Riko da sababi

·

·

Domin neman ƙarin bayani danna nan

Mai rubutu: Hamza Diso


Riko da sababi

Dogaro ga Allah na hakika ana yin shine tare da riko da sababi, duk da cewa Annabi yana da tabbas Allah zai taimake shi akan lamuran sa Amma bai daina riko da sababi ba, a lokacin da zai yi hijrah sai da ya tsara komai cikin sirri kafin yabar gida, sanda zai fadawa Sayyidina Abubakar Shirin tafiyar sai yaje gidansa ba a irin lokacin daya Saba zuwa ba, yazo bayan rana ta take, saboda lokacin kowa yana gida a Makkah ba a fitowa waje, sannan ya nemi Sayyidina Abubakar ya sallami duk wanda yake gurin kafin ya fadi abinda ya kawo shi.

Sanda zasu fita hijrah kuma suka fita ta kofar bayan gidan Sayyidina Abubakar bata gaba ba, ya kuma batar da sawu ta hanyar barin Sayyidina Ali akan shinfidar sa ta yadda za a zaci yananan, sannan daya fita daga Makkah bai dauki hanyar Madina kai tsaye ba, sai da ya sami gurin buya a wajen Makkah ta yadda ko an fito neman sa baza a ganshi a hanya ba, basu fito daga maboya ba har sai da masu nema suka fara gajiya.

Bai bari wani yasan zai fita ba har cikin musulmi banda Wadanda Shirin tafiyar ya hada dasu, kamar Sayyidina Ali Wanda shine zai kwanta a wajensa, sai mutan gidan Sayyidina Abubakar. Kai har mutan gidan Sayyidina Abubakar din basu da tabbas cewa Madina za aje, don ibn Hisham a cikin sira yace: sai da labari yazo Makkah cewar su Annabi Sun wuce ta wajen ummu ma’abad sannan Asma’u yar Sayyidina Abubakar ta gane Madina aka tafi

Sannan duk da shi Annabi ne Amma sai da ya dauki hayar dan jagora masanin hanya Wanda zai iya bi dasu ta hanyar datafi dacewa.

Duka wannan kokarin Yin riko da sababi ne, sai dai idan Kuma kayi iya yinka sai aka sami matsala to sai ka tsaya ka jira taimakon Allah kamar yadda ya faru bayan su Annabi sun buya kuma masu neman su suka zo bakin kogon, haka kamar yadda ya faru bayan Suraka bn Malik yabi su don ya kamasu nan ma taimakon Allah sai yazo.

Abun nufi Kawai kada ka zauna kace kana jiran taimakon Allah don kai kana kan gaskiya ko don kai mutumin kirki ne, ko don kana San cigaban Al’umma, ka zaci nasara zata zo maka daga sama.

Dole sai kayi da gaske, kuma dole sai ka sami matsala, dole ka Fadi sannan ka tashi, za a bata maka rai za a cutar dakai za a tsorata ka, Amma idan kayi hakuri nasara taka ce.

An jefi Annabi an zage shi an karya masa hakori Amma daga karshe shine yayi nasara.

Leave a Reply

Latest updates
Categories