HUKUNCE-HUKUNCEN AIKIN HAJJI DA UMRA Darasi na 4(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

Danna nan domin shiga karatu Online

HUKUNCE-HUKUNCEN AIKIN
HAJJI DA UMRA
Darasi na 4
LOKACIN UMRA
Ana iya yin umra a kowane wata
daga cikin watanni, ba a iyakan ce
wani wata ba saidai ta fi falala a
cikin watan Ramadhan. Kuma ana
iya yin umra a kammalata a
kowace sa‘a, ta safe ko ta rana, ko
ta dare.
FALALAR YIN UMRA A WATAN
RAMADHAN:
Yin umra a Ramadhan yafi
ragowar watanni domin ana baiwa
mutun ladan hajji, sai dai koda
mutun ya yi umra a Ramadhan
wajabcin hajji yana nan a kansa
har sai ya sauke shi.
LOKACIN HAJJI
Hajji yana da watanni kebantattu,
watanninsa su ne:
-Shauwal
-Zul Ka‘adah
-Zul Hijja
Kuma aiyuka da dama na hajji an
kebance musu sa‘ar da za a
aiwatar da su a cikinta.
NAU‘IKAN HAJJI
Hajji nau‘i uku ne;
1. Tamattu‘i
2. Kira‘ni
3. Ifradi
Kowacce mutun yayi kamar yadda
aka umarce shi, tayi, kuma nauyin
hajji ya fadi daga kansa.
TAMATTU‘I:
Shine yin umra a cikin wani wata
daga cikin watannin hajji, ko dai a
Shauwal, ko a Zul Ka‘adah ko a
farkon Zul Hijja, daga nan sai
mahajjaci ya cire ihiraminsa, ya ci
gaba da mu‘amala ta yau da gobe.
Har sai ranar takwas (8) ga Zul
Hijjah sai ya mayar da ihirami yayi
harama da hajji.
KIRA‘NI:
Shine yim umra a wani wata daga
watannin hajji, amma alhaji ba zai
cire ihiraminsa ba, zai ci gaba da
zama a cikinsa, kuma duk abinda
aka haramtawa me hajji haram ne
a kansa, har sai ranar takwas (8)
ga Zul Hijjah sai ya dora da
aiyukan hajji na wadannan
kwanaki kebantattu.
IFRADI:
Shine yin aikin hajji kadai, ba tare
da umra ba.
Bayani mai gamsarwa akan
kowanne zai zo insha Allahu nan
gaba.
MUHIMMAN GURARE DA SUKE
DA ALAKA DA HAJJI
-Mikati; Su ne guraren da aka
aiyana don yin harama da umra ko
hajji. Duk ta bangaren da Alhaji ya
bullo sai ya yi harama a mikatinsu.
– Makkah; A cikinta ne Ka‘aba take
da Safa da Marwa, da rijiyar
Zamzam.
-Mina; Itace gurin yin yanka, kuma
a cikinta ne wasu guraren jifan
shaidan suke.
-Arafah: Nan ne gurinda ake
tsayuwar arafah.
-Muzdalifah: Nan ne ake tahowa a
kwana bayan an baro Arafah. Itace
‘Maukif’ kuma itace ce ‘Mash‘arul
Haram’.
GURARE MASU GIRMA DA AKE
ZIYARTA
-Madina; A nan ne masallacin
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama yake, kabarinsa kuma
yana kewaye a ciki.
-masallacin Kuba; shine masallacin
da aka gina shi akan takwa, kuma
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
ala aalihi wa sallama ya kasance
yana ziyartarsa.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

One response to “HUKUNCE-HUKUNCEN AIKIN HAJJI DA UMRA Darasi na 4(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)”
  1. Bello Muhammad Ahmad Avatar
    Bello Muhammad Ahmad

    Salam malam ina son bayanin akan abubuwan da aiwatar a Umrah

Leave a Reply

Categories
Latest updates