KIRA ZUWA GA TAFARKIN MAGABATA NA QWARAI (Manhajus Salafis Salih). *** 020 AQIDAR AHLUS SUNNAH (Daga Sheikh Muhammad Salih al-Uthaimin).(Sheikh Aliyu Said Gamawa)

·

·

Domin neman ƙarin bayani danna nan

16. Muna kuma ba da gaskiya cewa Allah Ta’ala yana yin fushi da wanda ya cancanci fushinSa a cikin kafirai da makamantansu. Ya ce:
“Masu mummunan zato ga Allah, mummunan sakamako zai tabbata a kansu kuma Allah Ya yi fushi da su.” (Fath:6).
Ya kuma ce:
“Amma wanda ya buxe zuciyarsa da kafirci, to fushin Allah ya tabbata a kansa, kuma suna da azaba mai girma.” (Nahl:106).
17. Muna kuma ba da gaskiya cewa lallai Allah Ta’ala Yana da fuska wacce ake siffatan shi da daukaka da girma. Allah Ta’ala Ya ce:
“Fuskar Ubangiji mai Girma da Baiwa ita ce za ta wanzu.” (Arrahmaan:27).
18. Kuma muna ba da gaskiya cewa Allah Ta’ala Yana da hannaye biyu masu baiwa kuma masu Girma. Ya ce:
“HannayenSa biyu shimfadaddu ne, Yana ciyarwa yadda ya ga dama.” (Ma’ida:64).
Ya kuma ce:
“Ba su san darajar Allah, gaskiyar darajarSa ba, qasa baki dayanta tana cikin damqarSa, zai kuma nade sammai da (hannunsa) na dama, tsarki ya tabbata gare Shi, kuma Ya daukaka ga barin abin da suke hada shi (da su). Zumar:67.
19. Muna kuma ba da gaskiya cewa: Lallai Allah Taala Yana da Idanu biyu na haqiqa, don faxarSa da ya yi cewa:
“Ka qera jirgin ruwa a kan IdanunMu, kuma tare da wahayinMu.” (Hud:37).
Manzon Allah (S.A.W.) kuma ya ce:
“ShamakinSa haske ne. Da zai bude shi wallahi da hasken fuskarSa ya qone duk abin da ya tuqe gareshi daga halittarSa.”
20. Kuma AhlusSunnah sun yi ijmai a kan cewa: Idanun Allah biyu ne. Kuma zancen nan na Maaikin Allah (S.A.W.) ya qarfafa wannan maganar. Ita ce fadarsa da ya yi game da Dujal. Sai ya ce: (Lalle mai ido daya ne, kuma lallai shi Ubangijin naku Allah ba mai ido daya ba ne).
Muna kuma ba da gaskiya cewa lallai Allah Ta’ala.
“Idanu ba sa riske Shi, Shi ne yake riske idanu, Shi ne (Sarki) Masanin lamari (kuma) Masanin komai.” (An’am:103).

Leave a Reply

Latest updates
Categories