Kula da karatun Alqur’ani da kuma tadabburin sa

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Al-ƙur’ani shine Mu’ujizar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, wanda ya kasance gagara badau, Allah ya ƙalubalanci mutane da Aljanu da su kawo ayah ɗaya amma sun kasa.

Dukansa shiriya ne, kuma shine igiyar Allah da duk wanda ya riƙe bazai ɓace ba.

A duk lokacin da mutum ya kusanci Al-ƙur’ani Wurin haddace shi, da kuma fahimtar sa, da kuma tilawarsa, da kuma tadabburin sa, da aiki dashi toh haƙiƙa Imanin sa zai ƙaru, kuma hanyoyin shiriya zasu buɗe masa, kuma zai samu dace cikin lamuransa.

Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace:

Wanda yabi ƙur’ani yana kan shiriya, wanda kuma ya barshi yana kan ɓata.

Muslim: 2408

Mafi kyawun alaƙar musulmi da Al-ƙur’ani:

  • Mutum ya samu lokaci na musamman a kowani rana domin karanta Al-ƙur’ani da kuma Nazarinsa. Kodai yayi shi kaɗai ko kuma ya haɗu da wasu su rinƙa yi tare.
  • Mutum ya kula da fahimtar ma’anonin Al-ƙur’ani da kuma balagarsa, domin haka zai ƙara wa mutum imani da kuma ganin girman Al-ƙur’anin. Idan ya zamto mutum baya iya fahimtar ayoyin toh sai ya sami Malami da zai rinƙa zuwa wurinsa yana koya masa, ko kuma ya sami tafsirin maluma a kaset ya rinka bibiya.

Allah yasa mudace, ya kuma sa Al-ƙur’ani ya zamto hujja gare mu ba hujja a kanmu ba.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories