FATAWOYIN LAYYA2(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

Danna nan domin shiga karatu Online

A wannan darasi za mu amsa
tambayoyi kamar haka;
*Tambaya:
Mene ne sharuddan layya?
AMSA:
Yana daga cikin sharuddan layya:
abin da za a yanka, lallai ya
kasance daga cikin “bahimatul
anʿām” (dabbobin ni’ima), irin su:
rakuma da shanu da awaki da
tumaki). Domin haka, ba ya cikin
sharuddan layya, a yi ta da namun
daji, kuma ba za a yanka kaji da
sauran tsuntsaye ba, kamar yadda
wasu daga cikin ‘yan Zahiriyyah
suka tafi a kai. Dalili kuwa fadin
Ubangiji subhanahu wa ta’ala
cewa:
ﻭﻟﻜﻞ ﺃﻣﺔ ﺟﻌﻠﻨﺎ ﻣﻨﺴﻜﺎ ﻟﻴﺬﻛﺮﻭﺍ ﺍﺳﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﻣﺎ
ﺭﺯﻗﻬﻢ ﻣﻦ ﺑﻬﻴﻤﺔ ﺍﻟﺄﻧﻌﺎﻡ (34) … ﺍﻟﺤﺞ: ٣٤
Ma’ana:
Kowacce al’umma mun sanya
musu ibadunsu, domin su ambaci
sunan Allah a bisa abin da (Allah)
ya arzuta su da shi daga cikin
dabbobin ni’ima…
Wannan aya ta nuna cewa,
Ubangiji subhanahu wa ta’ala ya
ambaci dabbobin ni’ima ne, kuma
ya nuna cewa lallai ne idan za a
yanka su, a ambaci sunansa.
Amma ayar ba ta ambaci cewa ana
iya layya da namun daji ba, ko
tsuntsaye, kamar kaji da sauransu.
Kuma koda a cikin dabbobin ni’ima
din ba a yankawa sai wacce ta cika
wadannan sharuddan:
1- Shanu: Sai sun cika shekara
biyu zuwa sama.
2-Raquma: Sai sun cika shekara
biyar zuwa sama.
3-Tumaki da Awaki: Sai sun cika
shekara daya zuwa sama. Sai dai
idan ya ta’azzara ba a samu
shekararriya ba, to babu laifi a
yanka wacce ba ta shekara ba
amma ta kusa cika shekara a cikin
raguna ko awaki (watau jaz’a),
saboda hadisin da aka karbo daga
Jabir Ibn Abdullah radhiyallahu
anhuma ya ce: Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama ya ce:
ﻟﺎ ﺗﺬﺑﺤﻮﺍ ﺇﻟﺎ ﻣﺴﻨﺔ ﺇﻟﺎ ﺃﻥ ﻳﻌﺴﺮ ﻋﻠﻴﻜﻢ ﻓﺘﺬﺑﺤﻮﺍ
ﺟﺬﻋﺔ ﻣﻦ ﺍﻟﻀﺄﻥ.
Ma’ana:
Kada ku yanka sai shekararriya,
sai dai idan ya gagareku , sai ku
yanka wacce ake kira jaz’a daga
raguna.
Haka kuma, ana so dabbar da za a
yi layya da ita ta kasance
kubutacciya daga aibu. Saboda
hadisin da aka karbo daga Bara’u
Ibn Azib radhiyallahu anhuma ya
ce: Manzon Allah sallallahu alaihi
wa sallama ya ce:
ﻻ ﻳﻀﺤﻰ ﺑﺎﻟﻌﺮﺟﺎﺀ ﺑﻴﻦ ﻇﻠﻌﻬﺎ ﻭﻻ ﺑﺎﻟﻌﻮﺭﺍﺀ ﺑﻴﻦ
ﻋﻮﺭﻫﺎ ﻭﻻ ﺑﺎﻟﻤﺮﻳﻀﺔ ﺑﻴﻦ ﻣﺮﺿﻬﺎ ﻭﻻ ﺑﺎﻟﻌﺠﻔﺎﺀ
ﺍﻟﺘﻲ ﻻ ﺗﻨﻘﻲ
Ma’ana:
Ba a yanka ramammiya wacce
ramarta ta bayyana, ko gurguwa
wacce gurguntakarta ta bayyana,
ko mara lafiyar da rashin lafiyarta
ta bayyana, Ko me ido daya.
Banda wadannan siffofi na
dabbobi, akwai wasu siffofin. saidai
hadisan ba su inganta ba, don
haka ba mu kawo su a nan ba.
Kuma lallai ne abinda za a yanka
na layya, ya kasance mallakarsa
aka yi ta hanyar halal, ba ta hanyar
haram ba. Wato wajibi ne ya
kasance ba na sata ko kwace ba
ne, kuma ba dabbar da aka bayar
jingina ko amana ba ce.
Kuma ya kamata mai yin layya ya
sani cewa ba cewa aka yi ya yi
azumi ko rikon baki ba. Domin
haka, ba a hana shi ci ko shan abin
sha ba matukar yana bukata.
*Tambaya:
Yaushe ya kamata a yanka abin
layya?
AMSA:
Jumhurun malamai sun tafi a kan
cewa, ana yanka abin layya ne,
bayan sallar idi ko da liman bai
yanka ba. Dalilinsu kuwa shi ne
fadin Manzon Allah sallallahu alaihi
wa sallama cewa:
ﻣﻦ ﻛﺎﻥ ﺫﺑﺢ ﺃﺿﺤﻴﺘﻪ ﻗﺒﻞ ﺃﻥ ﻳﺼﻠﻲ ﺃﻭ ﻧﺼﻠﻲ
ﻓﻠﻴﺬﺑﺢ ﻣﻜﺎﻧﻬﺎ ﺃﺧﺮﻯ ﻭﻣﻦ ﻛﺎﻥ ﻟﻢ ﻳﺬﺑﺢ ﻓﻠﻴﺬﺑﺢ
ﺑﺎﺳﻢ ﺍﻟﻠﻪ .
Ma’ana:
Wanda ya yanka abin layyarsa
kafin sallarmu, to, ya sake yanka
wata dabbar maimakonta bayan
sallar idi, wanda kuma bai yanka
ba (sai bayan sallarmu), to, ya
yanka da sunan Allah.
Saidai kuma Imam Mālik ya tafi a
kan sabanin abinda jamhur suka
tafi akai inda ya ke cewa:
Ba a yanka abin layya sai bayan
liman ya yanka nasa.
Dalilinsa kuwa shi ne, hadisin da
aka karbo daga Jabir Ibn Abdullah
radhiyallahu anhu ya ce,
ﺻﻠﻰ ﺑﻨﺎ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻨﺤﺮ
ﺑﺎﻟﻤﺪﻳﻨﺔ ﻓﺘﻘﺪﻡ ﺭﺟﺎﻝ ﻓﻨﺤﺮﻭﺍ ﻭﻇﻨﻮﺍ ﺃﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ
ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻗﺪ ﻧﺤﺮ ﻓﺄﻣﺮ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ
ﻭﺳﻠﻢ ﻣﻦ ﻛﺎﻥ ﻧﺤﺮ ﻗﺒﻠﻪ ﺃﻥ ﻳﻌﻴﺪ ﺑﻨﺤﺮ ﺁﺧﺮ ﻭﻟﺎ
ﻳﻨﺤﺮﻭﺍ ﺣﺘﻰ ﻳﻨﺤﺮ ﺍﻟﻨﺒﻲ. ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
Ma’ana:
Mun yi salla tare da Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama a
Madina ranar babbar salla, sai
wasu mazaje suka je suka yi
yanka, suna tsammani Manzon
Allah sallallahu alaihi wa sallama
ya yi yanka, sai Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama ya ce:
duk wanda ya yi yanka kafin na yi,
to ya sake yankansa. Ya kara da
cewa: Kada su yanka har sai
Annabi sallallahu alaihi wa sallama
ya yanka.
Wannan shi ne zance mafi rinjaye
domin wannan hadisin da Imam
Malik ya kafa hujja da shi ya fada
karara cewar ba’a yanka sai bayan
liman yayi yankan sa, sabanin
dalilin jamhur. Don haka sai
mutum ya hakura har liman ya
yanka. Idan kuma mutum yana
nesa da gari ne, sai ya kintaci
lokacin da ya kamata a ce liman ya
yanka dabbar layyarsa, sai ya
yanka tasa. Wanda kuma ya yanka
kafin salla, to namansa ba na layya
ba ne, ya zama naman miya
kenan, ko ya sani ko bai sani ba.
Saboda haka sai ya sake yanka
wata maimakonta.
Dalili kuwa shi ne: wani sahabi
Uwaīmir Ibn Ashkar radhiyallahu
anhum ya taba yanka dabbar
layyarsa kafin sallar īdī, sai
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama ya ce:
ﺃﻋﺪ ﺃﺿﺤﻴﺘﻚ .
Ma’ana:
Ka sake yanka wata a
maimakonta.
A nan Annabi sallallahu alaihi wa
sallam bai tambaye shi ko ya sani,
ko bai sani ba. Wallahu a’alam!
*Tambaya:
A ina ya kamata liman ya yanka
abin layyarsa a sunnance?
AMSA:
A bisa koyarwa irin ta Manzon
Allah sallallahu alaihi wa sallama
liman zai yanka abin layyarsa ne a
filin idi, domin al’umma su shaida,
kuma su sami damar yin ta su
layyar, ba tare da wani kokwanto
ba. Dalili kuwa shi ne hadisin Jabir
radhiyallahu anhum ya ce:
ﺷﻬﺪﺕ ﻣﻊ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
ﺍﻷﺿﺤﻰ ﺑﺎﻟﻤﺼﻠﻰ ﻓﻠﻤﺎ ﻗﻀﻰ ﺧﻄﺒﺘﻪ ﻧﺰﻝ ﻣﻦ
ﻣﻨﺒﺮﻩ ﻭﺃﺗﻲ ﺑﻜﺒﺶ ﻓﺬﺑﺤﻪ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺑﻴﺪﻩ.
Ma’ana:
Na halarci idin babbar salla tare da
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama. Bayan ya gama
hudubarsa, sai ya sauka daga kan
minbarinsa, aka kawo masa ragon
layyarsa, sai ya yanka shi da
hannunsa (mai albarka).
Haka kuma an karbo wani hadisin
daga Abdullahi Ibn Umar
radhiyallahu anhum ya ce:
ﺃﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻛﺎﻥ ﻳﺬﺑﺢ ﺃﺿﺤﻴﺘﻪ
ﺑﺎﻟﻤﺼﻠﻰ ﻭﻛﺎﻥ ﺍﺑﻦ ﻋﻤﺮ ﻳﻔﻌﻠﻪ.
Ma’ana:
Hakika Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama ya kasance yana
yanka abin layyarsa a filin idi.
Saboda haka ni ma na kasance ina
aikata hakan.
Don haka sai limamai su yi koyi.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates