Hadith: Haramcin Gina Masallaci akan kabari

Danna nan domin shiga group na karatu Online

عائشة -رضي الله عنها-، قالت: لما نُزِلَ برسول الله -صلى الله عليه وسلم-، طَفِقَ يَطْرَحُ خَمِيصَةً له على وجهه، فإذا اغْتَمَّ بها كشفها فقال -وهو كذلك-: “لَعْنَةُ الله على اليهود والنصارى، اتخذوا قبور أنبيائهم مساجد -يُحَذِّرُ ما صنعوا”. ولولا ذلك أُبْرِزَ قَبْرُهُ، غير أنه خَشِيَ أن يُتَّخَذَ مسجدا

Sahihul Bukhari: 435

Fassara da Sharhi:

An rawaito daga Aisha Allah ya ƙara mata yarda tace: Lokacin da mutuwa tazo wa Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yana cikin Magagin mutuwa sai yace: Tsinuwar Allah ta tabbata akan Yahudawa da Kirista, sun riƙi ƙaburburan Annabawan su wurin bauta, yana tsoratar wa game da abinda suka aikata sai A’isha Allah ya ƙara mata yarda tace: da ba dun Tsoron kada a riƙi ƙabarin Annabi Sallallahu alaihi Wasallama a matsayin wurin bauta ba da an fitar da ƙabarinsa waje. Ma’ana da ba’a binne shi a cikin ɗakin ta ba, da an fitar dashi Maƙabartar Musulmai a baƙi’ an binne shi.

Wannan Hadisi yana nuna Haramcin gina Masallaci akan Maƙabarta, Da Sallah acikin ta.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories