Tarihin Annabi Sallallahu alaihi Wasallama Fitowa ta 8: Hukuncin Annabi kan dora Hajarul Aswad a mazauninsa

Shekara kafin hijira: 18

Shekarar Miladiyya: 605


An samu tsaɓani tsaƙanin ƙabilu a lokacin sake gina ɗakin ƙa’abah kan wanene zai ɗaura Baƙin dutse(Hajarul Aswad) a mazauninsa! Ƙabilar Quraish wacce itace annabi ya fito daga cikinta suka nemi cewa su zasu ɗaura wannan dutse a mazauninsa, wasu daga cikin ƙabilu suma suka ce sune zasu ɗaura.

Ansamu wannan tsaɓani ne sabida matsayin da wannan dutse ke da shi.

Bayan da suka sami wannnan saɓani sai suka nemi da a sami wanda zai musu hukunci. Sai suka amince kan cewa duk wanda ya fara fito wa ta wannan ƙofa toh shine zaiyi hukunci tsaƙaninsu kan wanene zai ɗaura wannan dutse a mazauninsa.

Ana haka sai ga Manzon Allah ya fito daga wannan ƙofa, bayan sun ganshi sai suka ce ga amintacce yazo muku. Sai suka bashi labarin abinda ke wakana. Sai Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yayi amfani da hikima wurin raba wannan gardama ta yadda ya baiwa kowace ƙabila damar saka hannu wurin ɗaura wannan dutse.

Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya ɗauki wannan dutse ya sanya ta kan tufafinsa sai ya umarci shuwagabannin ƙabilun da kowanne ya kama gefen tufar domin ɗaga dutsen zuwa mazaunina, bayan sun ɗaga sun kaishi zuwa ga wurin da za’a saka shi sai shi Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya ɗauki dutsen da hannunsa mai Albarka ya sanya shi a mazauninsa.

Kaga anan babu wanda zaice shine ya ɗaura dutsen shi kaɗai.

Click Here to Support our work

Leave a Reply

%d bloggers like this: