HADIN KAI BAYA HANA WA'AZI DA FADIN GASKIYA!(Muhammad Rabi'u Rijiyar Lemo)

Danna nan domin shiga karatu Online

Hadin kan musulmi da
dunkulewarsu su zama abu daya,
wani abu ne da Allah da Manzonsa
suka yi umarni da shi, kuma suke
son shi, Allah Madaukakin Sarki a
cikin lintafinsa mai girma a wurare
da dama ya hana bayinsa
musulmai rarrabuwa. Haka nan
Manzon Allah (S.A.W) ya hana
rarrabuwa, ya yi umarni da haduwa
da lazimtar Jama’a a wurare da
dama a cikin hadisansa ingantattu.
A gefe guda kuma tarin ayoyi masu
yawa sun zo akan yin wa’azi da
umarni da kyakkyawan aiki da
hana mummuna, kamar yadda
Manzon Allah (S.A.W) ya yi umarni
da isar da sakonsa koda kalma
daya ce mutum ya sani, don haka
hadin kai baya nufin ka kyale dan
uwanka akan barnar da yake ba,
shi ma ya kyale ka akan barnar da
kake kai ba, kada kowa ya fadi
abin da dan uwansa yake yi ba
daidai ba, wannan ba shi ne irin
hadin kan da Allah da Manzonsa
suke so ba, kuma ba shi ne aka yi
umarni da shi a cikin Alqur’ani da
hadisai ingantantu ba, Saboda
haka ba karamin kuskuren fahimta
ba ne, wani ya ce an raba kan
musulmi don ana yi musu wa’azi
akan su bar bidi’a da shirka, don
kuwa Allah Madaukakin Sarki a
cikin Suratul Ali-Imran inda ya yi
magana akan hadin kai da rashin
rarrabuwa sai da ya ratso da
maganar wa’azi da umarni da
kyakkyawan aiki da hani da
mummuna.
Magana ta gaskiya hadin kai na
gaskiya shi ne wanda aka gina shi
akan Alqur’ani da Hadisai
ingantattu akan fahimtar magabata
na kwarai, aka yadda da yiwa juna
nasiha da fadin gaskiya, amma
matukar zamu kawar da kanmu
daga kuraran juna, da bidi’o’i da
shirka da zagin sahabbai da
sauran miyagun akidu, mu daina
wa’azi a kansu, mu ja bakinmu mu
yi gum, wai da sunan hadin kai, to
babu ko shakka wannan ba hadin
kai ba ne, kuma babu yadda
zukatanmu za su hadu, kuma ba
shi ne Allah da Manzonsa suke so
ba. Allah ya yi mana gamonkatar.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

One response to “HADIN KAI BAYA HANA WA'AZI DA FADIN GASKIYA!(Muhammad Rabi'u Rijiyar Lemo)”
  1. musabimam gombe Avatar
    musabimam gombe

    Malam Allah yasakamaka da dimbin lada,
    malam ina da tambaya,
    musulmi zai iya hadikai da wanda ba musulmiba.

Leave a Reply

Categories
Latest updates