FATAWOYIN GOMAN FARKON ZUL HIJJA Darasi na 2(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

A darasinmu na yau za mu amsa
tambaya ne kamar haka;
Wadanne ibadu ne mafi soyuwa a
wurin Ubangiji subhanahu wa
ta’ala a cikin wadannan kwanaki
goma na farkon Zul-Hijja?
AMSA:
Ibadun da aka fi so a yi a cikin
wadannan kwanaki su ne:-
1- AZUMIN RANAR ARFA: Mafi
soyuwar ibada a wadannan
kwanaki shi ne, azumin ranar Arfa,
koda kuwa ta dace da ranar
Asabar.
Wasu malaman kamar Shaīkh
Nasiruddinil Albānī, da almajirinsa
Aliyu Ibn Hasan al-Atharī, suna
ganin ba za a yi azumin ranar Arfa
ba, in ya dace da ranar Asabar,
saboda sun inganta hadisin da
yake haramta yin azumin nafila
ranar Asabar. Sai dai mafiya
yawan malaman hadisi, sun
raunana wannan hadisin da hujjoji
masu karfin da lokaci ba zai ba mu
dama mu kawo su a nan ba.
Amma dalilan da suke nuna za a
iya yin azumin Arfa koda ya dace
da ranar Asabar sun hada da
hadisin da aka karbo daga Abū
Huraīrah radhiyallahu anhu ya ce:
na ji Manzon Allah sallallahu alaihi
wa sallama yana cewa:
ﻟﺎ ﻳﺼﻮﻣﻦ ﺃﺣﺪﻛﻢ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ ﺇﻟﺎ ﻳﻮﻣﺎ ﻗﺒﻠﻪ ﺃﻭ
ﺑﻌﺪﻩ .
Ma’ana:
Kada dayanku ya yi azumi ranar
Jumu’a, sai dai idan ya yi azumi
kafinta; ko zai yi azumin bayanta
(ana nufin: azumin nafila).
Abin nufi da azumi kafinta; azumin
ranar Alhamis; bayanta kuma shi
ne ranar Asabar. Kamar yadda
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama ya shiga dakin Nana
Juwairiyyah radhiyallahu anha sai
ya riske ta tana azumi ranar
Juma’a, sai ya tambaye ta; kin yi
azumi jiya(alhamis)? Sai ta ce a’a,
sai ya ce Zaki azumci gobe
(asabar)? Sai ta ce a’a. Sai ya ce;
tunda haka ne ji karya azuminki.
Wannan ya nuna ana yin azumin
nafila ranar Asabar.
Haka kuma, an karbo daga Abū
Huraīrah radhiyallahu anhu daga
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama ya ce:
ﻟﺎ ﺗﺨﺘﺼﻮﺍ ﻟﻴﻠﺔ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ ﺑﻘﻴﺎﻡ ﻣﻦ ﺑﻴﻦ ﺍﻟﻠﻴﺎﻟﻲ ﻭﻟﺎ
ﺗﺨﺼﻮﺍ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ ﺑﺼﻴﺎﻡ ﻣﻦ ﺑﻴﻦ ﺍﻟﺄﻳﺎﻡ ﺇﻟﺎ ﺃﻥ
ﻳﻜﻮﻥ ﻓﻲ ﺻﻮﻡ ﻳﺼﻮﻣﻪ ﺃﺣﺪﻛﻢ.
Ma’ana:
Kada ku kebance daren Jumu’a da
yin (kiyamul laili) a tsakanin darare.
Kada kuma ku kebance ranar
Jumu’a da azumi a tsakanin
ranaku, sai dai idan ya kasance
azumi ne da dayanku ya saba
yinsa.
Abin fahimta da fadinsa sallallahu
alaihi wa sallama “sai dai idan ya
kasance azumi ne da dayanku ya
saba yinsa”, yana nufin kamar idan
mutum yana yin irin azumin Annabi
Dāwūd alaihissalam wanda idan
aka yi yau, gobe sai a sha; ko
azumin ayyamul bīd (wato azumin
ranakun 13 da 14 da 15 na
kowane wata); ko Tasu’a da
Ashura (wato 9 da 10 na watan Al-
Muharram); ko azumin ranar Arfa.
Dukkan wadannan azumin nafilfili
ne, idan sun dace da ranar Jumu’a
ko Asabar za a yi su. Shi ya sa
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama ya yi togaciya a cikin
hanin, da cewa: “Sai dai idan ya
kasance azumi ne da dayanku ya
saba yinsa”. Ka ga ya hade dukkan
nau’in azumin nafila da mutum
yake yin sa. Don haka, babu wani
dalili mai karfi da ya hana yin
azumin Arfa idan ya dace da ranar
Jumu’a ko Asabar ita kadai.
Koda yake Aliyu Ibn Hasan Al-
Atharī ya kawo ka’ida ta usulul
fiqihi dake cewa: (idan aka togace
wani abu, togaciyar ba ta shafi
waninsa ba). Misalin wannan
ka’idar shi ne, ba za a yi azumin
nafila ranar Asabar ba sai idan an
yi ranar Juma’ar kafinta, a wannan
togaciyar an ambaci juma’a ne
kadai, don haka ba ta shafi wata
ranar ba.
Amma abin lura anan shine,
togaciyar da Annabi sallallahu
alaihi wa sallama ya yi a hadisin
karshe da cewa: “Sai dai idan ya
kasance azumi ne da dayanku ya
saba yinsa” , ya rushe wannan
ka’idar, amma sai mutum ya lura
da kyau, yayi izina zai gane haka.
Allah shi ne mafi sani.
Kuma hadisi ya tabbata a cikin
Sahīh Muslim dangane da falalar
ranar Arfa daga Abū Qatādah
radhiyallahu anhu cewa: Manzon
Allah sallallahu alaihi wa sallama
ya ce:
ﺻﻴﺎﻡ ﻳﻮﻡ ﻋﺮﻓﺔ ﺇﻧﻲ ﺃﺣﺘﺴﺐ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻥ ﻳﻜﻔﺮ
ﺍﻟﺴﻨﺔ ﺍﻟﺘﻲ ﻗﺒﻠﻪ ﻭﺍﻟﺘﻲ ﺑﻌﺪﻩ .
Ma’ana:
Azumin ranar Arfa yana kankare
zunuban shekarar da ta wuce da
wadda take gabanta.
2- Yawan zikiri da addu’o’i, da
yawaita kabbara da hailala da
hamdala ga Ubangiji subhanahu
wa ta’ala. Domin hadisi ya tabbata
daga Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama ya ce:
ﺧﻴﺮ ﺍﻟﺪﻋﺎﺀ ﺩﻋﺎﺀ ﻳﻮﻡ ﻋﺮﻓﺔ ﻭﺧﻴﺮ ﻣﺎ ﻗﻠﺖ ﺃﻧﺎ
ﻭﺍﻟﻨﺒﻴﻮﻥ ﻣﻦ ﻗﺒﻠﻲ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺣﺪﻩ ﻻ ﺷﺮﻳﻚ ﻟﻪ
ﻟﻪ ﺍﻟﻤﻠﻚ ﻭﻟﻪ ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻭﻫﻮ ﻋﻠﻰ ﻛﻞ ﺷﻲﺀ ﻗﺪﻳﺮ
Ma’ana:
Mafi alkhairin addu’a ita ce addu’ar
ranar Arfa, kuma mafi alkhairin
abin da na fadi (na addu’a) ni da
Annabawan da suka gabace ni, shi
ne: Lā ilaha Illallahu Wahdahū Lā
Sharīkalahū, Lahul Mulku Walahul
Hamdu Wahuwa Alā Kulli Shaī’īn
Qadīr.
Sannan hadisi ya tabbata a cikin
Musnad na Imam Ahmad daga
Abdullahi Ibn Umar radhiyallahu
anhu ya ce: Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama ya ce:
ﻣﺎ ﻣﻦ ﺃﻳﺎﻡ ﺃﻋﻈﻢ ﻋﻨﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻻ ﺃﺣﺐ ﺇﻟﻴﻪ ﺍﻟﻌﻤﻞ
ﻓﻴﻬﻦ، ﻣﻦ ﻫﺬﻩ ﺍﻷﻳﺎﻡ ﺍﻟﻌﺸﺮ، ﻓﺄﻛﺜﺮﻭﺍ ﻓﻴﻬﻢ ﻣﻦ
ﺍﻟﺘﻬﻠﻴﻞ ﻭﺍﻟﺘﻜﺒﻴﺮ ﻭﺍﻟﺘﺤﻤﻴﺪ .
Ma’ana:
Babu wasu ranaku mafiya girma a
wurin Allah, kuma babu wasu
ayyuka mafiya soyuwa a gare shi,
kamar wadannan ranaku goma (na
farkon watan babbar salla). Domin
haka, ku yawaita fadin La Ilaha
Illallahu, da Allahu Akbar, da
Alhamdulillahi a cikinsu.
3- Yawan yin sadaka: Dalilin
yawaita sadaka kuma shi ne:
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama ya yanka rakuma dari na
hadayarsa, kuma ya sa aka rabar
da naman gaba daya har da akalar
rakuman da fatunsu.
Haka kuma, ana son wadannan
zikiran da za a kawo nan gaba, a yi
ta maimaita su a bayan sallar farilla
ko nafila, wannan ya shafi maza da
mata baki daya. Ana son maza su
daga murya, mata kuma su yi
gwargwadon yadda za su jiyar da
kawunansu. Dalili kuwa shi ne:
ﻭﻛﺎﻥ ﻋﻤﺮ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻳﻜﺒﺮ ﻓﻲ ﻗﺒﺘﻪ ﺑﻤﻨﻰ
ﻓﻴﺴﻤﻌﻪ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﻤﺴﺠﺪ ﻓﻴﻜﺒﺮﻭﻥ ﻭﻳﻜﺒﺮ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺄﺳﻮﺍﻕ
ﺣﺘﻰ ﺗﺮﺗﺞ ﻣﻨﻰ ﺗﻜﺒﻴﺮﺍ ﻭﻛﺎﻥ ﺍﺑﻦ ﻋﻤﺮ ﻳﻜﺒﺮ ﺑﻤﻨﻰ
ﺗﻠﻚ ﺍﻟﺄﻳﺎﻡ ﻭﺧﻠﻒ ﺍﻟﺼﻠﻮﺍﺕ ﻭﻋﻠﻰ ﻓﺮﺍﺷﻪ ﻭﻓﻲ
ﻓﺴﻄﺎﻃﻪ ﻭﻣﺠﻠﺴﻪ ﻭﻣﻤﺸﺎﻩ ﺗﻠﻚ ﺍﻟﺄﻳﺎﻡ ﺟﻤﻴﻌﺎ .
Ma’ana:
Sayyadina Umar radhiyallahu anhu
ya kasance yana kabbarori a
hemarsa a Mina, sai mutanen
masallaci su yi ta kabbarori idan
sun ji ya yi. Mutanen kasuwanni
kuma suna ta yi har sai Mina ta
girgiza da kabarbari. Kuma
Abdullahi Ibn Umar radhiyallahu
anhu ya kasance yana yawaita
kabbara a wadannan kwanakin a
Mina bayan salloli a kan
shinfidarsa da cikin rumfarsa da
mazauninsa da matafiyarsa a
wannan kwanakin gaba daya.
Sannan kuma
ﻭﻛﺎﻧﺖ ﻣﻴﻤﻮﻧﺔ ﺗﻜﺒﺮ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻨﺤﺮ ﻭﻛﻦ ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ ﻳﻜﺒﺮﻥ
ﺧﻠﻒ ﺃﺑﺎﻥ ﺑﻦ ﻋﺜﻤﺎﻥ ﻭﻋﻤﺮ ﺑﻦ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻌﺰﻳﺰ ﻟﻴﺎﻟﻲ
ﺍﻟﺘﺸﺮﻳﻖ ﻣﻊ ﺍﻟﺮﺟﺎﻝ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﺴﺠﺪ .
Ma’ana:
Nana Maimuna ﺭﺿﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ ta
kasance tana kabbara a ranakun
Mina. Haka kuma mata da maza
sun kasance suna yin kabbara a
bayan Abānu Ibn Usman da Umar
Ibn Abdul’azīz a ranakun Mina (a
masallaci).
4- YIN LAYYA: Haka kuma ana
son mutum ya nemi kusanci da
Ubangiji subhanahu wa ta’ala da
yin layya.
Wannan bayaninta zai zo nan
gaba insha’ Allahu.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories