Hadisin yau: Falalar Azumin Nafila

Abu Sa’id Allah ya ƙara Masa yarda ya rawaito Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa:

من صام يومًا في سبيلِ الله، باعَدَ اللهُ وَجهَه عن النَّارِ سَبعينَ خريفًا

Wanda yayi Azumin kwana ɗaya domin Allah, Allah zai nesanta fuskansa ga barin wuta tsawon Shekaru saba’in

Bukhari: 2840, Muslim: 1153

Sharhi: Wannan hadisi yana nuna mana falalar yin azumi, da kuma yinsa don Allah. Duk wanda yayi azumi na kwana ɗaya domin Allah bai haɗa shi da riya ba Allah zai bashi lada mai girma sannan kuma zai nesanta fuskarsa ga barin Wuta tsawon shekaru Har saba’in.