KIRA ZUWA GA TAFARKIN MAGABATA NA QWARAI (Manhajus Salafis Salih) *** 001(Sheikh Aliyu Said Gamawa)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

KIRA ZUWA GA TAFARKIN MAGABATA NA QWARAI (Manhajus Salafis Salih) *** 001
WAJIBCIN TSAYUWA A KAN LITTAFIN ALLAH DA SUNNAR ANNABI (S.A.W.).
Musulunci addini ne saukakke daga Allah wanda ya zo ta hannun ManzonSa, Annabi Muhammad (S.A.W.) zuwa ga mutane da Aljanu baki daya. Saqon da Musulunci ke dauke da shi na bauta wa Allah Shi kadai da gudanar da dukkan rayuwa kan umarni da haninsa, na qunshe ne a cikin littafin Allah, wato Alqurani tare da qarin bayani da misalai na zahiri daga Manzon tsira kuma Annabin qarshe Muhammad (S.A.W.). Wadannan kafofi guda biyu na littafin Allah da rayuwar ManzonSa (wanda ya hada da maganganunsa da ayyukansa da amincewarsa da kuma hanninsa, su ne jagoran Musulmi. Da su Musulmi ke dogara wajen gabatar da kowane irin aiki da zai zama karbabbe komai qanqanta ko girman aikin.
Fahimtar Alkurani da Sunnar Annabi (S.A.W.) ba za su inganta ba sai an gina su a kan fahimtar magabata wadanda suka rayu da Annabi (S.A.W.) cikin Musulunci (sahabai) da wadanda suka biyo bayansu.
Tsayuwa a kan tafarkin Alqurani, da Sunnar Manzo Allah (S.A.W.) wajibi ne cikin umarnin da Allah madaukakin Sarki Ya Yi ga bayinsa. Wannan umarni ya fara aiki a kan Manzon Allah (S.A.W.) ne, sannan ya mamaye dukkan abin halitta musamman ma mutane da aljanu. Allah (S.W.A.) ya ce wa ManzonSa a cikin Alqur’ani: “Ka bi abin da aka yi wahayi zuwa gareka daga Ubangijinka, babu abin bautawa face shi, kuma ka bijire wa masu shirka.” (An’am:106).
Hakan nan kuma a wata ayar Allah (S.W.A.) Ya sake Yi wa Annabinsa makamancin wannan umarni, a inda Yake cewa: “Sannan mun sa ka a kan wata Shariah na (daga) alamarin (Addini), sai ka bi ta, kuma kada ka bi son zuciyoyin wadanda ba su sani ba.” (Jathiya: 18).

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories