DA'AWAR TAUHIDI ABIN ZAGI DA SUKA DA KUSHEWA(Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Babu wani Annabin Allah da ya zo
yana da’awar tauhidi face sai ya
koyar da mutane cewar su
bautawa Allah shi kadai kuma su
nisanci dagutu.
Amsar mushirikai da kafirai da
masu addinin gargajiya suke ba
dukkan wani Annabi ciki har da
Annabi Muhammad (SAW) shi ne
ya na zagin Iyayensu da
aibantashi.
Babu wani mutum da zai yi
da’awar kiyaye tauhidi ta wurin
kadaita Allah shi kadai face sai an
zage shi, kalaman da ake fadawa
wadancan Annabawa shi ma irin
shi a ke fada musu, domin daman
kafirci hanya daya ce.
Duk mutumin da zai ce a kadaita
Allah shi kadai, farkon abin da
zaka ji an ce shi ne ya raina su
wane, ya zagi iyayenmu, ya kafirta
malamanmu.
Babu wanda zai kira sunan wani
musulmi ya ce shi kafiri ne.
Manzon Allah ya hana haka, ya ce
ma duk wanda ya jifi wani da
kafirci to dole zata fada kan daya.
Amma kuma shi manzon Allah
SAW shi da kansa ya fada mana
cewar musulmi zai iya yin aiki da
zai fitar da shi daga musulunci. To
irin wadancan ayyukan su ake
cewar mai yin su yana aikin kafirci.
To yana da kyau ka tambayi kanka
ko da kana da’awar Sunnah, shin
ayyukan da nake yi akwai wanda
manzon Allah ya ce mai yinsu kafiri
ne, ko kuma ya kafirta? Idan babu
sai ka godewa Allah idan kuma
akwai kada ka ce kana jiran wani
ko shawarar wani ka yi maza ka
tuba tun rana bata fito daga
yamma ba. (An rufe kofar tubaba
ko kuma ka jika a cikin kabari)
Mu yi addinin Musulunci da akida
da Ilimi da Hujja da koyarwar
magabata na farko. Ba ra’ayi ba,
ba don kaga wani aboki ko uba ko
dan’uwa yana yi ba, ko kuma don a
garinku aka fito da wannan akidar
ba, ko dan garinku shine shugaba
a wannan tafiya, ko kuma kana
yinta ne domin ka baiwa wane
haushi, ko domin ka sami kudi, ko
dan kin ga mijinki yana yi, dukkan
wata akida da za mu yi mu dauki
littafai mu karanta bango zuwa
bango, mu ji ya wannan akida
take, me take kokarin koyar da mu,
tana koyar da mu girmana
wadansu mutane ne ko kuma tana
kokari karantar da mu yadda zamu
bautawa Allah shi kadai ne.
Ka da ka shagalu da yawan
alkawarin aljanna ko karama da
wasu su ke yiwa mabiyansu, domin
karshen karama shi Manzon Allah,
amma kuma kullum Sahabbai na
tare da shi a Masallaci wurin
Sallah, ba su dai na dukkan wata
ibada da ya koyar da su ba har sai
da suka koma gurin mahaliccinsu.
Hasalima ba su karbi wani zikiri ba
da da idan suna yin shi ba sai sun
yi sallah ba, ba su kuma karbi wani
zikiri ba da idan suka yi shi zai rika
cin ladaddakinsu
Kada wani ya rude ka cewar akwai
wani abu da idan ka yi shi zai baka
darajar Annabawa da Sahabban
Manzon Allah, da hakan gaskiya
ne, da Sahabbai da Tabi’ai sun
shagalu da wannan ibada.
Idan kai Musulmin gaskiya ne
babban abin da zaka fi damuwa da
shi shine
1) YA MANZON ALLAH YAYI KA
ZA,
2) YA SAHABBANSA SUKA YI
WANNAN IBADA,
3) YA MUTANEN NAN WADANDA
YACE AYI KOYI DA SU SUKA
4) YI YA KUMA WADANDA SHI
MANZON YA CE LOKACINSU YA
FI KOWANE LOKACI ALBARKA
SUNA YI.
Ina muku rantsuwa da Allah wanda
babu abin bautawa da gaskiya sai
Allah babu wanda zai yi ibada da
wannan matakai guda hudu face
ya tsira ya samu babban rabo.
Allah ka tsarkake mana niyyar m

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

11 responses to “DA'AWAR TAUHIDI ABIN ZAGI DA SUKA DA KUSHEWA(Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi)”
 1. Rabiu Nuhu Garko Avatar

  Allah ya taimaki sunnah

 2. rabiumusa Avatar

  allahu akbar

 3. rabiumusa Avatar

  assalamu alaikum warahamatullahi yan uwa musulmi wai dan allah menene sunnar annabi mhmd s.a.w?

  1. mahmoud chiroma Avatar
   mahmoud chiroma

   IZGILANCI BA ZAI KAIKA BA.. amma zaka mai maita da larabci

 4. Umar Aliyu Maska Avatar
  Umar Aliyu Maska

  Wajam’u rasulullahi layata shaasu

 5. Nasiru Hussaini Buhari Avatar
  Nasiru Hussaini Buhari

  Assalamu alaikum…
  Malam nidai inada mata saidai bansamu haihuwa ba tukunna. Amma muna fatan Allah SWT Yabamu zuri’a dayyiba amin.
  Malam ina da tambaya ne agareka domin matsalar da nike ciki ya tsananta.
  DAMUWATA: Malam iyayena ne da yayyina agida suka tasani gaba akan lallai sai na saki matata. Saboda kawai an kamata tana zina da wani.
  Wanda aka kamata dashi malaminta ne na makarantar islamiyyar danayi mata register, wadda take zuwa hadda, kuma natabbatarda cewa tasha yin zinan dashi, domin ita dakanta ta shaidarmin da hakan. Malam nidai inason matana tsakanina da Allah, ni kuma nayi bakin kokarina akan ganarda iyayennawa cewa sunnah ta karantar da hakan, amma sunki yarda sudai sai lalai na saketa. Hakan yasa na rabu da su iyayen nawa domin Annabi yace “haramunne yin da’a agaresu idan har zasu ja mutum ga sabon Allah”.
  TAMBAYATA SHINE: Malam idan nachanja mata wata makarantar banyi laifi ba? Saboda duk innaga mutumin raina baya mun dadi sam.
  NAGODE
  Allah yaka tsawon rai ya kuma kareka daga sharrin makiya sunnah… Amin.

 6. Murtala sanusi Avatar
  Murtala sanusi

  INDAI ZAKA FADA TO KAFADI GASKIYA DOMIN ALLAH YANATARE DA MAI GASKIYA

 7. MALAN ALLAH YASAKA DA ALKHAIRI
  MAGANA KAMAN BA GASKIYA ACIKI YAXA’A MATAR KA TAYI ZINA KUMA KACE HARWANI SHAWARA KSKE NEMA WANNAN KANUNA MANA KAI DAYUSS NE DUK DAYUS KUMA BAXAISHIGA ALJANNAH BA
  MATAR KA DAI PASIKACE MAZINATA WADDA SUKE DA AURE.IN ANKAMASU JEFEESU ZA’AYI A HUTA
  SANNAN KUMA GWANDA KABI IYAYENKA KASAKETA YAPINA INKUMA ZAKACI GABA DA ZAMS DA FASIQAR MATAN KA KUMA TOO GA PILI GA MAI DOKI

 8. Sabiu sani Daura Avatar

  Allah taimaki musulumci da musulmai

 9. muaa musa maicon Avatar

  inayiwa malam fatan alikairi

 10. usman umar maidahini Avatar
  usman umar maidahini

  duk abinda mutum yafada ubansa ya fadi fiye da shi akan wannan akida kuma wanan akida ita takaranta da duk wani wai maijinka sa dasuna malam akan wacen akidar mai suna izal to kaga dun kacewa malamin ka kafiri wanan tsakaninkane kaida ubangiji.( kuma mu bama tare da wanda yace siyasa tafi sallah.) kuma wai mutum yace mace idan tanada janaba tana karatun alqur,ani ina yaga wanan karatu annabi muhammad (saw) baifada ba dun haka bama akida dun kudi idan bahakaba kuhada kanku tsakanin jos da kaduna sanan duk mai bacin wani ko yakirashi da kafiri ya cigaba munasa haka yataso ya isko gida anayi .

Leave a Reply

Categories
Latest updates