WALIYYAN ALLAH!(Muhammad Rabi'u Rijiyar Lemo)

WALIYYAN ALLAH!
Waliyyi shi ne wanda ya yi imani da
Allah, yake kuma jin tsoronsa, kamar
yadda Allah Madaukakin Sarki ya fada
a cikin littafinsa mai girma, Suratu
Yunus aya ta 62 – 63.
Dukkan musulmi mai tsoron Allah
waliyyin Allah ne, gwargwadon
imaninsa gwargwadon walittakarsa,
mafiya darajar waliyyai Annabawa da
Manzannin Allah, sai Sahabban
Annabi (S.A.W), Siddikai, shahidai sai
Salihan bayi.
Babu wani zamani ko lokaci tun farkon
zuwan musulunci har zuwa daf da
tashin Alkiyama da babu waliyyan
Allah a cikinsa. Akwai waliyyan Allah
Mata kamar yadda ake samunsu a
maza, akwai waliyyan Allah a cikin
malamai da masu Mulki, da yan
kasuwa, da talakawa da masu kudi.
Ahlussunnati Wal Jama’a sun yi imani
da samuwar waliyyan Allah, har ma
karamominsu, kamar yadda Alkur’ani
da Hadisai ingantattau suka tabbatar da
hakan.
Walittaka bata haduwa da yin shirka da
bokanci ko da’awar komai Allah ne,
duk wanda dayan wadannan abubuwa
na shirka ko bokanci ko da’awar komai
Allah ne ya tabbata a kansa to wannan
ba waliyyin Allah ba ne, sai dai
waliyyin Shaidan.
Kuskure ne babba takaita waliyyan
Allah akan wasu mutane ko jama’a ko
darika, a ce kadai a cikinsu ake samun
waliyyai. Haka nan kuskure ne ayyana
wasu mutane ko mutum a ce duk
wanda baya sonsa ko baya son su,
baya son waliyyai, ko yana gaba da
waliyyai, ko bai yarda da waliyyai ba.
Haka nan kuskure ne babba fitar da
sahaban Manzon Allah daga waliyyan
Allah, har a rika ganin mai kaunarsu
baya son waliyyai, mai zaginsu da
aibata su masoyin waliyyai ne, tunda
dai ya yarda da wasu mutane da ake
kirawa walittaka.
Kofar walittaka a bude take, babu wani
mutum da zai zama cikamakin
waliyyan Allah, duk wanda ya yi
da’awar shi ne cikamakin waliyyai a
yau ko a zamanin baya, hakika ya yi
kuskure, kuma ya fadi abin da ba haka
yake ba, cikamakin waliyyai shi ne
karshen mumini da zai bar wannan
duniya. Allah ya sanya mu cikin
waliyyansa na gaskiya, masu kaunar
waliyyan gaskiya, Annabwa da
Siddikai da Salihan bayi. Ameen.

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: