Al-Qur’ani Mu’ujizar Annabi Muhammad

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Allah maɗaukakin sarki yace

قل لئن اجتمعت الإنس والجن على أن يأتوا بمثل هذا القرآن لا يأتون بمثله ولو كان بعضهم لبعض ظهيرا

Kace ya manzon Allah, idan da mutane da aljanu zasu haɗu domin su kawo kwatankwacin Al-Qur’ani mai girma baza su iya kawo wa ba, koda ko sunyi taimakekeniya tsakanin su

Kamar yadda aka sani ne larabawa sun kasance masu matuƙar fasahar zance tun a jahiliyyah, sun kasance suna da mawaƙansu, suna da masu Huɗubarsu, da kuma masu zance mai cike da Kalamai masu daɗi da kuma fasaha. Amma lokacin da Annabi yazo da Al-Qur’ani mai girma sai suka ruɗe, suka rasa gane wani irin zance ne wannan mai cike da ban mamaki, wasu daga cikinsu sukayi imani da annabi wasu kuma suka ƙi yi suka shiga gaba da wannan Al-Qur’ani da Annabi yazo dashi. Suka rinƙa yi wa Annabi laƙabi da Mahaukaci, boka da sauransu, kuma sukace ai in sunga dama suma zasu iya zuwa da magana kamar irin ta Al-Qur’ani. Toh sai Allah ya ƙalubalance su acikin Al-Qur’ani a wurare daban daban, a wani wurin ya neme su da su kawo kwatankwacin Al-Qur’ani, suka kasa, sai ya neme su da su kawo surah ɗaya tal, nan ma suka kasa, sai ya sake nemansu da su kawo ayah ɗaya tal. Nan ma suka kasa duk da fasahar zancen su da kuma tsananin son suga sun gushe hasken da Annabi yazo dashi.

Da haka ne mutum zai gane mu’ujizar Al-Qur’ani, kuma zai fahimci cewa Al-Qur’ani maganar Allah ne. Babu wanda ya isa yazo da irinta har tashin Al-Qiyaama.

Sheikhul Islam Ibn Taimiyyah Rahimahullahu yana cewa acikin littafinsa mai suna Aljawabussahih liman baddala dinal masih 4/73-74

Kafirai a zamanin annabi sun kasance masu tsananin son ɓata abinda Manzon Allah yazo dashi na Addinin gaskiya, suna iya ƙoƙarinsu domin cimma wannna buri nasu, wasu lokuta sukan je wurin Yahudu ko nasara su musu tambayoyi kan al’amarin gaibu wanda littafinsu yazo dashi domin suzo su tambayi Manzon Allah a kai kamar yadda suka tambayi annabi game da labarin Annabi Yusuf(Alaihissalam) da kuma Ashabul Kahfi, da kuma Zul Ƙarnaini.
Wani lokaci kuma sukan taru suyi zama kan me zasu lanƙaya wa annabi na suna? Wasu lokuta su kirashi da Mahaukaci, wasu lokuta su kirashi da mai sihiri, wasu lokuta su kirashi da boka, wasu lokuta su kirashi da mawaƙi. Toh idan har ya zamto irin wannna tsananin ƙiyayya da suke nuna wa da’awar annabi da kuma tsananin son su da su gusar da wannan haske da annabi yazo dashi zai samu idan suka amsa ƙalubale da ya basu, toh har idan zasu iya da sun amsa wannan ƙalubale sun kawo ayah ɗaya tal kaman ta Qur’ani, domin da sunyi haka da shi kenan sun rusa da’awar baki ɗaya, amma da yake Ƙur’ani maganar Allah ne, ba zasu iya kawo irin ta ba, sai suka kasa amsa wannan ƙalubale, kuma ya tabbata cewa Alƙur’ani mu’ujiza ce.

Mai son ganin nassin maganar sai ya duba littafin. Wannan fassara ne akayi da kuma sharhi da ɗan ƙarin bayani

Sabida haka haryanzu babu wani wanda ya isa yazo da kwatankwacin Al-Qur’ani har duniya ta naɗe, Allah ya turo annabawa da mu’ujizozi, shi Annabi sai Allah ya bashi Al-Qur’ani ya zamto shine mu’ujizar sa. Komai yana cikinsa, in kanason tsira duniya da lahira toh ka lazimce shi. Allah yasa mudace.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories