Mas'alolin Azumi(2) meye hukuncin wanda yaci abinci bayan anyi kiran sallah ta biyu abisa rashin sani? wasu abubuwa ne annabi yake bude baki dasu?

Danna nan domin shiga karatu Online

1)Wace abinci ce tafi falala mutum ya Bude baki dashi?
Amsa=anfison Mutum ya bude bakinsa da ‘ya’yan itace masu ruwa, inbai samu ba sai dabino, inbai samu ba sai yasha ruwa, dalilin haka kuwa shine hadisin Aisha(radiyallahu anha) tace ‘Manzon Allah ya kasance yana bude baki da ‘ya’yan itace masu ruwa, inbai samu ba sai yayi amfani da dabinai, idan bai samu ba, sai yayi amfani da ruwa iya gwargwado, idan ruwan bata isan masa ba sai yayi amfani da kowai irin abinci halal idan kuma bai samu komai ba sai yayi niyyan bude baki kawai.
2)Nine Naci abinci ina mai zaton cewa alfijir bata keto ba, bayan na kammala sai naji ana tada sallan alfijir, shin dole sai na rama wannan azumi?
Amsa= a wannan mas’ala akwai tsabani acikinta, malaman fiqhu ta hanabila suna cewa: idan mutum yaci abinci yana zaton dare ne, kuma ashe alfijir ta keto toh dole sai ya rama.
Amma wasu maluma suna ga cewa ba sai ya rama ba, Kaman sheikhul islam ibn taimiyyah, suna cewa babu wata ramako akansa domin yaci abincin ne abisa tabbacin cewa lokacin cin abinci halal ne, bada gangan yayi ba, kaga anan za’a iya masa uzuri fiye da mai mantuwa.
Sai dai sun gargadi mai azumi cewa ya rinka kula sosai da azuminsa, kuma bazai rama azumin bane inhar abincin da yacin ba yaci bane kan koshi da yayi, inhar yaci abincin ne kan koshi da yayi tun kafin ketowan alfijir toh zai rama azumin… Wallahu A’alam..
A saurari ta uku. Wassalaam.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

4 responses to “Mas'alolin Azumi(2) meye hukuncin wanda yaci abinci bayan anyi kiran sallah ta biyu abisa rashin sani? wasu abubuwa ne annabi yake bude baki dasu?”
 1. alameenmaster Avatar

  yayi ganganci

 2. Marwan B. Kabir Avatar

  Salam Ya sheikh Mutun Yasha Azumi Da Gangar Ya Makomansa A Musulunci Allah Ya Timaki Sheikh Inajiran Amsa

 3. Umar adam Avatar
  Umar adam

  Aslam malam idan mutum ya gama cin abinci kuma alokacin an kira assalatu yaya axumin yake

 4. assalamu alaiku malama muna mika godiya ga irin tina tarwa da kakaimana allah ya bamu ikun amfani dashi amem .
  allah gafarta malam miye hukuncin iyayinda sukacewa yarinya taje ta neme miji da kanta kuma ta nema amma suka hanata arensa kuma yarinyar tayi tsaye saishi kuma yaron shima yana sunta sosai. Inajiran amsa malam. Wslm

Leave a Reply

Categories
Latest updates