Hukuncin yanka Layya kafin Limami

Tambaya: Shin Ya Halatta Mutum ya yanka layyansa kafin Limami ya yanka tasa?

Amsa: Imamu Malik Allah yayi masa Rahama ya tafi kan cewa baya halatta mutum yayi yanka kafin limaminsa, dole sai ya jira limaminsa yayi kafin shima yayi. dalilin Hadisi da aka rawaito daga Jabir Allah ya kara masa yarda yace:

Annabi Sallallahu Alaihi Wa Sallama yayi Mana Sallah ranar Idi babba a Madina, sai wasu daga cikin mutane sukayi zato Annabi ya riga yayi yanka suma sai sukayi. sai Annabi Sallallahu Alaihi Wa Sallama ya umarci duk wanda yayi yanka kafin yayi da ya sake yanka, sannan kada wani yayi yanka har sai Annabi yayi.

Sahihu Muslim: 1964

Da wannan Hadisi Imamu Malik ya yanke hukunci cewa dole sai limami yayi yanka kafin sauran mutane suyi.

Amma Imamu Ahmad da wasu Maluman sun tafi kan cewa ba Sharadi bane sai limami yayi yanka kafin sauran mutane suyi, da zarar anyi Sallah toh shikenan kowa zai iya yin yankansa.

Wannan Hadisi da Imamu Malik yayi hujja dashi za’a dauke shi a matsayin tsawatar wa ne kada mutum yayi gaggawa wurin yin layya kafin lokacinsa. ma’ana kafin Sallah.

Domin a Zamanin Annabi Shine Jagora baki daya, babu wanda yake yin Sallah kafin shi, amma a wannan zamani namu akwai masallatai da yawa, kuma lokutan sallan su tana bambamta, sabida haka koda mutum bai samu zuwa masallaci ba sai ya kaddara lokacin Sallan, daga lokacin da yaga cewa yanzu an kammala Sallah to zai iya yanka layyansa ba tare da jiran wani ba.

Abinda wannan Amsa ta kunsa

Ba sharadi bane dole sai anjira Limami kafin a yanka layya, ya halatta a yanka da zarar an kammala Sallah ko lokacin Sallah ya wuce sabida Hadisi da aka Rawaito daga Annabi Sallallahu Alaihi Wa Sallam

Duk wanda yayi yanka kafin yayi Sallah To ya sake yanka wata, wanda bai yanka ba har muka yi Sallah to ya yanka da Sunan Allah

Sahih muslim: 1960

Allah shine mafi sani. Allah yasa mudace

Click Here to Support our work

Leave a Reply

%d bloggers like this: