KIRA ZUWA GA TAFARKIN MAGABATA NA QWARAI (Manhajus Salafis Salih) *** 006 — TAFARKIN MAGABATA NA QWARAI:(Sheikh Aliyu Said Gamawa)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Dukkan magabata wadanda suka rayu cikin tsantsar bautar Allah, ba su tsaya a kan komai ba sai tafarkin Sunnar Manzon Allah (S.A.W.). Sun gina daukacin rayuwarsu, Ibadarsu da muamalarsu da ladubansu da kuma halayensu a kan aqidar Musulunci sahihiya wadda ta cizgo daga Littafin Allah da Sunnar ManzonSa. Suna riqo da umarnin Allah da gudanar da addininsu ba tare da qetare iyaka ba, domin Allah Ya Yi hani da gabatar da wani aiki ko qauli wanda Shi da manzonSa ba su hukunta ba, kamar yadda ya ambata cewa: “Ya ku wadanda kuka yi imani, kada ku gabatar (da komai) gaba ga Allah da ManzonSa. Kuma ku ji tsoron Allah. Lallai ne Allah mai ji ne, kuma Masani ne.” (Hujuraat:01).
Hanya karbabbiya ita ce wadda Manzon Allah (S.A.W.) ya zo da ita, kuma ita ce hanyar magabatan farko. Allah (S.W.A.) Ya yi wa wadannan muminai magabata shaida ta qwarai kan da’awarsu gare shi da bin tafarkin Manzon tsira, a inda yake cewa: “Iyaka dai maganar muminai, idan aka kira su zuwa ga Allah da manzonSa domin ya yi hukunci a tsakaninsu, sukan ce ne, “Mun ji kuma mun yarda, kuma wadannan su ne masu cin nasara.”. (Nur:51).
Kuma kasancewar wadannan magabata masu tsananin tsoron Allah ne da tsarkake zuciya tare da tawali’u ba za a sami wani qetare iyaka daga garesu ba. Saboda haka duk qarin bayanin da suka yi cikin mas’alolin addini, ko dai a daidaikunsu, ko kuma cikin tarayya, to ba za a ce su sun saba da tafarkin Sunnar Manzon Allah (S.A.W.) ba. Domin a tattare da bin littafin Allah da Hadisin manzonSa, akwai riqo da hanyar wadanda suka rayu da shi manzon Allah (S.A.W.) da kuma wadanda suka biyo bayansu da kyautatawa. Allah (S.W.A.) yana ce wa manzonSa (S.A.W.): “Ka ce wannan ce hanyata, ina kira zuwa ga Allah a kan basira ni da wadanda suka bi ni, tsarki ya tabbata ga Allah. Ban kasance daga masu shirka ba.” (Yusuf:108).
Haka kuma Manzon Allah (S.A.W.) ya yi mana umarni da riqo da tafarkinsa tare da na Halifofinsa masu shiryarwa, a cikin wani Hadisi ingantacce wanda Ahmad da Abu Dauda da Tirmizi da Ibn Majah duk sun ruwaito shi cewa:
“…Duk wanda ya rayu cikinku bayana, a sannu zai ga sabani mai yawa. Don haka na hore ku da ku yi riqo da tafarkina, da kuma tafarkin Halifofina shiryayyu, kuma masu shiryarwa, ku qanqame kuma ku cije da turamen haqoranku. Sannan na hane ku da qirqirarrun alamura, domin duk qirqirarrun alamura bidia ne kuma dukkan bidia bata ce.”
Wadannan dalilai dai suna fahimtar da mu cewa irin hidimar da magabata suka yi na qara fitowa da hukunce-hukunce na Musulunci ta hanyar Ijtihadi ba ta saba da tafarkin Sunnar Manzon Allah (S.A.W.) ba.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories