SAHIHIYAR AQIDA ITA CE JIGO CIKIN ADDINI:(Sheikh Aliyu Said Gamawa)

Allah mai girma da daukaka ya aiko
dukkan Manzanni don isar da sakon
sa ga bayinsa zamani bayan zamani,
kuma dukkan su farkon kiransu yana
farawa ne kan TAUHIDI, wato a
kadaita Allah shi kadai cikin halitta da
sunaye da bauta.
Hakika dacewa da samun sahihiyar
aqida babbar ni’imace, kuma baiwace
mai girma. zama cikin kazamtar shirka
da kafirci sune tabewa da halaka
duniya da lahira.
‘Yan uwa na maza da mata lallai mu
nisanci bin dukkan hanyoyin da zasu
kaimu ga rushewar imani, da barin
sahihiyar hanya ta Tauhidi.
Mu nisanci hada Allah da wani cikin
bauta ta hanyar bautar gumaka, ko
kiransa da sunayen da ba nasa ba, ko
yi masa shirka cikin abinda ya halitta,
ko kafircewa ta hanyar cewa Allah
yana da ‘da, ko imani da wani
kulumboto, ko rantsuwa da wani
baicin Allah, da kiran wani ba Allah ba
cikin makabartu, ko yayin addu’a, ko
ambaton wanin Allah in za’a yi yanka,
da halaka ta hanyar fadawa layin
sihiri, bokanci da sauran aiyukan
shirka iri iri na neman taimako, ko
agaji daga wanin Allah, ko rokon ruwa
ko arziki ko haifuwa daga wani ba
Allah ba.
Mu ji tsoron Allah ya bayin Allah, mu
sani Allah yana yafe dukkan zunubbai
amma banda shirka, kuma har Annabi
(saw) ance masa.. in da za kai shirka,
da sai mu bata aiyukan ka… Tsarki ya
tabbata ga Allah wanda yayi halitta
shi kadai, kuma shi ake bautawa shi
kadai ta da ya aiko Annabin mu
Muhammad (saw), kuma gareshi
muka dogara, kuma gareshi muke
rokon komi da neman kowanni agaji
da taimako. Hakika sunayen sa
madaukaka ne, masu kyau da tsaki
kuma lahani baya shiga cikin su daga
muminin bawa.
Allah muke roko ya yi dadin tsira da
aminci ga annabi (saw).

KOWA YA SHUKA ALHERI ZAI GA ALHERI(Sheikh Aliyu Said Gamawa)

Alheri danko ne baya faduwa kasa
banza, yana da kyau kowa ya
natsu tsam yaga shin a rayuwata
wani alheri na taba shukawa don
kaina da iyalaina da sauran jama’a
masu zuwa bayana?
Akwai hanyoyi da yawa da alherin
ka zai kai har ga wanin ka tun
kana raye da bayan ka koma ga
Allah, kai har ma sauran dabbobi,
kwari, tsuntsaye da sauran halittun
Allah da ke rayuwa a doron kasa.
Ina bamu shawara mu yi tanadin
samar da itatuwan dashe don mu
dawo da bishiyoyi a gidajen mu,
garuruwan mu, da dazuzzukan mu.
Anan kowa nada damar bada
gudumawa a nasa matakin ta
dayan hanyoyi hudu:
1. Kati tanadi na musamman na
dan itace, ka dasa ka reneshi a
hankali in ya girma aje a dasa.
2. Ka sayi adadi mai yawa na
bishiyoyi ka rabawa al’umma su
dasa, ko aje gonaki da cikin daji a
dasa cikin damana.
3. A yi amfani da duk wata dama
ta shugabanci a samar da irin
itatuwan dasawa a rabawa
al’umma, kuma a dasa a duk inda
ya dace don raya al’ummar mu.
4. Kayi tanadin irin bishiyoyi daban
danab kaje ka watsa a cikin daji da
fatan a hankali ruwan damana zai
fitar dasu har su girma.
Hakika kyautatuwar muhalli na
daga cikin hanyoyin samun rayuwa
mai dadi cikin ni’imar dausayi da
samun albarkatun kasa da kare
kwararowar hamada da rage saurin
kafewar mashayar dabbobi a daji.
Pls yana da kyau mu dauki
matakin bai daya na dasa bishiyoyi
a gidaje da gonakin mu, sannan
hukumomi su taimaka mana wajen
samar da isassun irin bishiyoyi a
dasa mana su a dazuzzukan mu da
muhallan mu.
Tabbas akwai alheri mai yawa cikin
samar da jerin bishiyoyi a kusa da
jama’a, da bakin manyan titunan
mu, da kusa da manyan rafuka, da
gabar koguna da cikin tabkunan
mu don su taimaka wajen dadewar
ruwan bai kafe ba a daji don
amfanin mu da dabbobin mu.
‘Yan uwa munyi sakaci fa, kuma
muna yiwa kan mu illa ta hanyar
sare bishiyoyi ba dasawa, muna
karya dokar hukuma, kuma muna
kusanto da hamada zuwa muhallan
mu da kan mu, yanzu fa duk
dazuzzukan mu sun zama fayau
kamar tsakiyar gari, har namun daji
da dabbobin mu sun shiga wahalar
rayuwa na rashin abinci da abin
sha, ‘yan uwan mu mazauna daji
da masu sana’ar kiwo, da ‘yan
farauta, da masu suu na kifi, da
masana masu nemo magani daga
itatuwa duk mun durkusar da su
sun koma laluben yadda zasu dora
targaden da rashin bishiyoyi da
bushewar daji yayi mana.
Tarihi ya nuna cewa iyayen mu a
can baya sun mana tanadin alheri
wajen dasa bishiyoyi a gida da daji
don amfanin mu masu zuwa bayan
su, sai yau gashi mu kuma mun
sare shukan da sukayi mana,
dazukan sun bushe karaf tun akan
idon mu, to yaya na bayan mu
masu zuwa, pls wani tanadi muka
yi musu?? Ina fatan mu yiwa kan
fada, mu dawo da dabi’ar samarwa
kan mu da dazukan mu isassun
bishiyoyi.
Mu sani fa duk wanda ya dasa
bishiya kuma yayi mata hidimar
kulawa da bayin ruwa to tabbas
yana da ladan rayuwar ta, da ladan
wanda yasha inuwa, ko yaci ‘ya
‘yan ituwan ta, ko aka amfana da
iccen wajen magani ko duk abinda
ya dace. Dasa bishiya sadakace
mai gudana da zaka na samun
lada tun kana raye da bayan ka
koma ga Allah. Dan uwa da za’a
baka zabin aiki na karshe a
rayuwar ka yana da kyau ka zabi a
baka dama ka dasa bishiya don
yawan ladan wannan aiki.
Yana daga hanyoyin raya al’umma
ta yau da masu zuwa bayan mu
muyiwa kanmu gata da dasa
bishiyoyi don dawo da ni’imar
dausayin kasar mu, kyautata
muhallan mu, habaka tattalin
arzikin mu da yiwa na bayan mu
tanadin alheri. Allah ya bada iko,
amin

KIRA ZUWA GA TAFARKIN MAGABATA NA KWARAI (Manhajus Salafis Salih) *** 36(Sheikh Aliyu Said Gamawa)

HANYOYIN KYAUTATA WA’AZI
DA YADDA AKE FUSKANTAR DA
SABANI TSAKANIN MALAMAI
Daga: Dr Muhammad Babangida
Muhammad
Al’ummar Musulunci ta kafu ne a
kan harsashin wa’azi. Wa’azi ne
ya haifar da ita, wa’azi ne yake
tafiyar da rayuwarta kuma wa’azi
ne yake fuskantar da alaqarta da
sauran al’ummomi. Manzon
Allah (S.A.W.) ya isar da saqon
Allah ta hanyar gargadi da
wa’azi. Wadanda suka saurari
wa’azinsa suka yi imani da shi su
ne, “Musulmi.” Wadanda suka qi
sauraron sa, suka yi girman kai,
suka qi yin imani da shi su ne
kafirai. Makomar wadancan
aljanna, su kuma wadannan
makomarsu wuta.
Al’ummar Musulmi ta ginu a kan
imani da Allah da ManzonSa tare
da zamantakewa cikin ruhin
soyayyar juna da ’yan’uwantaka
da hadin kai da taimakon juna a
kan ayyukan alheri. Martabar
Musulmi da qarfinsu da
halifancinsu a bayan qasa sun
ta’allaqa da yadda suka riqi
wa’azi da kuma dangantakarsu
da juna.
Kyautata yin wa’azi da samar da
hadin kai da kiyaye ladubban
sabani tsakanin Musulmi suna
daga cikin mafi muhimman
buqatu na kowace al’umma
Musulma. Haqiqa a kowane
zamani al’ummar Musulmi suna
buqatar wa’azi don a mayar da
hankulansu zuwa ga
mahaliccinsu da dalilin halittar
su. Mutane suna buqatar wa’azi
don inganta ibadarsu da
rayuwarsu da kyautata
mu’amalarsu da juna.
Abin takaici ne cewa sabani da
husuma tsakanin Musulmi sun
fadada kuma sun yi muni mai
tsanani, abin da ke jawo koma
baya da yawa a cikin al’amuran
addinin Musulunci a halin da
muke ciki yanzu. Ya dace mu yi
tsokaci a kan wadannan
matsaloli domin samar da
mafita mafi dacewa.
Yana da kyau mu dubi
muhimmancin wa’azi da
qalubalen da ke fuskantar wa’azi
da masu wa’azi a yau da
qa’idojin da suka wajaba masu
wa’azi su lura da su domin
samar da mafi kyan tasiri a cikin
al’umma. Haka kuma yana da
kyau mu fayyace bayani a kan
sabani da dalilansa da
nau’ukansa da ladubban sabani
tsakanin malamai.

KIRA ZUWA GA TAFARKIN MAGABATA NA KWARAI (Manhajus Salafis Salih) *** 35(Sheikh Aliyu Said Gamawa)

KARANTARWAR SHEHU USMAN
DAN FODIYO A KAN BIN
SUNNAH (2)
Ci gaba …
4. An yi tambaya, shin ko ya
halatta ga wanda ya riga ya
kama wata mazhaba
ayyananniya ya fita daga gare ta?
A wajen jawabi an ce, “Na’am,”
zai iya fita yanke. Rafi’i shi ne ya
inganta wannan ra’ayi. Ko da
yake wani qaulin an ce ba zai iya
fita yanke ba, domin ya riga ya
daure kansa. A qauli na uku
kuwa aka ce bai halatta ya fita da
wadansu mas’alolin mazhaba ba,
sannan ya ci gaba da riqo da
wasu mas’alolin.
5. Duk Mujtahidi da ya sava wa
nassin Alqur’ani da Hadisi ko
Ijma’i, ba za a bi shi ga wannan
magana ba.
6. Duk abin da almajiran
mujtahidi suka fahimta daga
maganar mujtahidin nan ba za a
lissafa da shi ba a cikin
mazhabarsa. Amma daga baya,
sakacin mutane ya yi yawa har
suka riqa jingina ra’ayoyin masu
wallafar littafi da masu yi wa
littafi sharhi ga mazhabar
wadanda suke koyi da shi, suka
mai da su kamar ra’ayoyin
mujtahidin nan na asali. Sai daga
qarshe al’amari ya koma ga su
almajiran suna koyi da ratayawa
da junansu. Ta haka har ya zama
kowane littafi ya kai Juz’i ashirin,
alhali kuwa ainihin maganar
mujtahidin a cikinsa idan an tara
ba za ta kai Juz’i daya ba.
Wajibi ne a kan kowane Musulmi
mukallafi ya qudurta cewa
dukkan Imaman Musulmi a kan
shiriya ta Ubangijinsu su ke.
(Wato ba sa cikin bata). Wato su
Imamu Abu Hanifa, Maliki,
Shafi’i da Imamu Ahmad bin
Hambal.
8. Wajibi ne a kan kowane
Musulmi Mukallafi kada ya yi
qyamar aiki da maganganunsu
(Mujtahidan). Wadansu mutane
a yau sun kasance idan waninsu
ya yi amfani da maganar da ba
ta Imaminsa ba, sai ya ce, “Bari
in yi koyi da shi don larura.”
Watau ya yi aiki da hukuncin a
kan hukuncin larura wadda take
halartar da abin da aka hana. Sai
ya ga kamar dai ya afka ne a
cikin zunubi. To ya sani cewa
wannan aiki nasa da ya yi na
qyamar hukuncin Mujtahidin
nan, shi ne babban zunubi
wanda ya wajaba ya tuba saboda
aikata shi, kuma ya nemi gafara
a wurin Allah. Domin da su irin
wadannan mutane sun yar da
cewa dukkan Imaman
Musuluunci a kan shiriya su ke,
da ba su yi qyamar aiki da
magabatansu ba, domin shiriya
ba a qyamar ta matuqar dai an
tabbata ita ce.
9. Duk wanda ya bar aikin da aka
yi sabani a kan zamowarsa
wajibi, ko kuwa ya aikata abin da
aka yi sabani a kan zamowarsa
haram, to ba za a yi masa inkari
ba, idan har ya dogara da qaulin
malami. Sai fa idan ya dogara ga
maganganunsa wadanda suka
saba wa nassin Alqur’ani da
Sunnah ko Ijma’i. Amma
matuqar aikinsa ya yi daidai da
wata maganar Mujtahidi na
Alhalus-Sunnah, to ba za a yi
masa musu ba. Amma da a ce
an yi musu shi ne a ce abin da
wannan mutum ya yi haram ne.
Amma da a ce an yi musu ne da
nufin shiryarwa ko don yi masa
nasiha, to shi wannan ba za a
kira shi inkari ba. Amma a wajen
babin fatawa, malamin da ke yi
wa mutane fatawa da wani qauli
manisanci ga hankali, ko kuma
mai raunin hujja, ya bar
mashahuriyar magana mai
qarfin hujja, to za a iya yi masa
inkari domin bai halatta a yi
fatawa ba sai da mashahuriyar
magana mai qarfi.
10. Mutum wanda za a yi wa
inkari na hukunci, shi ne wanda
ya sava wa nassin Alqur’ani da
Sunnah ko na Ijma’i.
Wannan bayani na Shehu
Usmanu dan Fodiyo ya nuna
mana irin tsarin karantarwar
Shehun Malamin. Sannan za mu
fahimci cewa riqo da mazhaba
guda daya ba tilas ba ne cikin
addinin Islama. Haka kuma riqo
da mazhabar ba laifi ba ne, sai
dai in ka yi watsi da maganar
Manzon Allah (S.A.W.)
ingantacciya don riqo ko bin
jagoran mazhabar, to a nan kam
an kauce wa karantarwar Annabi
(S.A.W.) da Sahabbai da sauran
magabata na qwarai har da shi
jagoran Mazhabar da kake bi
din. Domin dukkansu sun ce in
an ga Hadisi ingantacce ya sana
da fatawa ko karantarwarsu to a
ajiye maganarsu a dauki ta
Manzon Allah (S.A.W.) ita ta fi
daidai (Wallahu A’alamu).

KIRA ZUWA GA TAFARKIN MAGABATA NA KWARAI (Manhajus Salafis Salih) *** 34(Sheikh Aliyu Said Gamawa)

KARANTARWAR SHEHU USMAN
DAN FODIYO A KAN BIN SUNNAH
(1)
Kamar yadda magabatan farko da
manyan malaman Sunnah suka
daidaita wajen tsayuwa a kan
tafarkin Manzon Allah (S.A.W.),
haka suka dage wajen isar da
wannan saqo. A cikin wadannan
magabata akwai Mujjadadi Sheikh
Usman dan Fodiyo wanda ya yi wa
Sunnar Manzon Allah (S.A.W.)
hidima, ya kuma yi fada sosai da
bidi’o’i da suka mamaye al’ummar
Musulmi na zamaninsa. Ya yi
rubuce-rubuce masu yawa a
wannan fanni, cikinsu akwai wani
littafinsa mai suna “Hidayatud-dull
ub” ya kawo mas’aloli guda goma
da suka shafi riqo da Sunnar
Manzon Allah (S.A.W.) kamar
haka:
1. Sanar da Almajirai cewa duk
abin da ya zo daga Sunnar Manzon
Allah (S.A.W.) ba za a kira shi
Mazhabar kowa ba. Wajibi ne
kuma a kan kowa ne Musulmi ya yi
aiki da shi, kuma wajibi ne a karbi
kiran duk wanda ya yi kira zuwa ga
wannan abu.
2. Allah bai wajabta wa kowa ba a
cikin LittafinSa, haka kuma Manzon
Allah (S.A.W.) bai wajabta wa
kowa ba a cikin Sunnarsa, cewa
tilas ne mutum ya kama wata
mazhaba ayyananniya. Da a ce su
magabatanmu sun yi haka da kuwa
sun afkar da mutane cikin zunubi,
domin da sun hana yin aiki ke nan
da duk wani Hadisi wanda shi
Mujtahidin nan mai Mazhaba bai
same shi ba.
An yi tambaya, ko wajibi ne a kan
dukkan Mutum wanda bai kai ga
darajar zama Mujtahidi ba, ya kama
mazhaba guda ayyananniya ya
lazimce ta?
A wajen wajibi an kawo ra’ayi biyu.
Na farko an ce yana lazimta kamar
yadda marubucin littafin Jam’uj
Jawami’i ya ingantar da wannan
magana. Ra’ayi na biyu kuwa ya
ce, a’a ba ya lazimta, kuma
wannan Annawawi ya zaba.

KIRA ZUWA GA TAFARKIN MAGABATA NA KWARAI (Manhajus Salafis Salih) *** 33(Sheikh Aliyu Said Gamawa)

BANBANCIN DA KE TSAKANIN
SHUGABANNIN MAZHABOBI WAJEN
HANYOYIN DA SUKE DOGARA DA
SU (6)
MAZHABAR IMAMU ZAHIRI
Wata qila zai dace a tabo qa’idojin
mazahabar Zahiriyyawa da
ginshiqanta a taiqaice. Wannan
kuwa saboda ita mazahabar tana
daga mazahabobin Musulunci
masu tasiri, wadda har yanzu tana
da mabiya daga Ahlus-Sunnah.
Babu shakka an sami nau’o’in
sabani mafi tsanani tsakanin
Zahiriyyawa da Hanafawa, sannan
tsakaninsu da Malikawa, sannan
da Hambalawa, sannan da
Shafi’awa, kuma Imamu Dauda ya
kasance yana ba da girma mai
yawa ga Imamu Shafi’iy. Mafi
bayyanar ginshiqan mazhabar
Zahiranci su ne: riqo da zahirin
ayoyin Alqur’ani mai girma, da
nassoshin Sunnah, da gabatar da
shi a kan la’akari da ma’anoni, da
hikimomi, da maslahohi wadanda
ake jin saboda su aka shar’anta
hukunce-hukuncen. Haka kuma ba
a aiki da qiyasi a wajen ma’abota
wannan mazhaba, matuqar babu
nassi a kan wannan illar da ta sa
aka ajiye hukunci a gurbi na farko,
(wato abin da za a yi qiyasin a
kansa) sannan kuma ya tabbata
cewa akwai wannan illa a gurbi na
biyu (wato abin da za a qiyasta) ta
yadda hukuncin zai sauka a
matsayin (tabbatar da dangantaka
tsakanin gurbin hukunci na farko
da gurbi na biyu) kamar yadda ake
haramta aiki da istihsani, kuma ake
kafa hujja da ijma’in da ya tabbata
a lokacin sahabbai kawai. Haka
kuma ba a yin aiki da Hadisi
(Mursali) da (Munqadi’i), wanda
wannan ya saba da mazahabar
Malikawa da ta Hanafawa da ta
Hambalawa. Hakan nan ba a aiki
da Shari’ar wadanda suka gabace
mu, kuma ba a halattawa ga kowa
aiki da ra’ayi, saboda fadar Allah
Ta’ala:
(( ﻣﺎ ﻓﺮﻃﻨﺎ ﻓﻰ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻣﻦ ﺷﻰﺀ‏) ‏) ﺳﻮﺭﺓ
ﺍﻷﻧﻌﺎﻡ 38: .
“Ba mu rage komai ba a cikin
littafin.”
(Suratul An’am: 38).
Domin kuwa tsallake hukunci da
aka yi nassi a kansa, zuwa
waninsa, qetare iyaka ne ga
dokokin Allah. Kuma bai halatta ga
wani mutum ya tsaya a kan
mafahumin da ya saba da zahirin
nassi ba.
Taqalidi (kwaikwayo) kuwa,
haramun ne ga amiy (gama garin
Musulmi) kamar yadda yake
haramun a malami, saboda haka
wajibi ne ga kowane mukallafi ya yi
bakin abin da zai iya yi na ijtihadi.
FADAKARWA
A gaskiya da yawa daga ginshiqan
mazhabobin da aka dangana ga
shugabannin Musulunci da ake bi,
ginshiqai ne da aka fitar da su
daga maganganunsu wadanda ba
za su inganta a ce an ruwaito su
ne daga gare su ba. Saboda haka
qanqame su da dagewa wajen kare
su, da kawo ra’ayoyi na jayayya, da
amsoshi na mayar da martani, ga
wanda ya saba da shi, da
shagaltuwa da dukkan wannan, ga
barin littafin Allah da sunnar
Manzon Allah (S.A.W.), gaba
dayan wannan yana daga mafi
bayyanar abubuwan da suke haifar
da mummunan sabani. Kuma ko
kusa su shugabannin da kansu
(RA) ba su nufi wannan ba, kuma
babu shakka irin wannan ta
nisanta Musulmin da suka zo daga
baya, daga manyan al’amura, ta sa
sun shagala da abubuwa marasa
muhimmanci, har ya zamana
al’umma ta afka cikin wani
zuzzurfan rami na ci baya wanda a
yau take birgima a cikinsa. Allahu
A’alam.

KIRA ZUWA GA TAFARKIN MAGABATA NA KWARAI (Manhajus Salafis Salih) *** 32(Sheikh Aliyu Said Gamawa)

BANBANCIN DA KE TSAKANIN
SHUGABANNIN MAZHABOBI WAJEN
HANYOYIN DA SUKE DOGARA DA
SU (5)
TSARIN IMAMUAHMAD
BIN HAMBALI
Shi kuwa Imamu Ahmad Bin
Hambali qa’idojin mazhabarsa
suna da kusanci qwarai da
qa’idojin mazahabar Imamu
Shafi’iy, wanda bayaninta ya
gabata. Saboda haka yana tabbatar
da hukunci ta hanyar riqo da
wadannan ginshiqai a kan jerin da
aka rattaba kamar haka:
1. Nassoshi daga A1-Qur’ani da
Sunnah, wadanda idan ya same su
ba ya waiwayar waninsu, kuma ba
ya gabatar da wani abu da ya
danganci aikin mutanen Madina,
ko ra’ayi ko qiyasi ko maganar
Sahabi ko Ijma’i wanda ya ginu a
kan rashin sanin wanda ya saba da
shi, wato ba ya gabatar da kowane
daya daga wadannan abubuwa a
kan Hadisi sahihi marfu’i.
2. Idan bai samu nassi game da
mas’ala ba, sai ya koma ga fatawar
Sahabbai. Idan ya sami magana ta
wani Sahabi wadda ba a san wani
Sahabi da ya saba kan maganarsa
ba, to ba zai tsallake zuwa ga wani
abu dabam ba, ba kuma zai
gabatar da wani aiki ko ra’ayi ko
qiyasi a kan wannan magana ba.
3. Idan Sahabbai suka yi sabani,
sai ya dubi maganar tasu ya zabi
wadda ta fi kusa da A1-Qur’ani da
Sunnah, kuma ba zai fita daga
maganganun nasu ba. Idan kuma
bai gano wata magana da ta fi
kusa da A1-Qur’ani da Sunnah ba,
sai ya hikaito sabanin nasu amma
ba zai nuna maganar da ya zaba a
kan ta sauran ba.
4 Hadisi mursali da Hadisi mai
rauni wanda ake iya magance
raunin nasa don bai sami wata
madogara ba a wannan babi banda
shi, ko kuma wani da shi, kuma
yana gabatar da irin wannan Hadisi
a kan qiyasi.
5. Qiyasi wanda a wajen Imamu
Ahmad din dalili ne na larura da
ake komawa gare shi a lokacin da
ya rasa daya daga hujjoji da suka
gabata.
6. Toshe kafar barna. (saddud
zara’i’i)

KIRA ZUWA GA TAFARKIN MAGABATA NA KWARAI (Manhajus Salafis Salih) *** 31(Sheikh Aliyu Said Gamawa)

BANBANCIN DA KE TSAKANIN
SHUGABANNIN MAZHABOBI WAJEN
HANYOYIN DA SUKE DOGARA DA
SU (4)
3. MAZHABAR IMAMUS-SHAFI’I
Qa’idoji da ginshiqan mazhabar
Imamus-Shafi’i (R.A.) su ne abin
da ya tattara cikin littafinsa na
“Usulul Fiqhi” mai suna (Ar-risala)
wanda ake ganin shi ne farkon
littafin Usulul Fiqhi mai gamewa da
aka wallafa a Musulinci.
Al- Imamus-Shafi’i (R.A.) ya ce:
Tushen Shari’ar Musulunci shi ne
Qur’ani da Sunnah, idan ba a sami
nassi a cikinsu ba, sai a yi qiyasi a
kansu. Idan kuma salsalar Hadisin
da aka ruwaito daga Manzon Allah
(S.A.W.) ta sadu da shi, kuma ta
inganta, to wannan shi ne matuqa.
Ijma’i kuma ya fi gauron Hadisi.
Haka kuma ana daukar Hadisi ne a
kan zahirin lafazinsa, idan kuma
yaqunshi ma’anoni fiye da daya, to
ma’anar da ta fi kusa da zahirin ita
ta fi cancanta a fahimce shi da ita.
Idan kuma Hadisai suka yi kafada
da kafada da juna, to Hadisi mai
salsalar da ta fi inganci shi ne
mafificinsu, Hadisi Munqadi’i
kuwa, ba a bakin komai ya ke ba,
idan ba daga Ibnul Musayyib ya ke
ba. Hadisi “Munqadi’i” shi ne
wanda maruwaici daya ya saraya
daga salsalarsa, amma da
sharadin kada mai sarayar ya zama
Sahabi ne shi. Kuma ba a qiyasce
Shari’a kan wani tushen da ba
nata ba, kuma ba a cewa da
tushen Shari’a ta qaqa ko saboda
me? Sai dai ana iya cewa don me
ga reshen Shari’a kawai. Idan
kuma qiyasin reshen ya inganta a
kan asali, ya zama ingantacce ke
nan, kuma za a iya kafa hujja da
shi. Saboda haka Imamu Shafi’i
yana bayanin cewa Qur’ani da
Sunnah duk matsayinsu daya ne,
dangane da shar’antarwa. Babu
wani sharadi da ake shardanta wa
Hadisi banda inganci, da saduwa
da tushensa, domin shi ma asali
ne na Shari’a, shi kuwa asali ba a
ce masa saboda me, ko ta qaqa?
Haka kuma ba a shardanta wa
Hadisi ya zama mashahuri idan ya
zo cikin abin da yake da wahala a
kauce masa (kamar yadda Imamu
Abu Hanifa ya sharxanta), amma
bai shardanta rashin savawar
Hadisi da aikin mutanen Madina
ba, (kamar yadda Imamu Malik ya
shardanta), sai dai bai yarda da
wani Hadisi daga Hadisan
“Misalai” ba, in banda na Sa’idu
Ibnul Musayyib, domin nasa suna
da hanyoyin da suka dangana su
ga tushe a wajensa. A nan Imamu
Shafi’i ya saba da Maliku da
Sauriy da sauran tsarakunsa (daga
malaman Hadisi) wadanda suke
kafa hujja da irin wadannan
Hadisai. Haka kuma bai amince da
kafa hujja da “Istihsani” ba, a
wanda a nan ma ya saba da
Malikawa da da Hanafawa gaba
dayansu. Har ma ya rubuta
littafinsa game da rashin amincewa
da Istihsani mai suna “Ibdalul
istihsan,” sannan ya fadi maganar
nan tasa mashahuriya inda ya ce,
“Wanda duk ya aiwatar da
istihsani, to ya shar’anta hukunci.
Kamar yadda ya qi karbar
Masalihul-mursala, ya qi amincewa
da kafa hujja da ita. Haka kuma ya
qi amincewa da kafa hujja da
qiyasin da bai kafu a kan wani
ingantaccen dalili mabayyani ba.
Haka kuma ya qi amincewa da kafa
hujja da aikin mutanen Madina,
kamar yadda ya kasance yana
ganin kuskuren Hanafawa game da
barin su ga aiki da Hadisai masu
yawa saboda rashin cika sharudan
da suka gindaya a kansu wajen
aikin Hadisan, kamar shuhura, da
makamancinta. Haka kuma bai
taqaita ba, (kamar yadda Malik ya
taqaita) wajen riqo da Hadisan
mutanen Hijaz su kadai.
Wadannan su ne ginshiqan
Mazhabar Imamu Shafi’i mafiya
muhimmanci kuma mafiya fice a
jimlance wadanda ana iya ganin
sabani tsakaninsu da ginshiqan
mazhabar Hanafawa da Malikawa a
fili.

KIRA ZUWA GA TAFARKIN MAGABATA NA KWARAI (Manhajus Salafis Salih) *** (30)(Sheikh Aliyu Said Gamawa)

BAMBANCIN DA KE TSAKANIN
SHUGABANNIN MAZHABOBI WAJEN
HANYOYIN DA SUKE DOGARO DA
SU (3).
MAZHABAR IMAMU MALIK
Shi kuwa Imamu Malik (R.A.),
tsarinsa ya bambanta, don shi ya
kasance yana cewa, “Yanzu duk
lokacin da wani mutum gwanin
jayayya ya zo mana, sai mu bar
abin da Jibrilu ya saukar da shi ga
Muhammad (S.A.W.), saboda iya
jayayyarsa? Kuma da ma a baya
mun ga cewa mazhabarsa ita ce
mazhabar mutanen Hijaz, wato
’yan makarantar Imamu Sa’id Ibnul
Musayyib (RA). Don haka ana iya
taqaice ginshiqan mazhabar Malik
kamar haka:
Game da nassin Qur’ani mai girma.
Sannan riqo da zahirin nassinsa
wanda shi ne “Umumi.”
Riqo da dalilin nassinsa wanda shi
ne “Mafhumil muhalafa.” Ma’anar
wannan shi ne rashin la’akari da
gundarin abin da nassi ya nuna
saboda dalili na wani nassin mai
gamewa, da ya fi shi qarfi, misali
Hadisi ya ce: cikin dabbobi
sakakku akwai zakka wanda ya
nuna babu zakka cikin dabbobi
tirkakku, amma ba za a yi la’akari
da wannan fahimtar ba, saboda
fadar Allah Ta’ala ka karbi sadaka
(Zakka) daga dukiyoyinsu.”
Sannan riqo da mafahumin nassi
(gundarin abin da nassin ya nuna
wanda ake kira “mafahumil
mukhalafa”) wato fahimtar da ta yi
daidai da lafazin nassi.
Sannan riqo da fadakarwarsa, wato
fadakarwa game da illar da ta sa
aka saukar da hukuncin, kamar
fadar Allah Ta’ala, “Domin lallai shi
qazanta ne, ko kuma fasiqanci ne.”
To wadannan ginshiqai ne guda
biyar kuma a Sunnah ma akwai
biyar kamarsu, wanda idan aka
hada su sun zama goma ke nan.
Sai kuma riqo da Ijma’i.
Qiyasi.
Aikin mutanen Madina.
Hukunci don toshe kafar barna.
Aiki da maslaha.
Sannan aiki da maganar Sahabi
(idan salsalar da aka samo
maganar ta hanyar da ta inganta
ne, kuma Sahabin yana daga
fitattu).
La’akari da savani (idan Hujjar mai
sabanin tana da qarfi).
Sannan Istishabi.
Sannan Shari’ar wadanda suka
gabace mu.

KIRA ZUWA GA TAFARKIN MAGABATA NA KWARAI (Manhajus Salafis Salih) *** (29)( Sheikh Aliyu Said Gamawa)

BAMBANCIN DA KE TSAKANIN
SHUGABANNIN MAZHABOBI WAJEN
HANYOYIN DA SUKE DOGARO DA
SU (2)
MAZHABAR IMAMU ABU HANIFA:
Imamu Abu Hanifa ya wanzu a
matsayin misali na hanyar fitar da
hukunce-hukunce, wanda ya saba
da hanyoyin shugabannin
mazhabobi guda uku. Saboda haka
qa’idojin mazhabarsa kamar yadda
shi da kansa ya bayyana, sun
taqaita ne cikin fadarsa, “Ni ina yin
riqo ne (watau tabbatar da
hukunci) da littafin Allah, idan
kuma ban sami nassi a cikinsa ba
sai na dauka daga Sunnar Manzon
Allah (S.A.W.) da maganganun
Sahabbai masu inganci, wadanda
suka yadu a hannun amintattu.
Idan kuma ban sami nassi a littafin
Allah da Sunnar ManzonSa ba, sai
na dauki maganar Sahabbansa,
kuma ina daukar maganar wanda
na so daga nan ba zan saki
maganarsu ba, na kama ta
waninsu. Idan kuma lamarin ya ci
tura zuwa Ibrahimu, da Sha’abi, da
Ibnul Musayyib, (ya lissafa
wadansu mazaje), sai ni ma na yi
Ijtihadi kamar yadda suka yi.”
Wadannan su ne manyan ginshiqai
na mazhabar Abu Hanifa. Akwai
kuma wadansu ginshiqai na reshe
masu daraja ta biyu, wadanda suka
haihu daga wadannan, ko kuma
suke komawa garesu. To daga irin
wadannan ginshiqai ne na reshe
sabani yake bayyana, kamar
fadarsu, tabbacin nunin lafazi mai
gamewa dai dai yake da lafazi
kebantacce, da fadarsu mazhabar
Sahabi a kan Sahabi “Umumi” abu
ne da yake kebance wannan
“Umumin da fadarsu, “Yawan
maruwaita ba ya fa’idantar da
rinjaye,” da fadarsu, “Rashin
la’akari da mafahumin sharadi da
sifa da na rashin karbar Hadisin
mutum daga cikin abin da yake da
wahala a kauce masa da cewa
umarni yana tabbatar da wajibci ne
matuqar ba a sami abin da zai
kawar da wajibcin ba.” Idan
maruwaicin Hadisi kuma masanin
fiqihu ya aikata abin da ya saba da
ruwayarsa, to za a yi aiki ne da
abin da ya aikata, ba da abin da ya
rawaito ba.” Wato a gabatar da
qiyasi “Jaliyyi” (bayyananne) a kan
Hadisin mutum daya, da ya yi karo
da shi; ko riqo da “Istihsani” da
barin qiyasi a lokacin da buqatar
hakan ta bayyana. Saboda haka ne
suka samo daga fadar Imamu Abu
Hanifa, “Mun san cewa wannan
ra’ayi ne kuma shi ne mafi kyawun
abin da muka sami ikon wanzarwa,
idan kuwa wani ya zo mana da
abin da ya fi shi, sai mu karba.”

KIRA ZUWA GA TAFARKIN MAGABATA NA KWARAI (Manhajus Salafis Salih) *** 28(Sheikh Aliyu Said Gamawa)

BAMBANCIN DA KE TSAKANIN
SHUGABANNIN MAZHABOBI WAJEN
HANYOYIN DA SUKE DOGARO DA
SU (2)
Daga: Dr. Taha Jabir Alwani
(Cikin Littafin Adabul Ikhtilaf Fil
Islam)
Ana daukar shugabannin
mazhabobi uku, Malik da Shafi’i da
Ahmad a matsayin masana Hadisi
da maganganun Sahabbai, kuma
su ne wadanda suka karanci
fiqihun mutanen Madina, suka riqe
iliminsu. Shi kuwa Imam Abu
Hanifa magajin fiqihun ma’abota
ra’ayi ne, kuma shugaban
makarantarsu a zamaninsa.
Haka kuma savanin da ya kasance
tsakanin makarantar “Sa’idu Ibnul
Musayyib” wanda ta ginu a kan
fiqihun Sahabbai, da Hadisan da
aka dangana musu, kuma
Malikawa da Shafi’awa da
Hanbalawa suka tafi a kan tsarinta,
da makarantar “Ibrahim
Annakha’iy” wanda ta dogara a kan
aiwatar da ra’ayi a halin da aka
rasa Hasidi. Ya zama babu
makawa irin wannan sabani ya ciru
zuwa ga dukkan wanda ya yi riqo
da daya daga hanyoyin makarantu
guda biyu, wajen tabbatar da
hukunce-hukuncen shari’a. Kuma
babu wanda yake musa cewa
wannan sabani ya dakushe
matuqa, a daidai wannan mataki.
Domin bayan halifanci ya bar
hannun Umamiyawa, ya koma
hannun Abbasawa, Abbasawa sun
dauko wadansu daga manyan
malaman Hijaz zuwa Iraqi, don
yada Sunnah a can. Daga cikin
wadanan malamai akwai Rabi’atu
Ibn Abi-Abdurrahman, da Yahaya
Bin Sa’id da Hisham Ibn Urwah da
Muhammad Ibn Ishaq, da
sauransu, kamar yadda wasu daga
Iraqawa suka tashi zuwa Madina,
suka yi karatu a wajen malamanta,
kamar su Abu Yusuf Yaqub Ibn
Ibrahim da Muhammad Ibnu
Hassan wadanda suka yi karatu a
wajen Maliku, kamar yadda da
yawa daga ra’ayoyin Iraqawa da
ire-iren tunaninsu suka ciru zuwa
Hijaz, haka ma tunanin Hijazawa
ya tashi zuwa Iraq. Amma duk da
haka sai mu tarar da shugabannin
mazhabobi uku, wato Malik da
Shafi’i da Ahmad, suna gina tsarin
tabbatar da hukunci kusan iri daya
a tsakaninsu, ko da kuwa sun sava
a cikin wani tsari na fitar da
hukunci da hanyoyinsa, a yayin da
Imamu Abu Hanifa ya sha bamban
da su cikin tsarinsa.

KIRA ZUWA GA TAFARKIN MAGABATA NA KWARAI (Manhajus Salafis Salih) *** 27(Sheikh

BAMBANCIN DA KE TSAKANIN
SHUGABANNIN MAZHABOBI WAJEN
HANYOYIN DA SUKE DOGARO DA
SU
Daga: Dr. Taha Jabir Alwani
(Cikin Littafin Adabul Ikhtilaf Fil
Islam)
Mazhabobin fiqihu, da suka
bayyana bayan zamanin Sahabbai,
da Tabi’ai kamar yadda wadansu
suke gani, su goma sha uku ne,
kuma gaba dayan ma’abota
wadannan mazhabobi, ana
dangana su ne ga mazhabar
Ahlus-Sunnah wadda ita ce
mazhabar da mafi yawan Musulmi
suke bi. Sai dai daga wadannan
mazhabobi babu wadanda suka
sami gatan a adana su a rubuce,
sai fiqihun guda takwas ko tara
daga wadannan shugabanni. Haka
kuma an sami rata cikin yawan
abin da aka rubuta daga fiqihun
nasu, sai ya zamana wadansu na
rubuta fiqihunsu gaba daya,
wadansu kuma aka taqaita a kan
wani bangare na fiqihun nasu, to
daga abin da aka rubuta na fiqihun
kowane bangare daga wadannan,
aka fahimci mazhabobinsu, daga
hanyoyin da suke bi wajen fahimtar
Shari’ar Musulunci.
Ga jerin shugabannin mazhabobi
nan kamar haka:
1. Al-Imamu Abu Sa’id Ibn Yasir
Al-basari.
2. Al-Imamu Abu Hanifa An-
Nu’umanu Ibn Sabit Ibn Zaidi.
3. Al-Imamu Auza’iy Abu Amru
Abdurrahman Ibn Amru Ibn
Muhammad.
4. Al-Imamu Sufyan Ibn Sa’id Ibn
Masruq As-Sauriy.
5. Al-Imamu Laisu Ibn Sa’ad.
6. Al-Imamu Malik Ibn Anas Al-
Asbahani.
7. Al-Imamu Sufyan Ibn Uyaynah.
8. Al-Imamu Muhammad Ibn Idris
As-Shafi’iy.
9. Al-Imamu Ahmad Ibn
Muhammad Ibn Hambal.
Akwai kuma Imamu Dawud Ibn Ali
Al-Ashahaniy Al-Baghdadiy wanda
aka fi sani da laqabin “Zahiri”,
wanda yake dangantuwa ne ga riqo
da zahirin nassin Qur’ani da
Hadisi.
Banda wadannan da aka ambata,
akwai wadansu shugabannin
mazhabobi masu yawa, kamar su
Ishaqu Ibn Rahuyah, da Abus
Sauru Ibrahim Ibn Khalid Al-kalbi.
Akwai kuma wadansu shugabanni
wadanda ba su sami mabiya da
yawa ba, kuma mazhabobinsu ba
su yadu ba ko kuma ya zamana an
dauke su a matsayin masu koyi da
mazhabobin da suka shahara.
Wadanda kuwa mazhabobinsu
suka sami kyakkyawar kafuwa suka
wanzu har ya zuwa wannan lokaci
da muke ciki, kuma yanzu suna da
mabiya masu yawa a dukkan
qasashen Musulmi, wadanda kuma
fiqihunsu da ginshiqansu su ne
turken fahimtar addini da bayar da
fatawa a wajen mafi yawan
malamai, su ne shugabannin
mazhabobi su hudu, wato: Abu
Hanifa da Malik da Shafi’i da
Ahmad Ibn Hanbal.

KIRA ZUWA GA TAFARKIN MAGABATA NA QWARAI (Manhajus Salafis Salih). *** 026(Sheikh Aliyu Said Gamawa)

FADAKARWA
Ba ta yiwuwa a ce akwai jagoran
mazhabar da yake da sanin dukkan
Hadisin Manzon Allah (S.A.W.) ko
a ce “Imam wane” ya san komai
kuma ba ya kuskure. Tun da kuwa
hakan ba za ta yiwu ba, tilas ne ga
Musulmi na qwarai ya riqe tafarkin
magabata ta yadda ba zai qyamaci
kowane irin aikin addini da ya
inganta daga Manzon Allah
(S.A.W.) ba ko da kuwa ya saba
da mazhabar da yake bi.
Wadannan manyan malamai na
mazhaba guda hudu da wasun su
dukkansu malaman Sunnah ne,
masoyan Manzon Allah (S.A.W.)
ne, sun yi ilimi mai yawa tare da
karantarwa cikin qan-qan da kai da
tsoron Allah. Don haka, cikakken
bi da qaunar su ba ya zama laifi,
amma yayin da aka fahimci sun yi
bayanin wata mas’ala a kan
kuskure aka kuma samu Hadisi
sahihi ya saba wa fatawa ko
fahimtarsu tilas a ajiye maganarsu
a dawo zuwa ga ta Manzon Allah
(S.A.W.). Duk daraja da ilimi da
daukakar malami ba su kai Manzon
Allah (SAW) ba. Wallahu A’alamu.

KIRA ZUWA GA TAFARKIN MAGABATA NA QWARAI (Manhajus Salafis Salih). *** 025(Sheikh Aliyu Said Gamawa)

MAGANGANUN MANYAN MALAMAI
A KAN SUNNAH DA MAQALE WA
MAZHABOBI (2).
Ci gaba
Wadannan shahararrun malamai ba
su yarda da karkasa al’umma zuwa
qungiya ko mazhaba-mazhaba ba,
kamar yadda bayanansu suka
nuna. Haka kuma ba su yarda da a
yi riqo da ra’ayoyinsu cikin
makanta ba (TAQALIDANCI)
musamman a wurin da suka yi
amfani da ijtihadi. Wannan kuwa
koyi ne da sahabban manzon Allah
(S.A.W.) kamar yadda ya zo daga
Abdullahi bin Umar:
“An karbo daga Salim dan
Abdullahi dan Umar ya ce, “Na
kasance ina zaune tare da
Abdullahi dan Umar a lokacin da
wani mutum ya zo masa daga
Sham. Sai ya tambaye shi game da
hajjin tamattu’i tare da umrah.
Abdullahi dan Umar ya ce wa mai
tambaya, hakan yana da kyau. Mai
tambaya kuwa sai ya ce, amma
mahaifinka ya hana yin hakan.
Abdullahi dan Umar ya ce masa
kaitonka mene ne don mahaifina
ya hana? Bayan Manzon Allah
(S.A.W.) ya aikata haka kuma ya yi
umarni da shi? Shin da maganar
mahaifina zan yi aiki ko kuma da
umarnin Manzon Allah (S.A.W.).
Mai tambaya ya ce da maganar
Manzon Allah (S.A.W.). Sai
Abdullahi dan Umar ya ce masa, to
ka tashi ka ba ni wuri.” (Ahmad da
Tirmizi duk suka ruwaito).
Haka ma jagororin mazhabobin
nan sun yi bakin qoqarinsu wajen
tsawatarwa a kan maqale wa
ra’ayoyinsu ba tare da hujja ba.
1. A lokacin da Imam Malik dan
Anas yake jan kunnen almajiransa
da kada su tsananta wajen riqo da
abin da ke cikin maganganunsa
matuqar an samu sahihin Hadisi
da ya yi karo da abin da ke cikin
fatawarsa, sai yake cewa:
“Ni ma fa mutum ne, ina iya
kunskure kuma ina iya yin daidai.
Don haka ku yi nazari a kan
ra’ayina, duk wanda ya yi
muwafaqa da Alqur’ani da Sunnah
ku karbe shi, wanda kuwa duk bai
yi daidai da Alqur’ani da Sunnah
ba, to ku bar shi.”
(Dubi Litafin Al-Jami’ na Ibn Abdul
Barri Juzu’i na 2, shafi na 32, da
Usulul-Ahkam na Ibn Hazm, juzu’i
na 6, shafi na 149).
Ya kuma ce:
“In banda Annabi (S.A.W.), babu
wani mutum, face za a iya karba
ko barin maganarsa.”
2. Shi kuma Imam Abu Hanifa ya
ce:
“Idan aka samu ingantaccen
Hadisi, shi ne Mazhabata.”
A wani wurin kuma ya ce:
“Ba ya halatta ga wani da ya yi
riqo da maganarmu, matuqar bai
san a ina muka ciro wannan
magana ba.” A wata ruwayar kuwa
yana cewa, “Haram ne ga wanda
bai san dalilin da na jingina a
kansa ba, da ya yi fatawa da
maganata. Domin mu mutane ne
muna iya fadar magana yau
sannan mu koma ga wata gobe.”
3. Imam Shafi’i ma ya yi
maganganu ma su yawa a game
da Sunnah. A wani wuri yana
cewa:
“Idan kuka sami wani abu a cikin
littafina, wanda ya saba da Sunnar
Manzon Allah (S.A.W.) ku riqi
Sunnar Manzon Allah (S.A.W.) ku
bar abin da na fada.” (Dubi Littafin
Majmu’u na Annawawi juzu’i 1
shafi 63).
4. Daga cikin irin maganganun
Imam Ahmad dan Hambal da suke
nuni da barin ra’ayin da suka saba
da abin da Sunnah ta tabbatar
akwai:alik ko Shafi’i ko kuma
Thauriy, amma ku karbo daga
wurin da suka karbo.”
Sannan kuma ya qara da cewa:
“Ra’ayin Al-Auza’i da ra’ayoyin
Malik da ra’ayin Abu Hanifa, duk
ra’ayoyi ne kawai, kuma a wurina
duk daya ne, abin sani dai shi ne
hujja tana daga riwayar (Hadisai)
.” (Dubi Littafin Jami’ na Ibn
Abdul-Barri juzu’i na 2 shafi na
149).
Wadannan maganganu duk
malaman sun yi su ne saboda
tsame kansu daga abin da zai iya
biyowa bayansu na daukaka
maganganunsu da qanqame
ra’ayoyinsu, a maimakon yin
amfani da abin da ya dace da
tafarkin sunna da koyarwar
magabatansu. Hakan kuwa yana
da muhimmanci a gare su saboda
kasancewar wadanda suka gabace
su daga Sahabban Manzon Allah
(S.A.W.) da Tabi’ai duk babu mai
mazhaba, kuma babu wanda
mabiya Sunnar Manzon Allah
(S.A.W.) suka yiwo riqo irin na
taqalidanci da shi. Zamanin
magabatan farko al’umma a
dunqule ta ke wuri xaya qarqashin
Sunnah ta Manzon Allah (S.A.W.),
babu rarraba zuwa mazhabobi ko
kungiyoyi savanin abin da ya
bayyana a bayansu. Ga shi kuma
Imam Malik yana cewa: “Babu
wani alherin da al’ummar baya
wanda za ta zo da shi wadda
al’ummar da ta gabace ta ba ta zo
da shi ba.” Saboda haka muminan
farko, su ake dubi wajen koyi.
Masu riqon makanta ga mazhaba
suna iya jefar da Hadisi, su qi aiki
da shi ba don wani dalili ba sai
don ya saba da mazhabarsu, kai
ka ce: Shugabaninsu ko
mazhabobinsu sun fi Sunnar
Manzon Allah (S.A.W.) ko kuma
mazhaba ce ke hukunci a kan
Sunnah, bayan kuwa wajibi ne
fahimtar mazhaba ta dace da
koyarwa Sunnah. Irin wadannan
masu taqalidanci ko ta’assubanci
wani lokaci har maganganun
malaman mazhabobin nasu ma ba
sa aiki da su. Domin kuwa Imam
Shafi’i yana cewa a cikin littafinsa
mai suna Al-Risala.
“Wajen taqalidanci ne (watau riqon
makanta ga wani malami ko
mazhaba), masu gafala su ke
gafala. Allah dai ya gafarta mana
tare da su.”
A cikin dalilan da masu daukaka
ra’ayoyin mazhaba ke bayarwa,
akwai cewa suna riqo da mazhaba
ne saboda tsoron kada Hadisin da
ya bijiro musu ko an soke aiki da
shi. Abin tambaya a nan shi ne
idan an soke aiki da wani Hadisi
ne, ina wanda ya maye gurbinsa?
Imam shafi’i ya yi hannunka mai
sanda a gare su cikin littafinsa mai
suna Al-Risala, inda yake cewa
“Haka ma Sunnar Manzon Allah
(S.A.W.), babu wani abu da zai
soke ta sai Sunnah makamanciyar
ta. Da Allah zai saukar da wani
sabon hukunci don zama Sunnar
Manzon Allah (S.A.W.) wanda
kuma akwai wani hukunci da aka
Sunanta gabannin hakan, to da sai
an yi bayanin soke aiki da
hukuncin farkon, domin gudun
samun sabani. Wannan magana ta
tabbata cikin Sunnar Manzon Allah
(S.A.W.).”

ALLAH YASA MU YI KARSHE MAI KYAU(Sheikh Aliyu Said Gamawa)

Rayuwa mai iyaka, jiya wasu sun tafi,
yau wasu za su tafi, gobe ma za’a
raka wasu kabari…. Abin fata ga kowa
karshe mai kyau. Haka nan da fatan
samun ni’ima da rayuwa mai dadi
cikin kabari. Kuma na tabbata kowa na
burin samun hisabi mai sauki da
shiga Aljannah.
Abin tambaya da dubawa shinne muna
yiwa kan mu tanadin hakan? In dai ni
da kai duk bamu san ranar tafiyar mu
ba, to me ya sa bama kokarin zama
cikin shiri ta hanyar tsoron Allah,
kiyaye umarni da hani da dagewa
wajen bin sunnah da neman yardar
Allah? Mu sani tare da mu akwai masu
rubuta aiyukan mu da furucin mu…
Lallai mutuwa tilas ne akan kowa,
yadda ake kai wasu kabari da kai,
haka wasu za su kaika. Yadda muke
jimami da damuwar rabuwa da
makusanci, haka dangi da masoya za
su rabu da mu wata rana.
Kabari nan ne masaukin farko, ana
tambayoyi a cikin sa, kuma ana fara
gamuwa da ni’ima cikin sa, wasu
kuma daga nan za su fara dandanar
azaba cikin kunci da matsi… Allah ya
sa mu dace.
Pls mu yiwa kan mu tanadi, mu ji
tsoron Allah, mu kiyaye hakkin junan
mu, mu tsare amana ta al’umma da ta
iyalan mu da duk wadda alaqar zaman
tare ta hadamu. Mu kame harshen mu
akan aibata juna, kada mu yiwa juna
hassada ko mugunta. Mu bude
zukatan mu wajen sulhu da yafewa in
an batar mana, mu saukaka cikin
magana da hulda, muna rangwame da
ragayya. Mu ji tausayin juna…. Allah
ya sa mu dace
Na tabbata ba wanda ke yiwa kansa
fatan tsanani ko azaba, don haka mu
kiyaye cikin aiyukan mu don samun
sauki da rayuwa mai dadi duniya da
lahira, amin.