TSAKANIN COVID-19 DA FATAWA

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Mai rubutu: Hamza Diso


Daya daga cikin mas’alolin da aka samu sabani tsakanin Mu’atazila da Sunnah itace mas’alar


التحسين والتقبيح العقلي

Shin hankali shine zai rarrabe tsakanin Abu mai kyau da Mara kyau? Ko kuwa shari’a ce kawai take da damar haka? Shin zamu bautawa Allah da abinda hankalin mu ya nuna mana ko kuma zamu koma ga shari’a?

Fahimtar malaman sunnah itace; shari’a ce kawai take da damar sanar da abinda yake dai-dai da kuskure, saboda hankulan yan Adam yana samu fifiko daga mutum zuwa mutum, sannan dan Adam yana da son zuciya da nemawa kansa maslaha, don haka dole mu komawa shari’a ta bamu haske kan dukkannin Al’amuran mu.

A takaice duk abinda ya taso ya kamata mu tambayi shari’a muji menene hukuncin wannan Abu, gini akan haka nake cewa

Shari’ar musulunci tayi mana umarni muyi duk wani Abu da zai kare lafiya da rayuka na Al’umma.

Allah madaukaki yace:


وخذوا حذركم

(Ku riki kariya/Tsarin Ku) wato kubi duk hanyar data dace wajen kare rayukan Ku, Ku tsaya cikin shirin ko ta kwana, wannan yasa a lokacin yaki musulmi suke sallah da makamansu a hannu.

Annabi- salatin Allah da amincinsa a gare shi- yace:


لا ضرر ولا ضرار


(Babu cutarwa) shiyasa aka hana Wanda yaci Albasa ko tafarnuwa zuwa sallar jam’i don kada ya cutar da musulmi da warin Tafarnuwa!!
Wannan yasa aka halatta mutane suyi sallah a gidajen su don gudun duhun dare idan ya hadu da cha’bal’bali, (ta’bo) kamar yadda Sahabi Dan Abbas yayi.

Shari’a ta koya mana cewar duk abinda ya taso to mu tambayi masana wannan Abu akan yanayinsa
Allah yace:


فَاسْأَلُوا أَهْلَ الذِّكْرِ إِن كُنتُمْ لَا تَعْلَمُونَ

(Ku tambayi masana idan Baku sani ba) wannan aya gamammiya ce; wato duk abinda baka sani ba to ka koma ga masanansa, idan abu yana da alaka da gini sai ka tambayi magina, idan lafiya ce tambayi likitoci, shiyasa likita ne (amintacce) yake da damar yin fatawa akan Mara lafiya, shin cutar tasa takai ta hanashi azumi ko bata kai ba

Tawakkali na gaskiya shine Wanda ake yinsa bayan anyi riko da sababi, bazaka kai kanka ga halaka sannan kace Allah zai kareka!!
Wannan shiyasa Annabi ya hana chakuda rakumi mai lafiya da marasa lafiya, duk kuwa da cewar Allah ne mai Dora cuta!!
Kuma Annabi yace a cikin hadisin Abi hurairah Wanda Ahmad ya ruwaito da isnadi mai kyau
( ka gujewa mai cutar kuturta yadda zaka gujewa Zaki) sannan Annabi ya hana zuwa garin da ake Annoba, duk wannan riko da sababi ne.

Saboda haka idan masana Lafiya sunce kowa ya koma gida, to komawar itace biyayya ga koyarwar Addini

Allah yasa mu gane, Allah ya bamu lafiya da aminci da yalwar Arziki

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories