KIRA ZUWA GA TAFARKIN MAGABATA NA QWARAI (Manhajus Salafis Salih). *** 017 AQIDAR AHLUS SUNNAH (Daga Sheikh Muhammad Salih al-Uthaimin).(Sheikh Aliyu Said Gamawa)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

4. Muna kuma ba da gaskiya cewa lallai Allah Yana magana da abin da Ya so, lokacin da Ya so, yadda (kuma) Ya so.
“Allah Ya yi magana, da (Annabi) Musa magana ta haqiqa.” Nisa’i: 164).
Haka ma Allah (S.W.T.) Ya ce,
“A yayin da (Annabi) Musa ya zo wa alqawarinmu, kuma “Ubangijinsa Ya Yi zance da shi.” (A’raf:143).
“Kuma sai Muka yi kiran sa daga nan kusa da dutsen nan da ke dama, sai Muka kusantar da shi, yayin ganawa.” (Maryam:52).
Muna kuma ba da gaskiya cewa:
“Kuma da a ce duk abin da ke bayan qasa na daga itatuwa su zama alqaluma, kuma (ruwan) teku ya zamar musu tawada, a kuma sami wasu tekun guda bakwai su qaru a bayansa, zancen Ubangijina ba zai qare ba. Lallai Allah Buwayayye ne (kuma gwani) Godadde.” (Luqman: 27).
Ya kuma ce:
“In da a ce ruwan teku ya kasance tawada ga zancen Ubangijina, da (ruwan) tekun zai qare gabannin zancen Ubangijina ya qare) Kahf:109.
Allah Ya tsarkaka ga barin abin da suke hada shi da su. Shi ne Allah wanda halittar sammai da qassai suna yi Masa tasbihi (suna tsarkake Shi) Shi ne Buwayayye kuma Gwani.
Muna kuma ba da gaskiya cewa lallai Allah Shi ne ne mamallakin sammai (bakwai) da qassai (bakwai). Yana halittar abin da Ya so, Ya bai wa wanda Ya ga dama yaya mata, Ya kuma bai wa wanda Ya ga dama yaya maza ko kuma Ya surka musu maza da mata, Ya kuma mayar da wanda Ya ga dama bakarare (wanda ba ya haihuwa). Lallai Shi Masani ne kuma Mai iko.
Muna kuma ba da gaskiya cewa:
“Lallai babu wani abu mai kama da Shi, Shi ne Mai ji, Mai gani. Ragamar sammai da ta qasa naSa ne, Yana shimfida arziki ga wanda Ya so, Ya kuma quntata (wa wanda ya so) lallai Shi Masanin komai ne.)” Zukhruf:11-12.
Muna kuma ba da gaskiya cewa:
“Babu wata dabba, wato mai rarrafe a bayan qasa, face arzikinta na ga Allah. Ya san matabbatarta da ma’ajinta, duk suna cikin wani bayyanannen littafi (Lauhul Mahfuz).” Hud:6.
5. Muna kuma ba da gaskiya cewa, lallai kalmominSa su ne mafi cikakkun kalmomi a gaskiya wajen labari da kuma adalci wajen hukunci, kuma mafiya kyau wajen zance. Allah ta’ala ya ce:
“(Kalmar Ubangijinka ta cika da gaskiya da adalci).” An’am:115
Ya kuma ce:
“Wane ne ya fi Allah gaskiyar zance?” Nisa’i:122.
6. Muna kuma ba da gaskiya cewa lallai Alqur’ani mai girma maganar Allah ta’ala ne, ko shakka babu, kuma shi ne ya saukar da shi ga mala’ika Jibrilu, sai kuma shi Jibrilu ya saukar da shi ga zuciyar Ma’aikin Allah (S.A.W.) Allah Ta’ala ya ce:
“Ka ce tsarkakakken rai shi ne ya saukar da shi daga Ubangijinka da gaskiya (wato Jibrilu).” Nahl:102.
Ya ce kuma:
“Lallai Shi Alqur’ani abin saukarwa ne daga Ubangijin talikai. Amintaccen ran nan Jibrilu ya saukar da shi a cikin zuciayarka, don ka kasance cikin masu gargadi, kuma da harshe ne na Larabci wanda yake bayyananne.” (Shu’ara’i 192-195).
7. Muna kuma ba da gaskiya cewa lallai Allah ta’ala Yana sama ga bayinSa da zatinSa da kuma sifofinSa, don fadarSa da ya yi cewa:
“Kuma Shi ne maxaukaki, Mai girma.” (Shura:4)
Da kuma fadarSa cewa:
“Shi ne Mai rinjaye a kan bayinsa, Shi ne Gwani Masanin komai.” (An’am:18)
Muna kuma ba da gaskiya, cewa lallai:
“Ubangiji Shi ne ya halicci sammai da qasa cikin kwanaki shida, sannan Ya daidaita a kan Al’arshi, Yana juya al’amura.” (Yunus:3)
Abin nufi da daidaituwarSa a kan Al’arshi, Shi ne daukakarSa a kanSa, da zatinSa, da daidaita da ta dace da sarautarSa, da kuma girmanSa, babu mahaluki da ya san haqiqanin ta sai Shi Allah.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories