Riƙo da sababi da dogaro ga Allah

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Allah yana da daman ya aikata abinda yakeso a lokacin da yakeso babu mai hanashi, haka nan Allah ya ƙaddara wa mutum duk abinda zai sameshi, amma wannan ƙaddarar tana gudana ne da sababi.

Shiyasa Allah ya umarci bayinsa da su roƙeshi, sannan su fita su nemi arziƙi, sannan su yi ƙoƙarin neman hanyan shiriya domin subi. Idan sukabi umarnin Allah sukayi riƙo da wannan sababi sai Allah ya Azurtasu, ya basu lafiya daga cututtukan dake damunsu, sannan kuma ya nuna musu hanyar shiriya bisa wannan riƙo da sababi da sukayi.

yana daga cikin misalai ta Sunnar Allah kan riƙo da sababi:

  • Allah yana da daman ya tsaga teku domin Annabi Musa Alaihissalam ya wuce shi da mabiyansa, amma domin ya tabbatar da wannan sunnah tashi sai yayi umarni wa Annabi Musa Alihissalam da ya bigi tekun, bayan ya buga sai ta rabe gida biyu suka wuce shi da mutanensa, irin wannan misalan suna da yawa a Al-Qur’ani da Sunnah.

Riƙo da sababi bashi yake nuna kuma mutum ya dogara da sababi baki ɗaya ya bar Allah subhanahu wata’ala ba. A’a. Mutum zaiyi riƙo da sababi ne sai kuma ya dogara da Allah domin samun cimma nasara.

Annabi Nouhu Alaihissalam lokacin da ya kwashi wa’inda sukayi Imani dashi cikin jirgi domin su guje wa Azaba da Allah zai sauƙar kan mutanensa. A lokacin da ya kwashi mutanensa domin kauce wa ruwa da Allah ya turo domin halakar da kafirai daga cikin mutanensa, a lokacin ya sami yaronsa wanda ya kasance baiyi imani dashi ba, ya ƙirashi da cewa yazo ya hau wannan jirgi domin su tsira tare, sai wannan ɗa nashi yace shi zai hau dutse domin tsira daga wannan Azaba. Amma daga ƙarshe Allah ya halakar dashi ɗan duk da cewa yayi riƙo da sababi. Amma rashin imaninsa, da dogaro da dabararsa da yayi ba tare da riƙo da Allah ba sai Allah ya halakar dashi. Amma Annabi Nouh ya tsira. Shiyasa duk abinda mutum zaiyi, da duk riƙo da sababi da mutum zaiyi ya rinƙa halarto da Allah cikin zuciyarsa, kada ya yarda ya dogara da Ƙoƙarinsa kawai.

Wanda ya fahimci wannan bazai zauna a gida yace ya dogara da Allah in Allah ya ƙaddara masa zai samu zai samu, in kuma Allah ya ƙaddara masa zai rasa zai rasa.

Haka nan wanda ya fahimci wannan bazai ƙi yin aikin Ɗa’a ba, yace in Allah ya ƙaddara masa shi ɗan wuta ne zai shiga wuta, haka nan inkuma Allah ya ƙaddara masa shiga aljannah zai shiga. Zai tashi ne yayi aiki, ya roƙi Allah shiriya domin ya sami dacewa.

Allah yasa mudace.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories