Yadda ake wankan janaba

Maqala

Siffar wankan janaba ya rabu kashi biyu:

Na farko: wanka wanda yake wadatarwa; duk wanda yayi wannan wankan to ya wadatar dashi. Shine Mutum ya ƙudurce Niyyar wankan Janaba, sai ya wanke jikinsa baki ɗaya. Ko ya tsaya a ƙarƙashin shower ya wanke jikin sa. Wannan ya wadatar dashi. Idan Mutum yayi haka to ya tsarƙaƙa. Wasu Maluman kuma sunaga sai wa Kurkure bakin sa ya shaƙi ruwa a hancin sa.

Na biyu: Wanka Cikakke; Shine wanda ya ƙunshi Wajibi da Mustahabbi.

Yadda ake yin wanka cikakke

Mutum zai wanke hannu kafin ya shigar dashi Kwanon wanka, sannan ya ɗebi ruwa ya zuba a farjin sa ya wanke sau uku, sannan sai yayi alwala irin alwalar Sallah cikakke, ko ya jinkirta wanke ƙafa zuwa ƙarshen wanka, ko ya wanke a lokacin. Sannan ya ƙwarara ruwa sau uku a kansa a tsefe suman kan shi har sai ruwan ya game kanshi, sannan ya zuba ruwa a gefenshi na dama, sannan ya zuba a gefen hagu.

Wannan shine wanka cikakke. An rawaito wannan irin wanka daga Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi. Sahihul Bukhari: 317.

Amma wanda ya taƙaita akan wanka na farko to ya wadatar.

Allah shine mafi sani.

Click Here to Support our work

Leave a Reply

%d bloggers like this: