Azumin sitta shawwal ga wanda ake bi azumin Ramadan

·

·

Domin neman ƙarin bayani danna nan

Sananne ne cewa Azumin sitta shawwal yana da falala mai girman gaske, anaso Musulmi ya azumce shi in yana da dama, Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya nuna cewa Azumtar Watan Ramadan sannan Azumi shida acikin watan shawwal bayan Ramadan yana daidai da Azumin shekara ne. Toh haƙiƙa wannan falala ce babba wanda bai dace Musulmi yayi wasa dashi ba. Toh shin Mutum zai iya yin wannan azumi koda ko ana binsa bashin azumin watan Ramadan?

An samu tsaɓani tsakanin Maluma kan halaccin hakan, wasu suna ga cewa dole sai mutum ya kammala ramakon Azumin watan Ramadan da ake binsa kafin ya fara wannan azumi shida na Shawwal, suka nuna cewa Annabi cewa yayi:

Wanda ya Azumci Ramadan sannan ya biye bayansa da Azumi shida toh kamar yayi azumin shekara ne

Muslim 1164

Da wannan ne suke ga cewa ai wanda bai yi azumin Ramadan cikakke ba ba zai sami wannan lada da Annabi yayi bayani akai ba,

Magana ta biyu kuma wacce itace tafi inganci shine Mutum zai iya Azumtar Sitta shawwal sannan daga baya yazo ya rama azumin da ake binsa na Ramadan, sabida shi lokacin ramako baya taƙaita a cikin wata ɗaya, lokacinsa yana da faɗi, amma lokacin Azumin sitta shawwal kuma lokacin sa babu faɗi, domin da zarar watan ya fice shikenan. Kuma duk wanda ya sha azumin watan Ramadan sabida wani Uzuri wanda Shari’a ta yarda da shi toh kamar wanda yayi Azumi ne. Wannan yake nuna cewa zai iya yin azuminsa na sitta shawwal sannan sai daga baya yazo ya rama Azumi da ake binsa na Ramadan, sai dai kuma idan mutum ya samu daman Ramako kafin ya fara Sitta Shawwal to hakan shi yafi. Allah yasa mudace.

Leave a Reply

Latest updates
Categories