Suka ga Sahabban Annabi Suka ne Ga Shari’a, da Annabi, da Allah

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Haƙiƙa masu zagi da kafirta Sahabbai suna suka ne ga shari’ar Musulunci, da kuma Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi, da kuma Allah Maɗaukakin sarki. Kuma dama shine haƙiƙanin abinda akeso a cimma tun lokacin kafa wannan Aqeedah ta Zagin Sahabbai da kuma kafirta su. Zamuyi bayani ɗaya bayan ɗaya kaman haka:

•Suka ne ga Shari’ar Muslunci: masu sukan Sahabbai haƙiƙa suna suka ne ga shari’ar Muslunci baki ɗayansa, sun sani ko basu sani ba. Domin wa’inda suka rawaito mana wannan addinin suka mana dakonsa sune wa’innan Sahabbai da ake kafirta wa, kuma idan har wa’innan sahabban kafirai ne, kuma Addini yazo ta hanunsu toh kaga baza’a karɓa ba, sabida ba’a karɓan Shari’a daga hanun wanda ba Musulmi ba. Sabida ba amini bane. Toh kaga anan duk wata ibada da mukeyi akwai alamar tambaya akai, haka nan ƙur’ani dake hanun musulmai shima akwai alamar tambaya akansa sabida duka zasu zamto basu da inganci.


•Suka ne ga Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi: idan har ya zamto annabi yayi rayuwarsa baki ɗaya da wa’innan sahabban nashi suna ba mutane kirki ba toh haƙiƙah wannan mummunan suka ne ga Annabi, domin yanayin abokan mutum suna nuna wani irin mutum ne shi. Inhar ya zamto duka sahabban Annabi sun kafirce bayansa, toh haƙiƙah dama musuluncin bai shiga zuciyarsu ba, sannan kuma shima annabi Sallallahu alaihi Wasallama za’a sa alamar tambaya akansa, wanda wannan babu wani musulmi mai hankali da zaiyi haka, wanda har mushrikai da suke tare dashi kafin a turoshi sun tabbatar da cewa shi mutumin kirki ne. Mutumin da Allah ya bada shaida akanshi da kansa yace haƙiƙa kana kan Halayen kirki masu girma. Suratul-Qalam 4.Toh irin Wannan mutumin zakazo kana tuhumar abokansa cewa ba mutanen kirki bane. Allah ya rabamu da taɓewa.


Suka ne ga Allah maɗaukakin sarki: haƙiƙah masu zagin sahabban Annabi da kafirtasu suna suka ne ga Allah subhanahu wata’ala. Domin Allah ya ɗauki wannan saƙo mai girma wanda shine ƙarshen sako a ban ƙasa, ya baiwa mutumin da shine mafi alkhairin halitta a ban ƙasa, sannan kuma bayan duka wannan yazo ya zaɓa masa munanan abokai wanda zasu zo su rushe duk abinda ya gina?! Toh haƙiƙah duk mai hankali zai fahimci cewa anci mutuncin Allah acikin wannan lamari.


Shi yasa abinda ya dace musulmi yayi shine, ya kauce wa jefa kansa zuwa ga halaka, domin magana ɗaya ta kan jefa mutum zuwa wuta, haka nan kuma magana ɗaya takan ɗaukaka mutum. kamar yadda Annabi ya bada labari acikin hadisi

إن العبد ليتكلم بالكلمة من رضوان الله تعالى ما يُلقي لها بالا يرفعه الله بها درجات، وإن العبد ليتكلم بالكلمة من سخط الله تعالى لا يُلقي لها بالا يَهوي بها في جهنم.
Manzon Allah yace: Haƙiƙah bawa zai kasance yana furta wani zance wanda ke ƙunshe da yardar Allah, bai damu da ita ba, amma Allah sai ya ɗaukaka darajar sa da wannan zance da yake furta wa, haka nan bawa zai kasance yana furta wani zance wacce ke jawo fushin Allah, bai damu da ita ba Allah zai jefa shi cikin jahannama sabida wannan zance da yake furta wa.

Bukhari 6477

Wannan hadisi tana nuna mana mahimmancin kame baki ga barin mummunan zance, yana daga cikin mafi munin zance kafirta musulmi, balle ma ace sahabban Annabi Sallallahu alaihi Wasallama. Allah yasa mudace, ya rabamu da faɗawa ga halaka.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories