HUKUNCE-HUKUNCEN AIKIN HAJJI DA UMRA Darasi na 5(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

·

·

Domin neman ƙarin bayani danna nan

HUKUNCE-HUKUNCEN AIKIN
HAJJI DA UMRA
Darasi na 5
BAYANI AKAN MIKATI:
Ga duk wanda zai yi aikin hajji ko
umra zai fara ne daga mukati, wato
gurare 5 wadanda Manzon Allah
sallallahu alaihi wasallama ya
aiyana ga masu zuwa aikin hajji da
umra don yin harama daga gurin
su kafin su karasa Makka.
Wadannan gurare duk suna
kewayen Makka ne domin su mai
aikin hajji ko umra zai fara tararwa
akan hanyarsa ta shiga Makka
daga garuruwa da za a ambata a
kasa.
Wadanda kuma mawakit suka
kewaye kamar mutanen da ke cikin
Makkah, ba za su fito zuwa mikati
don yin harama ba, za suyi
haramarsu ne daga gidajensu.
Wanda kuma yazo daga wani
garin, ba wadanda aka aiyana ba,
zai dau harama daga inda bai
ketare mikatin da ya bullo ta
jihharsa ba.
Hadisi ya tabbata daga Abdullahi
Bin Abbas radhiyallahu anhu ya
ce:
ﺇﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻭﻗﺖ ﻷﻫﻞ ﺍﻟﻤﺪﻳﻨﺔ
ﺫﺍ ﺍﻟﺤﻠﻴﻔﺔ, ﻭﻷﻫﻞ ﺍﻟﺸﺎﻡ ﺍﻟﺠﺤﻔﺔ, ﻭﻷﻫﻞ ﻧﺠﺪ ﻗﺮﻥ
ﺍﻟﻤﻨﺎﺯﻝ, ﻭﻷﻫﻞ ﺍﻟﻴﻤﻦ ﻳﻠﻤﻠﻢ, ﻭﻗﺎﻝ: ﻫﻦ ﻟﻬﻦ ﻭﻟﻤﻦ
ﺃﺗﻰ ﻋﻠﻴﻬﻦ ﻣﻦ ﻏﻴﺮﻫﻦ ﻣﻤﻦ ﺃﺭﺍﺩ ﺍﻟﺤﺞ ﻭﺍﻟﻌﻤﺮﺓ,
ﻭﻣﻦ ﻛﺎﻥ ﺩﻭﻥ ﺫﻟﻚ ﻓﻤﻦ ﺣﻴﺚ ﺃﻧﺸﺄ, ﺣﺘﻰ ﺃﻫﻞ ﻣﻜﺔ
ﻣﻦ ﻣﻜﺔ
Ma‘ana:
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
salama ya aiyana wajen harama;
Zul Hulaifa ga mutanen Madina,
Juhfa ga mutanen Sham,
Karnul Manazil ga mutanen Najad,
Yalamlam ga mutanen Yaman,
kuma ya ce: wadannan gurare
nasu ne, su da wadanda suka biyo
ta bangarensu, masu nufin hajji ko
umra.
Wanda kuwa mahallin da yake bai
fita daga cikin da‘irarsu ba, to, zai
dau haramarsa ne daga inda ya
taso, hatta mutanen Makka za suyi
haramarsu ne daga Makka.
Wani hadisin kuma ya tabbata
daga Nana A‘isah radhiyallahu
anha ta ce:
ﺃﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻭﻗﺖ ﻷﻫﻞ ﺍﻟﻌﺮﺍﻕ
ﺫﺍﺕ ﻋﺮﻕ
Ma‘ana:
Hakika Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama ya aiyana Zatu
Irkin ga mutanen Iraki.
MAHALLIN KOWANE MIKATI
1- ZUL HULAIFA:
Ga wanda ya baro Madina, ko
nahiyarta ta arewa, yana kilomita
410 kafin aje Makka. Akwai
masallaci a gurin ana kiransa
Masjidu Zil Hulaifa, ko Masjidul
Mikat, ko Masjidus Shajara.
2- JUHFA:
Ga wanda ya baro Sham ko
nahiyarta ta kudu-maso-yamma,
yana kilomita 187 kafin zuwa
Ka‘aba.
3- KARNUL MANAZIL:
Ga wanda ya baro Najad ko
nahiyar gabas kamar Riyadh, Da‘if
da sauransu, akwai manyan
hanyoyi 2 da suka gitta shi zuwa
Makka, a kan kowace hanya akwai
masallaci:
-Masjidu Sailil Kabir; kilomita 80
kafin zuwa Ka‘aba.
-Masjidu Wadi Muhrim; kilomita 76
kafin zuwa Ka‘aba.
4-YALAMLAM:
Ga wanda ya baro Yaman ko
nahiyarta ta kudu, yana kilomita
100 kafin zuwa Makka.
5- ZATU IRKIN:
Ga wanda ya baro Iraki, yana
kilomita 90 kafin zuwa Ka‘aba.

Leave a Reply

Latest updates
Categories