BAYANI AKAN AIKIN HAJJI Darasi na 3(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

BAYANI AKAN AIKIN HAJJI
Darasi na 3
ABUBUWAN DA MANIYYACI YA
KAMATA YA FARA YI KAFIN
TAFIYA:
Kafin mutun ya himmatu zuwa ga
aikin hajji ko umra, ya zama wajibi
ya tabbatar cewa dukiyar da zai
biya ko ya tafi da ita ta halal ce.
Bayan ya tabbatar da haka sai ya
kula da wadansu abubuwa kamar
haka:
1- Kyautata niyyarsa da ikhlasi,
wato ya ji a ransa cewa zai je
wannan ibada ne don Allah, ba
don riya ko neman duniya ba.
2- Lallai ne ya nemi sanin
hukunce-hukuncen hajji, domin ba
a bautawa Allah a dace sai da ilimi.
3- Lallai ne ya nemi afuwa daga
gurin duk wanda ya san ya shiga
hakkinsa, idan ana binsa bashi, ya
biya ko kuma ya nemi lamuni akan
ya je ya dawo ko kuma a yafe
masa.
4- Idan akwai abin da yake son yin
wasiyya, ya hanzarta yin ta.
5- Lallai ne ya nemi abokan tafiya
na gari (ga masu tafiyar kasa ko ta
mota), amma idan ta jirgi ce wacce
ba shi da zabin jirgin da zai hau da
wadanda za su hau tare da shi, sai
yayi kokarin kiyaye dokokin Allah,
idan kuma an sauka a masauki
yayi kokarin hada kansa da
mutanen da yake ganin na kirki ne.
Hakan zai taimaka masa wajen yin
ibada nagartacciya, da koyan
kyawawan dabi‘u da samun ilimi.
6- Ya sani dukkan mutanen da zai
hadu da su a wajen aikin hajji ‘yan
uwansa ne Musulmi. Don haka,
kada ya nuna musu banbancin
kabila ko launi ko yare. Kuma ya
kula wajen yi musu mu‘amala mai
kyau, da tausasa musu, da yin
hakuri dasu, da yin afuwa gare su.
HUKUNCIN MACE MAI TAKABA
TA TAFI AIKIN HAJJI KO UMARA
7- Idan kuma mace tana takaba,
kar ta ce za ta bar dakinta ta tafi
hajji don ta riga ta biya kudi. Sai
dai fa idan ta tashi a jirgi ne, ko ta
yi nisa idan tafiyar kasa ce, sai
labarin mutuwar mijinta ya same
ta, sai ta ci gaba har ta kammala
aikin hajjinta ko umrarta.
Wannan shine kaulin Imamush
Sha‘fi‘i da Imam Abu Hanifa, Allah
yayi musu rahama.
Idan kuwa ba ta yi nisa ba, ko bata
tashi a jirgi ba sai ta dawo tayi abin
da Allah ya umarce ta na luzumtar
takaba.
Amma macen da aka saketa take
cikin idda, saki 1 ko 2, tana iya
tafiya idan mijinta ya yarda, idan
kuma saki 3 ne ba ta bukatar izinin
wanda ya sake. Ta, sai da izinin
waliyinta.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates