Shin Mace zata iya yanka layyan ta da kanta

Fatawa

Tambaya: Shin mace zata iya yanka Layyanta ko na wani?

Amsa: Mace zata iya yanka Layyanta da kanta, ko ta yanka wa wani babu laifi yin hakan. Babu tsaɓani tsaƙanin Mazhabobin nan guda huɗu kan halaccin Haka.

Sannan An rawaito wata Baiwa ta Ka’ab Bin Malik tana kiwon Tumakai sai Wata Akuya ciwo ya kama ta sai ta yanka sai ya tambayi Annabi Sallallahu alaihi Wasallama shin za’aci? sai yace masa: Kuci.

Sahihul Bukhari 5505

Wannan yake nuna cewa ana cin yankan mace tunda Annabi yayi umarni da aci yankan wannan Baiwa.

Click Here to Support our work

Leave a Reply

%d bloggers like this: