HUKUNCE-HUKUNCEN AIKIN HAJJI DA UMRA Darasi na 8(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

Danna nan domin shiga karatu Online

SIFFAR DAWAFI
Wanda yake biye damu a wannan
bayani da muka dakko ya ga siffar
yadda ake yin umra a dunkule,
amma karin bayani shine muke yin
shi sannu-sannu.
Mun yi bayanin mikati da ihirami da
sunnoninsa, da abubuwan da aka
hanawa wanda ke cikin ihirami.
Har ila yau mun ji cewa; idan
mutun ya dau ihirami zai tafi yana
talbiyyah har sai ya je Ka‘aba don
yin dawafi, kuma mun ambaci
yadda ake yin talbuyyar.
SIFFAR DAWAFI DA SUNNONIN
SA:
-Mai aikin umra zai yi idhdiba‘i
(bude kafadar shi ta dama da nada
ihiraminsa a kan ta hagu) sannan
zai dakatar da yin talbiyyah idan ya
je saitin Hajarul Aswad, sannan ya
sumbace shi ko ya taba shi da
hannunsa sai ya sumbaci hannun
sannan ya ce: Allahu Akbar, (idan
bai sami damar hakan ba sai ya
nuna shi da hannu).
-Daga nan sai ya fara dawafi cikin
sassarfa da kazar-kazar, har sai ya
yi shaudi 3 sai ya koma yana tafiya
a tsanaki. (Su kuwa mata ba a
shar‘anta musu yin sassarfa da
bude kafadarsu ba).
-An so mai dawafi ya yawaita zikiri
da salati da karatun Al-Kur‘ani mai
girma a lokacin da yake zagayawa,
ko kuma ya rika yin addu‘a ko
kuma ya hada duk wadanda suka
samu.
-An so aduk sanda ya iso kan
kusurwar da itace kusurwar
Hajarul Aswad ke biye mata, wato
Rukunul Yamani, ya sumbace shi
da hannunsa ya ce: bismillahi,
wallahu akbar‘, sannan a tsakanin
wannan kusurwar da ta Hajarul
Aswad ya karanta ‘Rabbana atina
fiddunya Hasanatan wa fil Akhirati
Hasanatan, wa kina Azaban Nar‘
-An so idan ya sami dama a duk
zagaye ya sumbaci Hajarul Aswad.
-Idan mutun ya kammala zagaye
bakwai sai ya je bayan Makamu
Ibrahim yayi sallah raka‘a biyu,
sannan ya dawo ya kara sunbatar
Hajarul Aswad ko da da hannu ne.
-Daga nan sai ya je bakin rijiyar
zam-zam ya sha har sai ya koshi.
An so mutun ya yi addu‘a ko ya
halarto da bukatunsa a cikin
zuciyar shi a lokacin shan ruwan
zam-zam.
-Daga nan sai ya tafi yayi sa‘ayi
tsakanin duwatsun Safa da Marwa
(bayanin sa‘ayi zai zo cikakke in
sha allahu).
Wanda yayi duk abubuwan da aka
yi bayani sannan yayi aski ko
saisaye, wannan ya kammala
umra.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates