Shin ka taba zama kayi lissafin lokacin da kake salwantar wa a social media?

Danna nan domin shiga group na karatu Online

A wannan zamani na social media zaiyi wuya a samu wanda baya shiga ɗaya daga cikin wa’innan kafafe da suka shahara, matuƙar yana da Waya a hannunsa. Wani yana shiga domin yaɗa alheri(Madalla da wannan) wani kuma yana shiga domin yaɗa sharri(Tir da wannan).

Amma abinda mutane basu lura dashi shine lokuta da suke salwantar wa a wa’innan kafafe, da yawa basu lissafinsu, Kuma da yawa mutane suna ga kaman Allah bazai tambayesu kan wannan lokuta da suke salwantar wa ba. To sam abin ba haka yake ba, koda shiga kawai kayi baka yaɗa sharri ba, baka yi wani saɓon Allah aciki ba sai Allah ya tambaye ka.

Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yace

Digadigan Ɗan Adam ba zasu gushe ba a gaban Allah Ranar Alƙiyama sai an tambayeshi game da Rayuwarsa yaya ya gudanar da ita

Wannan yana nuna cewa za’a tambayi ko wanne daga cikinmu kan lokacinsa, a meye ya tafiyar dashi. Sabida haka mu lura cewa Lokaci yana da tsada, da zarar ya wuce to baya dawowa, muyi ƙoƙari muyi amfani dashi a abinda zai amfanar damu Anan duniya da lahira.

Wani zaka samu a rana yakan ɗauki sama da awa uku yana amfani da social media, kuma zaka samu ba wani abin amfani yake bibiya ba sai shirme. Shin ɗan’uwa kana ga wannan awa ukun inda zakayi amfani dashi wurin neman ilimin Addini ko na zamani acikin wata ɗaya Ƙaramin Ilimi zaka tara?

Ya kamata mu farga mu sani cewa lokaci tafiya yakeyi kuma idan ya wuce bazai dawo ba, kuma za’a tambaye mu akansa.

Mu rage salwantar da lokutanmu mu koma muyi amfani dashi a abubuwan da zasu amfane mu.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories