Shi addini umarni ne da kyakkyawa da hani ga mummuna

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Sheikhul Islam Ibn Taimiyyah yana faɗi acikin Littafinsa Iqtida’u siradil mustaqeem:

idan Bid’ah yana da makamancinsa acikin ayyukan alheri toh kayi ƙoƙarin canza wannan Bid’ah da wannan alheri, (Misali kaman masu zikirin bid’ah, sai su canza shi da wanda yazo a sunnah)

Yace: domin ita zuciya bata barin wani abu sai don wani abu, kuma bashi yiwu wa ga mutum ya bar wani alheri sai dai in zai koma zuwa ga wani alherin.

da yawa daga cikin masu inkarin bid’oi na ibada da kuma al’ada zaka samesu masu rauni ne wurin aikata sunnoni irin wa’innan ko kuma umarni dashi, Shi addini umarni ne da kyakkyawa da hani ga mummuna, baza’a samu tabbatuwan ɗaya ba sai ansame su duka, ba za’ayi hani ga mummuna ba sai kuma a gefe guda ana umarni da kyakkyawa, wanda wannan umarni da kyakkyawan shine zai maye gurbin wannan hani da akayi. Kamar yadda za’a umarci mutane su bauta wa Allah, sannan kuma a hanasu bauta wa waninsa. Domin rayuka an halicce su ne domin suyi ba dun su bari ba, idan har ba’a shagaltar da zukatan mutane kan aikin alheri ba to ba zasu bar aikin sharri ba.

Wannan bayani na Sheikhul Islam tana nuni da cewa a kullum mai da’awah ya kamata ya rinƙa raba ƙafa, ya zamto ba hani yake a kullum ba, ya zamto yana hani ne da mummuna kuma a gefe guda yana umarni da kyakkyawa, misali in ka hana mutane zikirori na Bid’ah to ka koya musu ta Sunnah domin su cigaba da yi, kada ka barsu kara zube.

Allah yasa mudace.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories