Hukuncin Kara Suman kayi

Domin neman ƙarin bayani danna nan

Fatawa

Tambaya: Menene Hukuncin ƙara Suman kai?

Amsa: Ƙara Suma Haramun ne ga Mace ko namiji. Wannan ƙarin da akayi anyi shi ne da wani suma na daban ko kuma anyi shi ne da zare mai kama da suma. Duka wannan bai halatta ba.

Dalili:

Abdullahi Bin Umar ya rawaito Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya tsine wa mai ƙara suma, da wacce take nema a ƙara mata

Sahihul Bukhari: 5947

Abu Huraira ya rawaito daga Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yace: Allah ya tsine wa mai ƙara suma, da wacce ta ke nema a ƙara mata

Sahihul Bukhari: 5933

Asma Binti Abi Bakr ta Rawaito cewa: Wata mata tazo wurin Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi tace masa Ya Manzon Allah ” ina da wata ɗiya wacce na aurar da ita, gashi ciwo ya same ta wanda ya janyo Suman kanta ya zuba shin zan iya ƙara mata suma?” Sai Annabi Tsira da Amincin Allah Su tabbata a gare shi yace: “Allah ya tsine wa mai ƙara suma, da wacce take nema a ƙara mata”

Bukhari: 5941 Muslim: 2122

Wa’innan Hadisai suke nuna cewa baya halatta mace ko namiji ya ƙara Suman kansa, koda ko Rashin Lafiya ne ya sanya suman ya zuba, kamar yadda wannan Hadisi na ƙarshe ya nuna.

Shin ya halatta mace ta ƙara suman idan Mijin ta ne ya umarce ta?

Baya Halatta mace ta ƙara sumar ta koda ko mijin ta ne ya umarce ta. Domin ba’a yi wa Wani biyayya wurin tsaɓa wa Allah. Duk wanda ya bada umarni da ta tsaɓa wa Allah to za’ayi watsi da Umarnin sa ayi amfani da ta Allah da Manzonsa.

Shin ya halatta a ƙara suma ga yara ƙanana?

Baya halatta, duk Hukuncin su ɗaya da na manya.

Allah Shine mafi sani. Allah yasa mudace.

Leave a Reply

Latest updates
Categories