Asali acikin ibada shine dakatawa har sai an samu dalilin yin sa da mayar da Martani kan cewa Hujja shine Annabi ya hana ba Annabi baiyi ba

Wannan ƙa’ida ce mai matuƙar Muhimmanci da ya wajaba akan kowani Musulmi ya fahimce shi.

الأصل في العبادة التوقف

Asali acikin harkan Ibada shine kamewa da dakatawa kada Mutum ya aikata wani Abu sai da dalili.

Wannan Shine abinda yake sananne a shari’ar Musulunci domin idan akace anbar harkar addini kowa ya kawo abinda yaga ya dace da son ranshi to haƙiƙa Hakan zai gurɓata addini ta yadda za’a kasa banbance wa tsaƙanin abinda Annabi yazo dashi da abinda mutane suka ƙirƙira.

Wasu sukan ce ai Hujja shine Annabi ya hana ba wai Annabi baiyi ba

To wannan a hankalce ko babu nassi za’a iya ruguza wannan magana tasu, domin idan har mukayi riƙo da wannan ƙa’ida da suka kawo to zai ruguza tsarin Addinin Musulunci baki ɗayan sa.

Misali Annabi ya koyar da Sallar Asubahi Raka’a biyu amma kuma babu inda yace kada a ƙara da Nassi ƙarara to anan zamu iya cewa toh zamu ƙara ta ta zama raka’a biyar sabida ai Annabi bai hana ba kuma ai Sallah aikin alheri ne.

Haƙiƙa ko masu kawo wannan ƙa’ida na tabbatar bazasu amince da hakan ba amma a haƙiƙa duk wanda ya fahimci ƙa’idar su zai fahimci cewa abinda take nufi kenan.

Kuma amfani da wannan ƙa’ida zai jawo ƙirƙirar bid’oi wanda basu da iyaka, domin kowa zai iya ƙirƙirar tashi kalar ibadar ya kuma kafa Hujja da cewa ai Annabi bai hana ba.

Saboda haka wannan ƙa’ida kuskure ce kuma babu wani daga cikin Maluma da duniyar Musulunci ta yarda dasu da ya taɓa kawo irin wannan ƙa’idar. Ƙa’ida wanda yake sananne shine Cewa “Asali a ibada shine dakatawa har sai ansamu dalili da yake umarni dashi” wannan kuma shine Ayoyi da hadisai suke mara wa baya. Domin an turo Annabi ne saboda ya koya wa mutane yadda zasu bauta wa Allah, idan ya zama cewa kowa zai iya ƙirƙirar ibada da yaga dama kuma a karɓa masa ya zama babu amfanin turo Annabi kenan. Allah yasa mudace.

Hadith: Ka ribaci abubuwa biyar kafin abubuwa biyar

Abdullahi Bin Abbas Allah ya ƙara masa yarda ya Rawaito daga Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yace:

ka ribaci abubuwa biyar kafin abubuwa biyar. Samartakan ka kafin tsufan ka, lafiyar ka kafin rashin lafiyar ka, wadatar ka kafin talaucin ka, sararin ka kafin shagaltuwar ka, rayuwar ka kafin mutuwar ka

Sahihut-Targhib Sheikh Albani: 3355

A wannan hadisi Annabi yana koya mana yadda zamu ribaci rayuwar mu baki ɗaya.

Muyi amfani da samartakan mu kafin tsufar mu: domin lokacin samartaka ne mutum yake da cikakken ƙarfin, duk abinda yake so yayi a lokacin zai fi samun daman yi, amma da zarar mutum ya tsufa to wani abin dole ya gagare shi,

Muyi amfani da lafiyar mu kafin Rashin lafiyar mu: shi rayuwa mutum bazai dawwama da lafiyar sa ba a kowani lokaci, dole wani lokaci rashin lafiya zai kama mutum, wani lokaci ma da zarar rashin lafiyar ta kama mutum to shikenan har ya mutu ba zai samu sauƙi ba, shiyasa anan Annabi yake umartan mu da muyi amfani da lafiyar mu kafin rashin lafiya ta riskemu abinda mukeso muyi mu kasa yi saboda rashin lafiya.

Muyi amfani da wadatar mu kafin talauci: Shi arziƙi bashi da tabbas, zai yiwu yau kana dashi gobe kuma ka wayi gari babu, saboda haka kayi amfani da damar ka, lokacin da kake dashi kayi amfani dashi ta hanyar da ta dace, wurin taimaka wa Addini da ayyukan alheri. Idan aka jarrabe ka da babu to ka riga kayi a baya.

Muyi amfani da Rarar lokaci da muke dashi kafin abubuwa suyi mana yawa: a duk lokacin da ka samu dama da sarari to kayi amfani dashi kafin wani abu yazo ya shagaltar da kai, kayi amfani da lokutan ka wurin neman ilimi da ayyukan alheri, bawai ka zauna kullun kana zaman Majalisa, ko buɗe social media shikenan ba. Duka wannan ba zai tserar da kai ba, kuma ka sani za’a tambaye ka kan wannan lokaci da aka baka.

Muyi amfani da rayuwar mu kafin mutuwar mu: ko meye zamuyi a rayuwa zamuyi shi ne idan muna da rai, da zarar mun mutu to wannan damar ta kuɓuce kenan, Kuma babu wani lada da zamu samu sai dai daga ta hanyoyi uku.

 • Sadaƙa mai gudana(Misali mutum ya tone rijiya, ko ya gina makaranta….)
 • Ilimi wanda ake amfan dashi
 • Yaro na gari ya rinƙa yi mana Addu’a. II ji

Wa’innan hanyoyin sune kaɗai zamu iya samun lada dasu bayan mun mutu.

Mai hankali shine wanda yayi amfani da duniyar sa wurin gina lahirar sa.

Wuraren da ya Halatta ayi Gulman mutum

Gulma shine ka ambaci wani abu na wani wanda baya so a sani. Kamar Mutum na aikata wani abu mara kyau sai kaje kana yaɗa shi a cikin mutane.

Gulma Haramun ne, Amma akwai wasu wurare da ya halatta ayi gulman mutum. Gasu kaman haka:

 • Kai koke: Misalin mutum ya zalunce ka, ka kai koken sa wurin wanda zai bi maka haƙƙin ka, kaman Alƙali ko Waninsa, a lokacin ya halatta kayi bayanin halin wannan mutumi , Misali kace wane ya zalunce ni ya ci mini dukiya da makamantansa.
 • Hani da mummuna: Misali mutum yana aikata mummunan aiki, ya halatta ka faɗa wa wa’inda zasu dakatar dashi su hukunta shi.
 • Neman shawara: Misali wani ya nemi shawarar ka yana so yayi kasuwanci da wani mutum, kai kuma kasan halin mutumin nan bashi da kyau to dole ka faɗa masa gaskiyar halin wannan mutumin. Ko kuma ya nemi shawarar ka yanaso ya aurar da ɗiyar sa ga wani mutum kuma kasan mutumin bashi da hali mai kyau, anan ma dole ka faɗi gaskiyar halin mutumin nan da ka sani.

Addu’ar haduwa da abokin gaba ko wanda ake jin tsoron sa

Abu Musa Al-Ash’ary Allah ya ƙara masa yarda yace:

Annabi Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance idan yaji tsoron wasu mutane sai yace “Allahumma inna naj’aluka fi nuhurihim, wa na uzu bika min shururihim”. اللهم إنا نجعلك في نحورهم ونعوذ بك من شرورهم

Abu dawud: 1537,. Annasa’i: 8631,. Ahmad: 19720

Fassarar Addu’ar

Ya Allah muna sanya ka a mayankan su Ma’ana ( ka tsare mu daga sharrin su idan suka nufe mu da mummunan abu) sannan muna neman tsarinka da sharrukan su.

Wannan addu’a ana yinsa ne idan mutum zai haɗu da wanda yake jin tsoron sa, ko abokin gaban sa da yake jin tsoron zai cutar dashi.

Tsare kanka daga shaidanun Al-janu

Assalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Wa Barakaatuh.

A-janu halittu ne na Allah kamar yadda mutane suke halittu, Cikinsu akwai Musulmai, akwai kafirai, Akwai masu mulki akwai masu kuɗi akwai talaka. Sannan kuma Kamar yadda Shari’a ta hau kanmu haka suma shari’a ta hau kansu.

Abune sananne a shari’a cewa Al-janu suna da banbanci da ƴan Adam, ta yadda suna iya ganin mu amma mu bamu iya ganinsu, Sannan kuma suna iya shiga jikin ɗan adam Kamar yadda Nassoshi na Shari’a suka tabbatar, sannan kuma yanayi na yau da kullum ya tabbatar da hakan.

To yaya Musulmi zai kare kansa daga shaiɗanun Al-janu?

 • Lazimtar Zikirin safe da yamma: in kanaso ka samu kariya daga shaiɗanun Al-janu to ka lazimci zikirin safe da yamma wanda aka Rawaito daga Annabi Sallallahu alaihi Wasallama, Domin wannan zikirin yana ƙunshe da addu’oi wa’inda zasu tsare mutum daga shaiɗanu da masu sihiri, Mutum zai iya amfani da littafin hisnul Muslim ya duba shafin zikirin safe da yamma
 • Yin Bismillah yayin shiga gida: idan Mutum zai shiga gidansa to yayi Bismillah domin idan yayi Bismillah to shaiɗanu bazasu iya shiga gidan ba, Amma idan baiyi ba to zasu bishi su shiga kamar yadda aka rawaito daga Annabi Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, Haka nan yana da kyau mutum ya koya wa yaransa da iyalansa duk wanda zai shiga gida ya rinƙa yin Bismillah kafin Sallama, ta yadda koda ya mance bai yi ba za’a samu wani daga cikinsu yayi.
 • Yin Addu’a yayin fita daga gida: idan Mutum zai fita daga gida sai ya karanta Addu’ar da aka Rawaito daga Annabi, “Bismillah Tawakkaltu alallah Wala haula wala Quwwata illa billah” بسم الله توكلت على الله ولا حول ولا قوة إلا بالله idan Mutum ya karanta wannan Allah zai bashi kariya.
 • Yin Bismillah yayin cin abinci: Idan mutum yazo cin Abinci ya ambaci sunan Allah, idan yayi haka toh zai kore shaiɗanu daga abincinsa, idan kuma baiyi ba to tare dashi zasu ci. Idan ya mance baiyi ba sai yayi a ƙarshe. Yace : “Bismillahi fi awwalihi wa aakhirih” بسم الله في أوله وآخره
 • Yin Addu’a yayin shiga bayan gida: Idan Mutum shiga ban ɗaki yayi Addu’a wanda aka Rawaito. ” Allahumma inni Auzu bika Minal khubthi wal khaba’ith” اللهم إني أعوذ بك من الخبث والخبائث. Hakanan inya fito yayi Addu’a. “Gufranak” غفرانك
 • Yin Addu’a yayin saduwa da iyali: Lokacin saduwarka da iyalinka ka ambaci sunar Allah sannan kayi Addu’a “Allahumma jannibnash-shaiɗana wa jannibish-shaiɗana ma razaqtana” اللهم جنبنا الشيطان وجنب الشيطان ما رزقتنا
 • Yawaita karanta Al’qur’ani Musamman Suratul Baqara: Karanta Al’qur’ani a gida yana korin shaiɗanu musamman Suratul Baqara, domin Annabi yace shaiɗan yana gudu daga gidan da ake karanta suratul baqara.
 • Kawar da duk wani kayan ɓarna daga gida: Dole Musumi ya kula da abinda yake shiga cikin gidansa, kada ya bari ana shigar masa da fina finan batsa, ko waƙoƙi Marasa kan gado da makamantansu, domin wannan yana janyo shaiɗanu cikin gidan
 • Kawar da duk wani hoto: Haka nan hotuna da ake maƙala wa a bango ko ake ajiye su a bayyane suna hana Mala’ikan Rahama shiga gida wanda hakan ka iya janyo shaiɗanu cikin gidan.

Wannan kaɗan ne daga matakan kariya daga shaiɗanun Al-janu. Allah yasa mudace, ya kuma tsare mu daga sharrin su

Wannan ba Barkwanci bane Cin Mutuncin Addinin Musulunci ne

Allah maɗaukakin sarki yace:

Haƙiƙa za’a jarrabe ku cikin Dukiyoyinku, Da kawunanku, sannan kuma zakuji cutar wa mai yawa daga wa’inda Allah ya basu littafi gabaninku(Yahudawa da Nasara) da Mushrikai

Surat Aal Emran: 186

Cutar da Addini da maƙiya addini sukeyi abu ne wanda Allah ya bada labarin cewa zasu yi shi, amma haka bashi yake nufin muyi shiru mubarsu suci gaba da aikata hakan ba, dole mu tashi mu fuskance su muyi iya ƙoƙarinmu wurin baiwa Addinin mu kariya.

Read More…

Bayani kan Kashe Sheikh Goni Aisami da raunin da ya hau kan Al’ummar Musulmi

Assalamu Alaikum ƴan Uwa Musulmi.

Haƙiƙa wannan kisan Gilla da kuma cin Amana da akayi wa ɗan’uwa Sheikh Goni Aisami abune mai matuƙar baƙanta rai, ace Jami’in tsaro da ya kamata ya baiwa mutum kariya shine kuma zai yi irin wannan aiki. Allah ya kyauta.

Amma abinda yafi ja min hankali shine yadda Shuwagabannin mu Musulmai da Masu faɗa aji acikinmu wanda suke gaggawar yin Allah wadai idan aka taɓa wani wanda ba Musulmi ba sukayi shiru kan wannan lamari, Musamman ma wanda ya kashe wannan ɗan uwa ba Musulmi bane, ƙaddara ace Soja ne Musulmi ya kashe Pastor shin kana ga yanzu da ƙasar nan bata ɗauki zafi ba? Bada jimawa ba muna da labarin abinda ya faru da Deborah, Yadda ƙasannan ta ɗau zafi, har shugaban ƙasa sai da yayi jaje yayi Allah wadai, Amma lokacin da aka kashe wata Mata Musulma da ƴaƴanta a ƙasar iyamurai Baka ji ƙasar ta ɗau zafi kamar yadda akayi lokacin deborah ba.

Read More…