HUKUNCE HUKUNCEN AIKIN HAJJI DA UMRA Darasi na 7(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

HUKUNCE HUKUNCEN AIKIN
HAJJI DA UMRA
Darasi na 7
ABUBUWAN DA AKA HANA ME
IHIRAMI
Dukkanin wanda ke cikin ihirami na
aikin hajji ko na umra zai kiyaye
abubuwa kamar haka:
1- Tarawa da iyali.
2- Yin aure ko neman aure ko
aurawa wani.
3- Yin farautar dabbar dake rayuwa
a tudu (bayan kasa) ko taimakawa
ayi farautarta, amma yana iya
farautar dabbar da rayuwarta a
cikin ruwa take, kamar kifi da
sauransu.
4- Sanya tufafi da aka dinka kamar
riga, wando, hula, safa d.s
(wannan ya shafi maza ne kadai,
idan kuwa mutun bai sami hirami
ba, babu laifi ya sanya wando).
5- Rufe kai da rawani ko mayafi
d.s. Shima wannan ya shafi maza
ne, (amma suna iya shiga
karkashin wani abu da ke yin
inuwa ko tare ruwan sama kamar
mota me rufi, daki me rufi, rumfa
d.s).
6- Ita kuma mace za ta sanya
kowane irin tufafi da ya rufe mata
jikinta muddin baya nuna ado,
amma ba za ta sanya nikabi ko
safar hannu ko ta kafa ba, saifa
idan tana cikin maza ajnabai kuma
tana tsoron fitina.
7- Babu aski ko cire gashi ta
kowace irin hanya, kuma gashi ko
a ina yake; gashin kai ko na gaba
ko na hamata d.s.
8- Babu yanke farce ko karye shi.
9- Babu sanya turare a jiki ko a
tufafi.
10- Babu sanya takalmi sau ciki,
koda mai ihirami bashi da sandal
ko silifas sai ya yanke dunduniyar
wanda yake dunduniya ciki ya
sanya.
Har ila yau ba a son cin abin da zai
sanya warin baki kamar tafarnuwa
ko shan taba d.s da kuma yin
maganganun batsa.
Wadannan hane-hane su suka
sanya ake son mai niyyar fara aikin
hajji ko umra ya aske gashin
gabansa da na hamata, ya yanke
farce ya sanya turare a jikinsa
(amma banda a jikin ihiraminsa)
tun kafin yayi harama.
Mutumin da yayi ihirami sai ya
kiyayi abubuwan da aka fada,
kuma sai ya tafi yana talbiyyah har
sai ya je Ka‘aba don yin dawafi.
Alhazai da idan sun dau harama
daga mikati za su biya ta masauki
don ajiye kayaiyaki sai su yawaita
yin wannan talbiyyar da aka
ambata.
LAFAZIN TALBIYYAH SHINE:
ﻟﺒﻴﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻟﺒﻴﻚ
ﻟﺒﻴﻚ ﻻ ﺷﺮﻳﻚ ﻟﻚ ﻟﺒﻴﻚ
ﺇﻥ ﺍﻟﺤﻤﺪ, ﻭﺍﻟﻨﻌﻤﺔ
ﻟﻚ ﻭﺍﻟﻤﻠﻚ
ﻻ ﺷﺮﻳﻚ ﻟﻚ
Idan mutun ya je yayi dawafi sai
yayi sa‘ayi sannan aski, za mu
kawo siffar kowannensu daki-daki
in Allah ya yarda.
Daga nan ya kammala umra.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates