FATAWAR MANYAN MALAMAN DUNIYA KAN WANTA BAI YI NIYYAR AZUMIN RAMADHAN BA SAI DA SAFE(Dr. Isa Ali Pantami)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Akwai fatawoyi guda biyu na
Malamai ga Wanda ya kwanta babu
labarin GANIN wata, kuma sai da
gari ya waye ya Samu labarin
GANIN Watan.
1) Suna GANIN bai da Azumi, sai
ya Rama, saboda Hadith da ke
cewa: “Babu Azumi ga Wanda bai
YI Azumi ba gabannin Alfijir”
2) Wanda kuma itace mafi inganci
ga Malamai irin Shaykh
Nasiruddeen Albaniy, Shaykh
Saleem bn Idd Alhilaliy, da Aliyu
Hassan Ali AbdulHameed cewa
wannan Azumi yayi ko da safe
mutum yayi NIYYAR. Sun kafa
hujja da cewa
A) Hadithin da masu cewa Azumi
bai YI ba, yana magana Akan
Wanda ya bar NIYYAR da ganganci,
ba Wanda ya bari a rashin sani ba.
Wannan shine Maganar Abuddarda,
Abu-Dalha, Abu Huraira, Bn Abbas,
Huzaifa. Duba Taaliqut-Taaliq.
B) Cewa Hukuncin farilla baya
canjawa, kuma a farkon Musulunci
lokacin da aka farlanta Azumin
Ashura, akwai Sahabbai da sun YI
breakfast da sabe. Amma Manzon
Allah, sai ya ce suyi Azuminsu,
kuma bai ce su Rama ba bayan
RAMADHAN. (Duba Bukhari 3/212,
Muslim 1125).
C) Masu cewa a “Kama baki” sai
bayan Ramadhan tukunna mutum
ya Rama, to gaskiya babu wata
Ibadah Mai suna Kama baki a
Musulunci. Kuma babu Nassi Akan
Kamun baki.
Don haka abunda yafi karfin hujja,
itace Fatwa ta biyu. Idan Baka da
labarin GANIN Wata sai da safe.
Sai kaci GABA da Azumi ko da
bayan breakfast ne, kuma Azumi
yayi in sha Allah. Wallahu A’alam.
Allah ya sa mu dace

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

2 responses to “FATAWAR MANYAN MALAMAN DUNIYA KAN WANTA BAI YI NIYYAR AZUMIN RAMADHAN BA SAI DA SAFE(Dr. Isa Ali Pantami)”
  1. ALLAH YASAKA DA ALKHAIRI
    nima na zabi fatawa ta 2 dan tafi sauki dan musulunci sauki ne dashi ba wahala b ALLAH YA MUDACE

  2. Ibrahim aliyu Avatar

    Allah ya saka maku da alkhairi

Leave a Reply

Latest updates
Categories