DARAJAR KWANAKI GOMAN FARKO NA WATAN ZUL HIJJAH(DR IBRAHIM JALO JALINGO)

·

·

Domin neman ƙarin bayani danna nan

Kwanaki goman farko na watan
Zul Hijjah kwanaki ne masu
darajar gaske, kwanaki ne da ya
kamata musulmi su yawaita
ayyukan ibada a cikinsu: Azumi,
da Salloli, da Kabbarori, da ba wa
mabukata sadaka, da sauransu.
Imamul Bukharii ya ruwaito hadithi
na 969 cewa Annabi mai tsira da
amincin Allah ya ce: ((Babu wasu
ranaku da aikin alheri ya fi soyuwa
cikinsu a wurin Allah kamar
kwanaki goman farko na watan
Zul Hijjah. Sai Sahabbai suka ce
wa Manzon Allah: Koda yin jihadi
ne cikin tafarkin Allah? Annabi mai
tsira da amincin Allah ya ce:
Na’am, koda yin jihadi ne cikin
tafarkin Allah, amma banda
mutumin da ya fita jihadi da kansa
da kuma dukiyarsa, sannan bai
dawo da kome ba daga cikin abin
da ya fita da shi)). Intaha.
Imamul Bukharii ya ce cikin
Sahihinsa, a babin falalar aiki cikin
kwanakin Tashriq: ((Ibnu Umar, da
Abu Hurairah sun kasance suna
fita zuwa kasuwa cikin kwanakin
nan goma suna yin kabbara,
sannan mutane na yin kabbara
saboda kabbarorinsu)). Intaha.
Alhafiz Ibnu Hajar ya ce cikin
Fathul Barii 2/534: ((Abin da ke
bayyana shi ne: Su kwanaki
goman farko na Zul Hijjah sun
samo darajarsu ne ta hanyar
kasancewarsu wani irin wuri da
manyan ibadodi ke haduwa a
cikinsa, wadannan kuwa su ne:
Salla, da Azumi, da Sadaka, da
Hajji, wannan abin ba ya faruwa
cikin wasun wadannan kwanakin))
. Intaha.
Idan wani ya ce: Ai Imam Abu
Dawud ya ruwaito hadithi na 2439
da isnadi sahihi daga Nana A’isha
Allah Ya Kara mata yarda ta ce:
((Ban taba ganin Annabi mai tsira
da amincin Allah ya yi azumi koda
sau daya ba a cikin kwanaki
goman farko (na Zul Hijjah) ba)).
Intaha.
Sai a ce da shi: Maluma sun ce
wannan hadithi yana nuni ne a
kan irin yadda wani lokaci Annabi
mai tsira da amincin Allah yake
barin wani aikin lada saboda
tsoron kada a farlanta shi a kan
al’ummarsa, ba wai yana hana yin
azumi ba ne cikin wadannan
kwanaki.
BABU ASKI DA YANKAN
FARSHE DA DEBE WANI ABU
DAGA JIKI
Da zarar an ce watan Zul Hijjah ya
kama to dukkan mai niyyar yin
layya kada ya debe wani abu
daga fatar jikinsa: kada ya aske
wani abu na gashin jikinsa ko
gashin kansa, kada ya yanke wani
abu na farshensa.
Imam Muslim ya ruwaito hadithi na
1977 cewa Annabi mai tsira da
amincin Allah ya ce: ((Idan
kwanaki goman farko na watan
Zul Hijjah suka shigo, sannan
dayanku ya yi niyyar yin layya to,
kada ya taba wani abu na
gashinsa, da fatar jikinsa)). A wata
riwaya kuma ya ce: ((Ya kame
kansa daga gashinsa da
farshensa)). Intaha.
Amma wasu Maluma sun ce: yin
aski ko yanke farshe ga mai niyyar
yin layya cikin wadannan kwanaki
haramun ne, wasu kuwa suka ce
makruhi ne kawai bai kai haramci
ba, wasu kuwa suka ce halal ne a
yi hakan.
To, amma abin da muke gaya wa
yan’uwa Musulmi a nan shi ne:
Abin da sunnar Annabi take
nunawa shi ne yin hakan haramun
ne, saboda asalin lamarin Shari’ah
shi ne: duk abin da Annabi ya
hana yin shi to yin nasa haramun
ne, sai in an sami wani dalili
daban da zai iya fidda shi daga
wannan asalin, a wannan mas’alar
kuwa babu wannan dalilin.
Muna rokon Allah ya taimake mu,
Ya ba mu ikon ayyukan alheri cikin
wadannan kwanakin.

One response to “DARAJAR KWANAKI GOMAN FARKO NA WATAN ZUL HIJJAH(DR IBRAHIM JALO JALINGO)”
  1. […] DARAJAR KWANAKI GOMAN FARKO NA WATAN ZUL HIJJAH(DR IBRAHIM JALO JALINGO). […]

Leave a Reply

Latest updates
Categories