Tafsirin Suratul An’am Aya ta 82: Imani da Allah da Guje wa Shirka

Allah maɗaukakin sarki yace:

{ ٱلَّذِینَ ءَامَنُوا۟ وَلَمۡ یَلۡبِسُوۤا۟ إِیمَـٰنَهُم بِظُلۡمٍ أُو۟لَـٰۤىِٕكَ لَهُمُ ٱلۡأَمۡنُ وَهُم مُّهۡتَدُونَ }

[Surah Al-An`âm: 82]

Fassara/Sharhi

Wa’inda Sukayi Imani Sannan basu cakuɗa Imaninsu da Zalunci(Shirka) ba, Wa’innan sune suke da Aminci, kuma sune Shiryayyu.

Allah maɗaukakin sarki yana Bayani a wannan Ayah game da Mahimmancin Imani, Sannan kuma da haɗarin Shirka wanda shine ma’anar Zalunci a wannan Ayah kamar yadda Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya fassara. Kamar yadda Imamul Bukhari ya kawo:

Abdullahi Bin Mas’ud yace:

Lokacin da wannan Ayah ta sauƙa Sai Sahabban Annabi suka ce wanene acikin mu bai zalunci kansa ba? Sai Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yace Musu ba wannan bane Anan ana nufin Haɗa Allah da wani(Shirka). Shin baku ji faɗin Luƙman wa ɗansa ba? ” Ya Ɗa na kada ka haɗa wani da Allah wurin bauta, domin Haɗa wani da Allah wurin bauta zalunci ne mai girma Surau Luƙman: Ayah 13.

Sahihul Bukhari: 3360

Wannan Yake nuna Cewa Zalunci da ake nufi acikin wannan ayah shine Haɗa Allah da wani wurin bauta. Domin Allah baya gafarta wa Wanda ya haɗa shi da wani wurin bauta matuƙar ya mutu bai tuba ba.

Sannan Wannan Ayah tana nuna mana cewa in mutum yana neman zaman lafiya da kwanciyar Hankali to ya riƙe Allah shi kaɗai, sannan ya bauta wa Allah kada ya haɗa shi da wani, domin yin haka shi zai sa ya samu aminci.

Haka nan wannan Ayah tana nuna mana cewa Shiryayye shine wanda Yake da Imani, kuma baya shirka, duk wanda ya zamto bashi da Imani, ko kuma yana haɗa Allah da wani wurin bauta to ba shiryayye bane.

Allah ya sanya mu cikin masu Imani ya kuma Shiryar damu tafarki madaidaiciya ya kuma tsare mu daga shirka.

Click Here to Support our work

Leave a Reply

%d bloggers like this: