Aswaki: Sunnar da mata sukayi watsi dashi

·

·

Domin neman ƙarin bayani danna nan

Hadisai sunzo daga Annabi Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi kan falalar yin aswaki, lokacin alwala, sallah, shiga gida, lokacin da mutum yaji canji cikin bakinsa, ko lokacin da mutum ya tashi a bacci.

daga cikin hadisan da suka zo kan aswaki:

السواك مطهرة للفم مرضاة للرب

Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yace Shi aswaki yana tsarƙaƙe baki, kuma yana yardar da Ubangiji.

Sannan kuma an sake rawaito wa daga gareshi yace:

لولا أن أشق على أمتي لأمرتهم بالسواك عند كل صلاة

Da ba don kada na takura wa al-ummah ta ba da na umarce su da yin aswaki lokacin kowani Sallah.

Sahihul Bukhari: 7239

Wannan yake nuna mahimmancin aswaki, da yadda Annabi yake bashi mahimmanci hatta kafin Allah ya ƙarbi ransa sai da yayi aswaki kamar yadda A’isha Allah ya ƙara mata yarda ta bada labari.

Sannan an rawaito daga Aisha Allah ya ƙara mata yarda tace:

أنَّ النبيَّ صَلَّى اللَّهُ عليه وسلَّمَ كانَ إذا دَخَلَ بَيْتَهُ بَدَأَ بالسِّواكِ

Manzon Allah ya kasance idan zai shiga gidansa yakan fara ne da aswaki.

Sahih Muslim: 253

Hukuncin Aswaki gun mata:

Kamar yadda aka sani ne cewa shi hukuncin addinin Musulunci yana game maza da mata ne baki ɗaya sai dai in an sami abinda ya banbanta su. Kamar yadda muka gani cikin wannan hadisan aswaki babu wani abu dake nuna cire mata kan aikata wannan sunnah. Sai dai sau da dama ba kasafai kake ganin mata suna raya wannan sunnah ba.

a matsayin ka na mai gida ya dace daga yau in zaka saya wa kanka aswaki toh ka saya wa iyalinka domin ku raya wannan sunnah tare.

Sannan shi yin aswaki lokaci zuwa lokaci yana kare mutum daga warin baki wanda hakan zai ƙara danƙon Soyayya tsaƙanin ma’aurata.

Allah yasa mudace.

Leave a Reply

Latest updates
Categories