumin nafila).
Abin nufi da azumi kafinta; azumin
ranar Alhamis; bayanta kuma shi
ne ranar Asabar. Kamar yadda
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama ya shiga dakin Nana
Juwairiyyah radhiyallahu anha sai
ya riske ta tana azumi ranar
Juma’a, sai ya tambaye ta; kin yi
azumi jiya(alhamis)? Sai ta ce a’a,
sai ya ce Zaki azumci gobe
(asabar)? Sai ta ce a’a. Sai ya ce;
tunda haka ne ji karya azuminki.
Wannan ya nuna ana yin azumin
nafila ranar Asabar.
Haka kuma, an karbo daga Abū
Huraīrah radhiyallahu anhu daga
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama ya ce:
ﻟﺎ ﺗﺨﺘﺼﻮﺍ ﻟﻴﻠﺔ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ ﺑﻘﻴﺎﻡ ﻣﻦ ﺑﻴﻦ ﺍﻟﻠﻴﺎﻟﻲ ﻭﻟﺎ
ﺗﺨﺼﻮﺍ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ ﺑﺼﻴﺎﻡ ﻣﻦ ﺑﻴﻦ ﺍﻟﺄﻳﺎﻡ ﺇﻟﺎ ﺃﻥ
ﻳﻜﻮﻥ ﻓﻲ ﺻﻮﻡ ﻳﺼﻮﻣﻪ ﺃﺣﺪﻛﻢ.
Ma’ana:
Kada ku kebance daren Jumu’a da
yin (kiyamul laili) a tsakanin darare.
Kada kuma ku kebance ranar
Jumu’a da azumi a tsakanin
ranaku, sai dai idan ya kasance
azumi ne da dayanku ya saba
yinsa.
Abin fahimta da fadinsa sallallahu
alaihi wa sallama “sai dai idan ya
kasance azumi ne da dayanku ya
saba yinsa”, yana nufin kamar idan
mutum yana yin irin azumin Annabi
Dāwūd alaihissalam wanda idan
aka yi yau, gobe sai a sha; ko
azumin ayyamul bīd (wato azumin
ranakun 13 da 14 da 15 na
kowane wata); ko Tasu’a da
Ashura (wato 9 da 10 na watan Al-
Muharram); ko azumin ranar Arfa.
Dukkan wadannan azumin nafilfili
ne, idan sun dace da ranar Jumu’a
ko Asabar za a yi su. Shi ya sa
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama ya yi togaciya a cikin
hanin, da cewa: “Sai dai idan ya
kasance azumi ne da dayanku ya
saba yinsa”. Ka ga ya hade dukkan
nau’in azumin nafila da mutum
yake yin sa. Don haka, babu wani
dalili mai karfi da ya hana yin
azumin Arfa idan ya dace da ranar
Jumu’a ko Asabar ita kadai.
Koda yake Aliyu Ibn Hasan Al-
Atharī ya kawo ka’ida ta usulul
fiqihi dake cewa: (idan aka togace
wani abu, togaciyar ba ta shafi
waninsa ba). Misalin wannan
ka’idar shi ne, ba za a yi azumin
nafila ranar Asabar ba sai idan an
yi ranar Juma’ar kafinta, a wannan
togaciyar an ambaci juma’a ne
kadai, don haka ba ta shafi wata
ranar ba.
Amma abin lura anan shine,
togaciyar da Annabi sallallahu
alaihi wa sallama ya yi a hadisin
karshe da cewa: “Sai dai idan ya
kasance azumi ne da dayanku ya
saba yinsa” , ya rushe wannan
ka’idar, amma sai mutum ya lura
da kyau, yayi izina zai gane haka.
Allah shi ne mafi sani.
Kuma hadisi ya tabbata a cikin
Sahīh Muslim dangane da falalar
ranar Arfa daga Abū Qatādah
radhiyallahu anhu cewa: Manzon
Allah sallallahu alaihi wa sallama
ya ce:
ﺻﻴﺎﻡ ﻳﻮﻡ ﻋﺮﻓﺔ ﺇﻧﻲ ﺃﺣﺘﺴﺐ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻥ ﻳﻜﻔﺮ
ﺍﻟﺴﻨﺔ ﺍﻟﺘﻲ ﻗﺒﻠﻪ ﻭﺍﻟﺘﻲ ﺑﻌﺪﻩ .
Ma’ana:
Azumin ranar Arfa yana kankare
zunuban shekarar da ta wuce da
wadda take gabanta.
2- Yawan zikiri da addu’o’i, da
yawaita kabbara da hailala da
hamdala ga Ubangiji subhanahu
wa ta’ala. Domin hadisi ya tabbata
daga Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama ya ce:
ﺧﻴﺮ ﺍﻟﺪﻋﺎﺀ ﺩﻋﺎﺀ ﻳﻮﻡ ﻋﺮﻓﺔ ﻭﺧﻴﺮ ﻣﺎ ﻗﻠﺖ ﺃﻧﺎ
ﻭﺍﻟﻨﺒﻴﻮﻥ ﻣﻦ ﻗﺒﻠﻲ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺣﺪﻩ ﻻ ﺷﺮﻳﻚ ﻟﻪ
ﻟﻪ ﺍﻟﻤﻠﻚ ﻭﻟﻪ ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻭﻫﻮ ﻋﻠﻰ ﻛﻞ ﺷﻲﺀ ﻗﺪﻳﺮ
Ma’ana:
Mafi alkhairin addu’a ita ce addu’ar
ranar Arfa, kuma mafi alkhairin
abin da na fadi (na addu’a) ni da
Annabawan da suka gabace ni, shi
ne: Lā ilaha Illallahu Wahdahū Lā
Sharīkalahū, Lahul Mulku Walahul
Hamdu Wahuwa Alā Kulli Shaī’īn
Qadīr.
Sannan hadisi ya tabbata a cikin
Musnad na Imam Ahmad daga
Abdullahi Ibn Umar radhiyallahu
anhu ya ce: Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama ya ce:
ﻣﺎ ﻣﻦ ﺃﻳﺎﻡ ﺃﻋﻈﻢ ﻋﻨﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻻ ﺃﺣﺐ ﺇﻟﻴﻪ ﺍﻟﻌﻤﻞ
ﻓﻴﻬﻦ، ﻣﻦ ﻫﺬﻩ ﺍﻷﻳﺎﻡ ﺍﻟﻌﺸﺮ، ﻓﺄﻛﺜﺮﻭﺍ ﻓﻴﻬﻢ ﻣﻦ
ﺍﻟﺘﻬﻠﻴﻞ ﻭﺍﻟﺘﻜﺒﻴﺮ ﻭﺍﻟﺘﺤﻤﻴﺪ .
Ma’ana:
Babu wasu ranaku mafiya girma a
wurin Allah, kuma babu wasu
ayyuka mafiya soyuwa a gare shi,
kamar wadannan ranaku goma (na
farkon watan babbar salla). Domin
haka, ku yawaita fadin La Ilaha
Illallahu, da Allahu Akbar, da
Alhamdulillahi a cikinsu.
3- Yawan yin sadaka: Dalilin
yawaita sadaka kuma shi ne:
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama ya yanka rakuma dari na
hadayarsa, kuma ya sa aka rabar
da naman gaba daya har da akalar
rakuman da fatunsu.
Haka kuma, ana son wadannan
zikiran da za a kawo nan gaba, a yi
ta maimaita su a bayan sallar farilla
ko nafila, wannan ya shafi maza da
mata baki daya. Ana son maza su
daga murya, mata kuma su yi
gwargwadon yadda za su jiyar da
kawunansu. Dalili kuwa shi ne:
ﻭﻛﺎﻥ ﻋﻤﺮ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻳﻜﺒﺮ ﻓﻲ ﻗﺒﺘﻪ ﺑﻤﻨﻰ
ﻓﻴﺴﻤﻌﻪ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﻤﺴﺠﺪ ﻓﻴﻜﺒﺮﻭﻥ ﻭﻳﻜﺒﺮ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺄﺳﻮﺍﻕ
ﺣﺘﻰ ﺗﺮﺗﺞ ﻣﻨﻰ ﺗﻜﺒﻴﺮﺍ ﻭﻛﺎﻥ ﺍﺑﻦ ﻋﻤﺮ ﻳﻜﺒﺮ ﺑﻤﻨﻰ
ﺗﻠﻚ ﺍﻟﺄﻳﺎﻡ ﻭﺧﻠﻒ ﺍﻟﺼﻠﻮﺍﺕ ﻭﻋﻠﻰ ﻓﺮﺍﺷﻪ ﻭﻓﻲ
ﻓﺴﻄﺎﻃﻪ ﻭﻣﺠﻠﺴﻪ ﻭﻣﻤﺸﺎﻩ ﺗﻠﻚ ﺍﻟﺄﻳﺎﻡ ﺟﻤﻴﻌﺎ .
Ma’ana:
Sayyadina Umar radhiyallahu anhu
ya kasance yana kabbarori a
hemarsa a Mina, sai mutanen
masallaci su yi ta kabbarori idan
sun ji ya yi. Mutanen kasuwanni
kuma suna ta yi har sai Mina ta
girgiza da kabarbari. Kuma
Abdullahi Ibn Umar radhiyallahu
anhu ya kasance yana yawaita
kabbara a wadannan kwanakin a
Mina bayan salloli a kan
shinfidarsa da cikin rumfarsa da
mazauninsa da matafiyarsa a
wannan kwanakin gaba daya.
Sannan kuma
ﻭﻛﺎﻧﺖ ﻣﻴﻤﻮﻧﺔ ﺗﻜﺒﺮ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻨﺤﺮ ﻭﻛﻦ ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ ﻳﻜﺒﺮﻥ
ﺧﻠﻒ ﺃﺑﺎﻥ ﺑﻦ ﻋﺜﻤﺎﻥ ﻭﻋﻤﺮ ﺑﻦ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻌﺰﻳﺰ ﻟﻴﺎﻟﻲ
ﺍﻟﺘﺸﺮﻳﻖ ﻣﻊ ﺍﻟﺮﺟﺎﻝ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﺴﺠﺪ .
Ma’ana:
Nana Maimuna ﺭﺿﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ ta
kasance tana kabbara a ranakun
Mina. Haka kuma mata da maza
sun kasance suna yin kabbara a
bayan Abānu Ibn Usman da Umar
Ibn Abdul’azīz a ranakun Mina (a
masallaci).
4- YIN LAYYA: Haka kuma ana
son mutum ya nemi kusanci da
Ubangiji subhanahu wa ta’ala da
yin layya.
Wannan bayaninta zai zo nan
gaba insha’ Allahu.

HUKUNCE-HUKUNCEN AIKIN HAJJI DA UMRA Darasi na 12(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

RANAR 10 GA WATA
Idan Alhaji ya kwana a Muzdalifa
ranar Arafa ya wayi gari ranar 10
ga wata, idan yayi sallar asuba sai
ya isa Mash‘arul Haram
(masallacin Muzdalifa), idan bai
samu guri a da’irarsa ba zai tsaya
a duk inda ya samu a Muzdalifa,
sai ya fuskanci Alkibla ya yawaita
addu‘oi da zikiri da salati da
kabarbari.
-Idan gari yayi haske sosai kafin
fitowar rana sai ya tafi Mina. Yana
iya tsintar tsakonkonin yin jifa guda
7 a kan hanyarsa, (girmansu
gwargwadon gabar dan yatsan
hannu,) amma ba zai wanke su ba
domin wanke su bidi‘a ne.
-Idan ya isa Mina zai jefi Jamratul
Akaba da wadannan tsakonkonin.
-Daga nan sai yayi yanka.
-Bayan nan sai yayi aski ko yayi
saisaye, amma yin askin yafi. Su
kuwa mata sai su aske karshen
gashinsu, gwargwadon gabar
yatsa.
-Daga nan yana iya sanya kayan
gida, sai ya tafi Makka yayi
Dawaful Ifadah (amma ba zai yi
sassarfa a zagaye ukun farko
kamar yadda yayi a baya ba).
– Idan Tamattu’I yake yi sai ya je
yayi sa‘ayi tsakanin Safa da
Marwa. Su kuwa masu yin Ifradi ko
Kirani indai sun riga sunyi sa‘ayi na
farko ba sai sun maimaita ba.
-Idan ya yi sa’ayin sai ya tafi Mina
don yin kwanakin Mina kwana 2 ko
3 wadanda karin bayani zai zo a
kansu insha Allahu.

Fatawoyin Falalar Goman Farko Na Watan Babbar Salla Da Layya Da Sallar idi(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

Godiya ta tabbata ga Allah
Ubangijin talikai. Tsira da amincin
Allah su kara tabbata ga Annabi
Muhammadu sallallahu alaihi wa
sallama da iyalan gidansa, da
sahabbansa.
Bayan haka, wannan littafi ya
kunshi bayanai a kan hukunce-
hukuncen layya da falalar kwanaki
goma na farkon watan Zul-Hijja.
Kuma littafin ya samu ne
sakamakon bukatar da ake da ita
ta fahimtar wannan babbar ibada
karkashin koyarwar Alkur’ani da
Sunnar Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama bisa fahimtar
magabata na kwarai.
Sakamakon muhimmancin da
wannan al’amari yake da shi, na
kuduri aniyar tunatar da ku,
musamman wadanda suke nesa,
da wadansu kasashe wadanda
wnnan Littafi bai je ba.
Muna rokon Ubangiji subhanahu
wa ta’ala ya kyautata niyyarmu ya
sanya wannan aiki ya zama
karbabbe a wurinsa, sannan ya
yafe mana kurakuranmu, āmīn.
ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ
Darasi na 1
A wannan darasi za mu amsa
tambaya kamar haka;
Mene ne falalar ranaku goman
farkon Zul-Hijja?
AMSA:
Hakika wadannan ranaku,
ranakune ne masu falala, kamar
yadda Ubangiji subhanahu wa
ta’ala ya fada a cikin littafinsa mai
tsarki cewa;
ﻭﺍﻟﻔﺠﺮ (1) ﻭﻟﻴﺎﻝ ﻋﺸﺮ 2) )
Ma’ana:
Ina rantsuwa da ketowar alfijir,
kuma ina rantsuwa da darare
goma (ma’ana ranaku gona na
farkon Zul hijja).
Kuma hadisi ya tabbata daga
Abdullahi Ibn Abbas radhiyallahu
anhu ya ce: Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama ya ce:
ﻣﺎ ﺍﻟﻌﻤﻞ ﻓﻲ ﺃﻳﺎﻡ ﺃﻓﻀﻞ ﻣﻨﻬﺎ ﻓﻲ ﻫﺬﻩ ﻗﺎﻟﻮﺍ ﻭﻟﺎ
ﺍﻟﺠﻬﺎﺩ ﻗﺎﻝ ﻭﻟﺎ ﺍﻟﺠﻬﺎﺩ ﺇﻟﺎ ﺭﺟﻞ ﺧﺮﺝ ﻳﺨﺎﻃﺮ
ﺑﻨﻔﺴﻪ ﻭﻣﺎﻟﻪ ﻓﻠﻢ ﻳﺮﺟﻊ ﺑﺸﻲﺀ .
Ma’ana:
Babu wasu ranaku da ayyukan
alkhairi suka fi soyuwa a wurin
Ubangiji subhanahu wa ta’ala
kamar wadannan ranaku (goma na
farkon Zul-Hijja). Sai suka ce: ya
Ma’aikin Allah sallallahu alaihi wa
sallama ko da jihadi fisabilillahi
ne? Sai Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama ya ce: Ko da
jihadi fisabilillahi ne, Sai dai
mutumin da ya fita jihadi da ransa
da dukiyarsa kuma bai koma gida
da wani abu ba (ma’ana: ya yi
shahada a fagen fama har da
dukiya baki daya).
Haka kuma, an karbo daga Jabir
Ibn Abdullah radhiyallahu anhu ya
ce: Manzon Allah sallallahu alaihi
wa sallama ya ce:
ﺃﻓﻀﻞ ﺃﻳﺎﻡ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ ﺍﻟﻌﺸﺮ ﻳﻌﻨﻲ ﻋﺸﺮ ﺫﻱ ﺍﻟﺤﺠﺔ ﻗﻴﻞ
ﻭﻻ ﻣﺜﻠﻬﻦ ﻓﻲ ﺳﺒﻴﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻗﺎﻝ ﻭﻻ ﻣﺜﻠﻬﻦ ﻓﻲ ﺳﺒﻴﻞ
ﺍﻟﻠﻪ ﺇﻻ ﺭﺟﻞ ﻋﻔﺮ ﻭﺟﻬﻪ ﺑﺎﻟﺘﺮﺍﺏ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ
Ma’ana:
Mafifitan ranakun duniya su ne
ranaku goma (na farkon Zul-Hijja).
Sai aka ce da shi: babu
kwatankwacinsu ko a jihadi fi
sabilillahi? Sai ya ce: babu
kamarsu sai dai mutumin da aka
turmuza fuskarsa a cikin turbaya
(Ma’ana: an kashe shi, ya yi
shahada a fagen fama).
Don haka Sa’īd Ibn Jubaīr ya
kasance yayin da ranaku goma na
farkon Zul-Hijja suka shiga, yana
yawaita ibada a cikinsu.
Don haka nake kira da cewa
Yana da kyau ga dukkan mai
kaunar Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama, kuma yake son
samun babban rabo da ya kasance
yana kara kyautata ayyukansa a
cikin wadannan ranaku.
Wa sallallahu wa sallama ala
Nabiyyina Muhammadin wa ala
alihi wa Sahbihi ajma’in.

HUKUNCE-HUKUNCEN AIKIN HAJJI DA UMRA Darasi na 11(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

SIFFAR HAJJI A RARRABE:
RANAR 8 GA WATA
-Alhajin da yake akin hajji na
Kirani ko Ifradi, kasancewar suna
cikin ihiraminsu, sai su tafi Mina.
Shi kuwa mai tamattu‘i wanda ya
cire ihiraminsa tun bayan ya
kammala aikin Umra, a wannan
rana ta 8 ga wata, sai ya yanke
farce, ya aske duk wani gashi
wanda bukatar aske shi ka iya
tasowa.
-Sai yayi wanka ya sanya
ihiraminsa daga inda yake a
Makka.
-Idan ya kasance Alhaji ya haure
mikati, don zuwa ziyara ko wani
al’amari, anso masa ya sake
shigowa Makka yana me umra.
-Idan lokacin daukar haramarsa
lokacin sallah ne, ta farilla ko ta
nafila, anso yayi sallah sannan
yayi harama yace:
ﻟﺒﻴﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺣﺠﺎ
idan kuma ba lokacin sallah ba ne,
ba sai yayi wata sallah ba.
-Alhaji zai yawaita talbiyyah akan
hanyarsa ta zuwa Mina, kuma
anso sallar azahar ta riske shi
acan.
-Zai yi sallolin azahar da la‘asar,
kowaccensu kasaru kuma akan
lokacinta.
-Alhaji ya kula da yawan karatun
Kur‘ani da yin talbiyyah da istigfari
da hailala da salatin Annabi
sallallahu alaihi wa sallama.
RANAR 9 GA WATA:
-Idan ya wayi gari ranar 9 ga wata,
wato ranar arafa, sai ya tafi filin
Arfa. Anso ya isa kafin azahar, sai
ya bi liman ya sallaci azahar da
la‘asar kowacce kasaru, ana idar
da wannan a tayar da dayan.
Wanda kuwa bai sami zuwa da
wuri ba sai ya hadu da ire-irensa
su yi jam‘i a cikin shema.
-Wadanda shemar su take wajen
filin arfa wajibi ne suyi kokari su
shiga da‘irar filin arafa koda bayan
faduwar rana ne domin babu hajji
ga wanda bai tsaya a Arafa ba.
-Alhajin da ya sami shiga arafa da
abin hawansa, anso ya fuskanci
alkibla yana akansa, idan bai samu
ba ya tsaya a tsaye, idan ba zai iya
ba sai ya zauna, ya daga hannu ya
yita addu‘a har faduwar rana ko
kuma idan ya gaji sai ya huta.
-Alhaji ba zai bar Arafa ba har sai
rana ta fadi, kuma ba zai yi sallar
magrib ba har sai ya isa Muzdalifa.
-zai yi sallar magriba da isha‘i a
lokaci daya a Muzdalifa, kuma
babu sallar nafila a tsakanin su.
-Alhaji zai kwana a Muzdalifa
sannan ya isa Mash‘arul Haram
bayan sallar asuba, sai ya tsaya a
tsaye yana fuskantar Alkibla, yana
yawaita hamdala da hailala da
salati da tasbihi d.s.
Wadannan su ne aiyukan ranakun
8 da na 9 ga wata.

HUKUNCE-HUKUNCEN HAJJI DA UMRA Darasi na 10(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

BANBANCIN HAJJI TAMATTU‘I
DA SAURAN NAU’IKAN HAJJI:
Idan Alhaji ko Hajiya sun yi
harama da hajji tamattu‘i ne, idan
ya kammala umra kamar yadda
bayaninta ya gabata filla-filla, sai
ya cire ihiraminsa, ya ci gaba da
sanya kayansa na al‘ada, kuma an
halatta masa abinda aka haramta
masa a baya.
-Alhaji zai ci gaba da sauran
mu’amalolinsa har sai ranar takwas
ga watan Zul-Hajji sai ya mayarda
ihiraminsa yayi harama da aikin
hajji. Wannan shi ake kira aikin
hajji da umra a rarrabe (tamattu‘i).
-Su kuwa masu yin ifradi da kirani
idan sun gama sa‘ayi ba za su yi
aski ko saisaye ba, kuma baza su
cire ihirami ba, kuma ba a halatta
musu komai ba har sai ranar
Arafat, kamar yadda bayani zai zo
a gaba .