Khawarijawa(Muhammad Rabi'u Rijiyar Lemo)

Khawarijawa wasu jama’a ne da suka
yi wa Sarkin muminai Aliyyu dan Abi
Dalib tawaye, suka kafirta shi tare da
duk wadanda suke tare da shi, kamar
yadda suka kafirta Mu’awiya dan Abi
Sufyan da duk wadanda suke tare da
shi.
Yana daga cikin manya-manyan akidun
khawarijawa kafirta duk wani wanda
ya aikata babban zunubi, kamar zina ko
sata ko kisan kai, a wurinsu a akidarsu
duk wanda ya aikata babban zunubi to
ya kafirta, kuma a lahira dan wuta ne,
zai kuma dawwama a cikinta.
Khawarijawa sune farkon jama’ar da
suka rabu da musulmi, suka kuma
kawo rarraba cikin musulmi, kafin
zuwansu ko bullarsu ba a san tawaye
ga shugaba ba, tare da yakarsa.
Shaikhul Islam Ibnu Taimiyya yana
cewa : “khawarijawa su ne farkon
wadanda suka kafirta musulmi, suna
kuma kafirtawa ne da zunubi (Ma’ana
da mutum ya aikata zunubi to ya
kafirta) haka nan suna kafirta duk
wanda ya saba musu a cikin bid’arsu,
suna halatta jininsa da
dukiyarsa” (Alfataawa : 7/279).


Tuni dama Manzon Allah (S.A.W) ya
yi nuni da zuwan khawariju a cikin
hadisai ingantattu da dama, kuma a
lokacin da khawarijawa suka bulla,
sahabban Manzan Allah (S.A.W)
gabadayansu sun yi ittifaki akan su ne
Manzon Allah yake nufi da wadannan
hadisai, don haka ma suka yake su.


SIFFOFIN KHAWARIJAWA
WADANDA SUKA SABAWA
AHLUSSUNNAH DA SU :


Khawarijawa suna da siffofin da suka
banbamta su da Ahlussunnah Wal
Jama’a, ga su kamar haka :
1 – khawarijawa suna kafirta musulmi
don ya yi sabo. Ahlussunnah basa
kafirta musulmi da sabo, sai dai in ya
halatta aikata shi, kamar yadda yake
rubuce cikin littattafansu na akida.
2- akidar khawarijawa ne yi wa
shuwagabanni tawaye, sabanin
Ahlussunnah suna bin shuwagabanni
cikin abin da bai sabawa Allah da
Manzonsa ba.
3 – Akidar khawarijawa ne sabawa
musulmi da yi musu mu’amala irin ta
kafirai, da halatta jininsu, sabanin
Ahlussunnah da suke girmama Ijma’in
musulmai, kuma basa halatta jinin
kowane musulmi sai wanda ya yi abin
da jininsa ya halatta, kamar yadda yake
rubuce a cikin littattafansu.
4- khawarijawa suna da karancin
fahimatar addini, da karancin ilimin
addini, kamar yadda Manzon Allah ya
siffata su da cewa, suna karanta
Alkur’ani amma baya wuce
makogwaransu, ma’ana basa fahimtar
abin da yake cikinsa.
5 – khawarijawa sun jahilci sunnah,
basa yawan kafa hujja da ita, sai dai
Alkur’ani, saboda sun kafirta da yawa
daga cikin sahabbai. Ahlussunnah
kuwa suna da kula da sunnah da kafa
hujja da ita, kamar yadda kowa ya
sani.
6 – Khawarijawa sun kafirta Aliyyu da
Mu’awiya da dukkan sahabban da suke
tare da su. Ahlussunnah kuwa sun
yarda da Aliyyu da Mu’awiya da
dukkan sahabban da suke tare da su,
basa kafirta kowa daga cikinsu.
7 – Khawarijawa suna da tsanani a
cikin addini, mace mai haila za ta yi
sallah, da kafirtawa da zunubi da
sauransu, Ahlussunnah kuwa ba haka
suke ba.
Wadannan kadan kenan dagasiffofin
khawarijawa, Allah ka tsare mu daga
bata, ka shiryar da mu hanyar gaskiya,
ka bamu tabbata a kai. Ameen

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: