KIRA ZUWA GA TAFARKIN MAGABATA NA QWARAI (Manhajus Salafis Salih) *** 007 TAFARKIN MAGABATA NA QWARAI(Aliyu Said Gamawa)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Manhajus Salafis Salih (Tafarkin Magabata na qwarai), hanya ce guda daya miqaqqiya wadda babu karkata a cikinta. Ita ce kuma hanyar da Annabi (S.A.W.) da sahabbansa suka rayu a kanta, ya kuma tabbatar da cewa duk wani abin da ya saba wa wannan tafarki dole a yi watsi da shi.
An karbo wani Hadisi daga Abdullahi Ibn Masud cewa wata rana Annabi (S.A.W.) ya zana musu wani babban layi miqaqqe, sannan ya ja qananan layuka a dama da hagun wannan layi. Sai ya ce wa sahabbansa: “wannan layi da ke miqe shi ne tafarkina, sauran qananan layuka kuwa duk a kan kowannensu akwai wani shaidani yana kiran mutane zuwa ga halaka.” Daga nan sai ya karanta ayar da ke cikin Suratul An-ami cewa: “Kuma lallai wannan ne tafarkina madaidaici don haka ku bi shi, kuma kada ku bi wasu hanyoyi sai su rarraba ku daga hanyata. Wannan ne Allah ya yi muku wasiyya da shi ko kwa yi taqawa.” (An’am:153).
Sannan akwai Hadisi wanda aka karbo daga Abu Musa Al-ashari cewa Manzon Allah (S.A.W.) yana cewa: “Taurari alamomi ne masu jagora a sararin samaniya, idan suka gushe sai abin da zai biyo baya. Ni kuma jagora ne ga Sahabbai don haka idan na gushe abin da zai biyo baya sai ya biyo baya. Haka kuma Sahabbai na jagora ne ga sauran alummar Musulmi baki daya, don haka idan sun gushe to abin da zai biyo baya sai ya biyo baya.” (Imam Muslim).
Abin fahimta a nan shi ne cewa magabatan farko (Salafus Salihu) suna qarqashin jagorancin Manzo Allah (S.A.W.), su kuma wadanda suka biyo bayansu na riqo da tafarkin Sahabban, wanda shi ne tafarkin Manzon Allah (S.A.W.). Idan kuwa aka bari koyarwarsa ta gushe, to lallai abin da zai biyo baya shi ne tozartar Addini. Allah ya kiyashe mu.
Babu wanda ya kai magabata na qwarai cikin Musulunci lazimtar Alqurani ta hanyar kiyaye shi da tilawar sa da tafsirin sa. Haka ma hadisan Manzon Allah (S.A.W.) wajen sanin su da fahimtar ma’ana da iya tantancewa don fito da ingantaccen zance daga qirqirarrun alamura tare kuma da bin ilimin masu aiki na qwarai. Wannan ya nuna cewa saqon Musulunci bayyanannie ne tun zamanin magabata, babu wani abu da ke cikin duhu wanda bai fito fili ba. Annabi (S.A.W.) yana cewa: “Na bar muku tafarki bayyananne wanda darensa ke daidai da ranarsa, babu mai gocewa daga wannan tafarki sai halakakke.” (Imam Ahmad ne ya ruwaito Hadisin).
Saboda haka ba su rarraba ilimi zuwa boyayye da bayyananne ba. Babu wani ilimi da ke boye ko aka kebe shi ga wasu mutane na musamman. Ya zo cikin Fathul Bari cewa Khalifa Umar bin Abdul-Azeez ya rubuta wasiqa zuwa ga Muhammad Ibn Abi Hazm yana ce ma sa, Ba za a rushe ilimi ba har sai an mayar da shi wani abu boyayye.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories