Tafsirin Suratul-Qasas Aya ta 60: Duniya ba komi bace Lahira itace abin nema

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Allah maɗaukakin sarki yace:

{ وَمَاۤ أُوتِیتُم مِّن شَیۡءࣲ فَمَتَـٰعُ ٱلۡحَیَوٰةِ ٱلدُّنۡیَا وَزِینَتُهَاۚ وَمَا عِندَ ٱللَّهِ خَیۡرࣱ وَأَبۡقَىٰۤۚ أَفَلَا تَعۡقِلُونَ }

[Surah Al-Qasas: 60]

Fassara/Sharhi

Kuma Duk abinda aka baku Anan duniya na koma menene, to na ɗan Jin daɗin Rayuwar duniya ne da ƙawarta, Amma abinda yake wurin Allah shine yafi alheri, kuma yafi wanzuwa, Shin baku hankalta?

A wannan Ayah Allah yana bayani game da Rayuwar duniya, da kuma jin daɗi da ɗan Adam ke samu acikin ta, na dukiya da ƴaƴa da Allah yake azurta shi dasu, da duk wani abu dai wanda ɗan Adam yake so anan rayuwar duniya. Duka wa’innan abubuwa ba komi bane kawai

jin daɗi ne na ɗan lokaci kaɗan. Abinda yake wurin Allah ga wa’inda suka bauta masa suka bi umarninsa anan duniya shine mafi alheri, domin dawwamamme ne har abada baya gushe wa.

Duk wani Abinda ɗan Adam zai samu anan duniya na abin duniya jarabawa ce, kuma za’a tambaye shi akansa. Ta yaya ya samu, sannan ta yaya ya kashe. sannan ita jin daɗin duniya ba mai dawwama bace, domin zai yiwu mutum yau na da dukiya gobe ya wayi gari bashi da komi, haka nan mutum zai iya zamto wa yau na da cikakken lafiya washegari ya tashi babu lafiya. to haka rayuwar duniya take, tsaɓanin lahira inhar Mutum ya shiga Ni’imar Allah to babu fita har abada. Sabida haka mai hankali shine wanda zaiyi iya ƙoƙarin sa wurin gina lahiransa ba duniyarsa ba, kada ya zamto kawai tunanin Mutum duniya. Babu laifi mutum ya nemi duniya ya tara yayi ayyuka na alheri masu yawa wataƙila hakan shine silar shigarsa Aljanna, amma abinda ake magana akai shine kada mutum ya zama duniyar ce kawai a gabansa, ya mance da lahira.

Mai hankali shine wanda kullum tunaninsa mutuwa, yana lissafin cewa Allah zai iya ɗaukan Ransa a koda yaushe sabida haka duk abinda yake yi yana tuna Allah baya cutan mutane, baya aikata munanan saɓon Allah, kuma yana mai gaggawan tuba da zarar ya aikata wani abinda bai dace ba, domin tsoron kada Allah ya ɗauki ransa a yanayi wacce bata dace ba.

Allah ya sanya mu cikin masu hankali, masu tunani, ya kuma sanya mu cikin masu rabauta.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories